African LanguagesHausa

Zargi Kan Maganin Cutar Daji ko Cancern da aka yi a Shafin Facebook ba daidai ba ne

Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargin wai cutar daji wato Cancer ba ta kissa, wai ana iya maganinta da  lemun tsami a cikin ruwa mai zafi, ko man kwa-kwa da kuma rage shan sukari.

Cutar daji babban rukunin cututtuka ne wadanda kan iya farawa daga kowani gaba a jikin dan adam. Wannan kan faru ne idan kwayoyin cutar suka yadu fiye da kima, har suka gota iyakar da bai kamata su gota ba su ka shiga sauran gabobin jiki, abin da ake kira metastasizing da turanci.

Cutar dajin ta kasu gida biyu akwai wanda ake kira “neoplams” wanda tsuro ne ko kari amma ba lallai ne ya kasance yana da lahani ga jikin dan adam ba. Sa’annan kuma akwai “malignant” wanda shi ne ba’a so dan yana da lahanin gaske.

Wani Aligwo Steve Nwosu, ya wallafa wani labari a shafin Facebook inda ya ke bayanin cewa cutar dajin ba ta kissa  rashin damuwa ko kulawa ne ke yawan hallaka wadanda su ka kamu da cutar. Nwosu ya danganta wannan zargin da wani kwararre kan cutar dajin a jami’ar koyon aikin likita na jihar Osh a birnin Moscow, mai suna Gupta Prasad Reddy.

Labarin ya ambato kwararren na cewa “cutar daji ba ta kissa amma mutane su kan mutu ne saboda rashin kulawa. 

Labarin na zargin wai ana iya kawar da cutar ta yin amfani da hanyoyi uku. Na farko shi ne a daina cin duk wani abin da ke da sukari saboda idan har babu sukari a jikin mutun cutar za ta mutu da kanta.

Na biyu kuma shi ne shan lemun tsamin da aka hada da ruwan zafi kafin a ci abinci, sa’annan a bari sai karfe biyun dare kafin a ci wani abu. Labarin na kuma zargin cewa wani binciken da Kwalejin Koyon Aikin Likita na Maryland ya yi, ya nuna cewa amfani da wannan salon ya fi chemotherapy sau dubu.

Na ukun shi ne shan babban cokali uku na man kwakwa kowace safiya da kowani dare.

Tantancewa

Da muka yi binciken mahimman kalmomi muna amfani da sunan  kwararre a fanin cutar daji  na jami’ar koyon aikin likitan da ke  jami’ar jihar Osh, Moscow, Rasha, da Gupta Prasad mun ga cewa an riga an yi binciken kan mutumin a Africa Check wadda ta yi gargadi kan labarin karya dangane da cutar daji/Cancer daga “Dr Gupta”  a shafin Facebook.

Haka nan kuma jami’ar koyon aikin likitan na jihar Osh ba a Rasha ta ke ba. Jami’a ce a Jamhuriyar Kyrgyzstan.

Binciken da muka yi kuma kan Kwalejin Koyon Aikin Likita a Maryland ya kai mu ga makarantar koyon aikin likitan da ke jami’ar Maryland a Baltimore, Amurka. A shekarar 1807 aka mayar da jami’ar makarantar gwamanti ta farko mai koyar da aikin likita a Amurka.

Daga nan mun duba kowane a cikin zargi hudun da wannan labarin ya yi.

Zargin Farko: Cancer ba cuta mai kissa ba ce

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) cutar daji ita ce cutar da ta fi kissa a duk fadin duniya inda ake kiyasin a shekarar 2020 kadai, mutane milliyan 10 su ka hallaka a dalilin shi. Nau’o’in da suka fi yawa sun hada da dajin mama, huhu, hanji, da na al’aurar maza.

Kusan kashi daya cikin uku na mutuwar da ake yi a dalilin cutar dajin sakamakon amfani da taba sigari ne, da girmar jiki, da shan giya, da rashi ko karancin ‘ya’yan itace da kayan lambu a abinci, da kuma rashin motsa jiki. Wannan ya nuna cewa zargin wai cutar daji ba ta kissa ba gaskiya ba ne.

Sai dai ana iya daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar ta hanyar  inganta abubuwan da ka iya janyo hadarin kamuwa da cutar, aiwatar da dabarun kariyar da aka riga aka yi amanna da su domin akwai hujjar tasirinsu. Alal misali, gano cutar da wuri da kuma kula da wadanda suka kamu da ita. 

Hanyoyin kulawa sun hada da yin tiyata a cire gabar da cutar ta shafa, da magunguna, da chemotherapy – wato magungunan da ke dauke da guban da ke kashe kwayoyin cutar, da kuma radiotherapy – wato inda ake amfani da makamashi da igiyoyin lantarki masu haske ta yadda za su kona kwayoyin cutar a jikin mutun. Akan yi amfani da chemotherapy ko radiotherapy amma wata sa’a a kan hada duka biyun dan inganta damar samun lafiya. 

Zargi na biyu: Rage shan sukari na warkar da Cancer 

Rage shan sukari ba shi da wata alaka da cutar daji. Babu wani binciken da ya nuna cewa rage shan sukari yana kare wa ko ma warkar da cutar daji, sa’anan babu binciken da ya nuna cewa shan sukarin na janyo cutar. 

