Getting your Trinity Audio player ready...
|
Cikakken Sako
Da dama ‘yan Najeriya basu gamsu ba (unsatisfied) da sakamakon zaben 2023 wanda yayi sanadi na hawan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulki, manyan abokan adawa Peter Obi na Labour Party (LP) da Atiku Abubakar na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), a lokuta da dama sun soki zabin na Tinubu da shigarsa ofis (office) na fadar shugaban kasa.
Shekaru biyu daga bisani wannan shafi na Facebook Express, ya yada labari daga shafin Daily Excessive, wanda yayi da’awar cewa shugaban na INEC Mahmood Yakubu, ya ba wa ‘yan Najeriya hakuri saboda murdiyar zabe da suka yi, an yi zargin cewa Yakubu ya sauya sakamakon ne ta yadda zai ba wa Tinubu nasara saboda barazana da shi da iyalansa suke fuskanta.
A rahoton an rawaito Yakubu ana zargin yana cewa wannan shine mataki da ya dauka mafi kalubale a rayuwarsa.
Ya zuwa ranar 5 -ga watan Mayu 2025, wannan da’awa( the claim) ta samu martani 32, da masu tsokaci 64, sannan an sake yada labarin sau 101.
Wannan labarin da aka turawa DUBAWA don tantancewa mun lura cewa an tura wa mutane ba adadi ta kafar ta WhatsApp.
Ganin yadda sakon ke yaduwa da yadda zai shafi kimar tsarin zabe a Najeriya ya sanya DUBAWA ganin wajibcin gudanar da bincike kan wannan da’awa.
Tantancewa
Mun kuma duba shafin mun kuma karanta abin da ake magana a kansa, bayan karanta rahoton mun lura cewa babu wata alaka, babu inda labarin ya nuna cewa Mista Mahmood ya yi wata magana mai kama da haka.
Mun kuma danna inda zai kaimu ga shafin amma bayan gwadawa sau biyu sai ya kaimu wani shafin kasuwanci, trading websites. Wannan abu ne sananne idan ana son jan hankalin mutum zuwa wani shafi , DUBAWA ta gudanar da binciken gano gaskiya kan wadannan shafuka kamar a wadannan wurare here da here da here.
Mun kuma yi kokari na tabbatar da gano sahihancin shafin na intanet ta hanyar amfani da (ScamAdviser), amma an gaza gano wannan shafi ko kaiwa gare shi.
Sharhi kan wannan shafi daga ScamAdviser.
DUBAWA ta gano cewa wannan shafin Facebook da ya yada wanan labari an kirkire shi ne a ranar 9 ga watan Yuni, 2019, kuma cikin mutane bakwai da suka yi sharhi kan shafin biyu daga cikinsu sun nemi da ya rika fadin gaskiyar labari.
Mun kuma gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ko za a samu wata sahihiyar kafar yada labarai da tayi labarin amma babu. Mun kuma samu irin wannan labari da aka yada a wani shafin na Facebook mai suna UNITED NATIONS MISSION FOR REFERENDUM IN BIAFRALAND, da mujallar Igbo Times ta buga a ranar 4 ga watan Mayu,2025. A kwai kuma wani link da yake kaiwa ga shafin wasanni na Telegram.
Mun tuntubi mai magana da yawun Mahmood, wato Rotimi Oyekanmi, sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani sako da muka samu daga gare shi.
A Karshe
Labarin da ya yadu cewa shugaban hukumar zabe a Najeriya INEC, Yakubu Mahmood, ya ba wa ‘yan Najeriya hakuri saboda yayi magudi wajen fitar da sakamakon babban zaben shugaban kasa na 2023 karya ne. Shafin na yada bayanai ne don kawai ya ja hankali.