|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani saƙon WhatsApp da ya yadu na ikirarin cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) na ɗaukar ma’aikatan wucin gadi 266 domin ayyukan zaɓe masu zuwa a faɗin Nijeriya.

Hukunci: Ƙarya ce. Jami’an INEC sun tabbatar da cewa saƙon na WhatsApp da kuma shafin yanar gizon da aka haɗa da shi ba na gaskiya ba ne.
Cikakken bayani
Bayan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jadawalin babban zaɓen shekarar 2027, wani saƙo ya fara yawo a WhatsApp cewa hukumar na neman ma’aikatan wucin gadi 266 domin ayyukan zaɓukan da ke tafe a ƙasar baki ɗaya.
Wani ɓangare na saƙon ya ce: “Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na gayyatar wadanda suka cancanta daga dukkan jihohi su nemi guraben aiki domin ayyukan zaɓe masu zuwa a faɗin ƙasa. Za a sanar da waɗanda aka zaɓa ta saƙon imel.”
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya (FCT) da aka tsara yi ranar Asabar, 21 ga Fabrairu, 2026.
Saboda yawaitar zamba ta hanyar saƙonnin bogi da ke yawo musamman a lokacin zaɓe, DUBAWA ta yanke shawarar tantance sahihancin saƙon da kuma shafin yanar gizon da aka haɗa da shi.
Tantancewa
DUBAWA ta binciki shafin yanar gizon da aka haɗa a cikin saƙon WhatsApp ɗin, inda ta gano cewa ba shafin hukuma na INEC ba ne.
Nazarin shafin ya nuna cewa an ƙirƙiri shafin ne ta hanyar Google Blogspot, wani dandali na rubutu a blog kyauta, kuma ba ya da alaƙa da shafin yanar gizon hukuma na INEC.
DUBAWA ta kuma tuntubi Zainab Aminu, jami’a a sashen yaɗa labarai na INEC, wadda ta bayyana cewa saƙon ɗaukar aikin ƙarya ne.
“INEC na ɗaukar ma’aikatan wucin gadi ne kawai ta hanyar shafin hukuma da ake kira INECPRES. Duk wani shafi da ba wannan dandalin ba, ya kamata a yi taka tsan-tsan da shi” in ji Zainab.
A Karshe
Saƙon da aka yaɗa a WhatsApp da ke cewa INEC na ɗaukar ma’aikatan wucin gadi 266 ba daga hukumar ya fito ba. Saboda haka, ƙarya ne.