Wannan labarin daga  cancer.net ya bayyana cewa ana danganta rage shan sukari da cutar dajin ne saboda tsarin da jikin dan adam ke amfani da shi wajen mayar da abinci makamashi, wato abin da a turance ake ce mi shi metabolism. Duk sadda aka ci abinci kafin jiki ya yi amfani da shi sai ya sarrafa shi zuwa nau’in da jikin zai iya amfani da shi kai tsaye a matsayin makamashi domin lafiya da kuma ingancin jikin dan adam. Dan haka idan abinci na dauke da sukari ko kuma an yi shi da hatsi ne, jiki kan sarrafa shi zuwa glucose wanda sukari ne zalla.

Shafin Mayoclinic ya ce kwayoyin jikin mutun da na cutar dajin duka suna amfani da sukarin glucose dan samun kuzari. Haka nan kuma, kwayoyin cutar dajin sun fi sauran kwayoyin jikin dan adam gaggawa waje amfani da sukarin na glucose a cewar the Warburg Effect. The Warburg Effect hanya ce da ake amfani da ita wajen gane ko mutun na dauke da cutar dajin. 

A wani gwajin daukar hoto da ake kira Positron Emission Tomography da turanci ko kuma PET scan a takaice, likitoci kan sanya sukarin glucose din da aka sarrafa a dakin gwaji a jinin mutun. Tunda kwayoyin cutar dajin na amfani da sukarin tun kafin ainihin kwayoyin halittan jikin mutun su yi, da zarar aka je daukar hoton, hasken hoton zai haskaka duk gabobin jikin da ke da kwayoyin cutar dajin da ma duk wani karin da ke da dangantaka da ita. Wannan hoton na PET scan ne ake amfani da shi wajen gani ko mutun na dauke da cutar dajin ko kuma ma wajen sanin ko magungunan da ake bai wa mai dauke da cutar na aiki.

A cikin matakan kariya daga kamuwa da cutar dajin da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta gindaya, babu wani abu dangane da shan sukari. Dan haka wannan zargin karya ne.

Zargi na uku: Shan lemun tsamin da aka hada da ruwan zafi ya fi Chemotherapy aiki

A Wani rahoton da cibiyar binciken kiwon lafiya ta kasa wato National Centre for Health Research ta rubuta, cibiyar ta ce babu wata hujjar da ta nuna cewa lemun tsami na iya magance nau’o’in cutar dajin da ake da su. Wannan rahoton da  Deccan Herald su ka rubuta shi ma ya karyata zargin cewa ruwa da lemun tsami na warkar da cutar daji. 

Duk da cewa wannan binciken (study) na bayyana mahimmancin lemu da sinadaran da ya ke kunshe da su musamman bisa la’akari da magungunan da a kan sarrafa da su, wanda ke nuna rawar da su ke takawa wajen kariya daga kamuwa da cutar daji da ma irin amfanin da su ke da shi wajen magungunan zamani na cutar,, akwai kuma binciken da ke kwatanta karfin lemun tsami da na chemotherapy. 

Rahoton ya bayar da shawarar da a cigaba da gudanar da bincike domin samun alfanu daga duk fannonin sinadaran da ke cikin ruwansu.

Jaridar Deccan Herald ma ta karyata zargib cewa ruwan zafi da lemu na iya warkar da cutar daji

Zargi na hudu. Man kwa-kwa da cutar daji

Wani binciken da aka yi a shekarar 2017 dangane da abin da ake kira Laurie acid ( study on the Laurie acid,) wanda ake samu a cikin man kwa-kwa, ya nuna cewa Laurie acid yana da sinadarin da ke iya yaki da wasu daga cikin nau’o’in cutar daji amma ana bukatar karin bincike domin samun hujjoji masu kwari da ma gano amfanin shi da hanyoyin da ya kamata a bi wajen yin amfani da shi bisa tanadin doka

Wannan binciken da aka yi a shekarar  2019( study ) ya nuna cewa wadansu man kwa-kwan da suka hada da Man kwa-kwa zalla wanda ba’a taba ba (Virgin Coconut Oil VCO), Man kwa-kwan da aka sarrafa( Processed Coconut Oil PCO) da wanda aka tace (Fractionated Coconut Oil FCO) duk suna da sinadaran da ke yaki da cutar daji kuma ana iya amfani da su a matsayin magani musamman a dajin da ta shafi hanta da baki. 

Sai dai wannan zargin ba gaskiya ba ne domin duk da cewa an gano wai akwai sinadaren da ke kashe cutar ana bukatar karin bincike dan gano ainihin irin rawar da za su taka sa’annan a ciki sharuddan da ake bukata kafin a yi amfani da su wajen samar da waraka. 

Mun kuma gano binciken da fullfact.org ta yi wanda shi ma ya karyata duk zargin magungunan da aka yi a wannan rahoton. 

A Karshe

BIncikenmu ya nuna mana cewa wannan rahoton da aka sa a Facebook na dauke da zarge-zargen da ba su da tushe bare gaskiya. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button