Getting your Trinity Audio player ready...
|
A baya-bayan nan wasu labarai (news circulated) sun karade shafukan sada zumunta cewa Emmanuel Iwuanyanwu tsohon shugaban kungiyar al’ummar Ohanaeze Ndigbo da ya rasu, ya bar wasiya cewa haramun ne matarsa ta sake yin aure muddin tana so ta ci gadonsa.
Yayin da mutane da dama ke ganin cewa matakin da ya dauka bai dace ba, wasu kuma na ganin fitaccen shugaban na wannan kungiya ta zamantajewa da al’adun Igbo, shi ke da iko ya fadi yadda yake so a yi da dukiyarsa cikin iyalansa bayan rasuwarsa.
A kokari da DUBAWA ke yi kan harkokin yada labarai da ilimantar da al’umma, mun fito da bayanai kan matsayar dokar Najeriya a dangane da wannan batu.
Halasci da Tilasatwa ko akasin haka kan abin da ya shafi sake yin aure
Da fari dai a dokar kasa ta Najeriya ya halasta wanda yake da kadara ya yi wasici da ita, wannan tsari shi ake kira da suna (testamentary freedom,) dama ce ta ba da kadara ga wanda mutum ke da sha’awar ya bawa, sai dai duk da haka wannan baya nufin babu ka’ida ko iyaka.
Duba da wannan, batun cewa bai halasta mace ta yi aure ba idan tana son ta gaji mijinta in ya mutu, ba haka abin yake ba a dokar Najeriya, wannan tsari ya ci karo da sashi na 42 na kundin tsarin mulkin Najeriya Section 42 na 1999.
Binciken masana da tattaunawa da kwararru a fannin shari’a da mai bincikenmu ya gudanar ya nuna cewa an samar da wannan sashe ne don taka birki ga mutane da ke neman hana wasu hakkin da ya kamata su samu dalilin jinsinsu ko addini ko daga inda suka fito da sauransu.
Sau tari, wasu kotunan na Najeriya na jaddada hakkin mata ga samun gadon mijinsu, duba da wannan, batun cewa kar mace ta sake aure kafin ta samu gado ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.Domin kara samu gamsuwa da wadannan bayanai DUBAWA ta binciko karin wasu shari’a da aka yi kamar ta Ukeje vs. Ukeje da Mojekwu vs. Mojekwu.
Duk da cewa wannan sharia biyu da aka yi basu da batun sake aure, mun lura da batu na neman danne hakkin matan a wajen gado, kuma kotun ta basu gadonsu, abin da ya jaddada matsayar kundin tsarin mulkin kasa.
Matsayar Lauyoyi
Moshood Ibrahim, wani lauya da ke zaune a birnin Ilorin ya fadawa DUBAWA cewa a tsarin kotu babu batun cewa mace za a bata gado ne idan har ba za ta sake yin aure ba,wannan take wa mata hakki ne da nunawa matan wariya.
“ A kan wannan mace na da damar kalubalantar batun sake auren a kotu don a dawo mata da abin da ke zama hakkinta ne,’ a cewarsa.
Ga ma wata hujjar ta fuskar shari’a kamar yadda sashi na 34 Section 34 a kundin ya tanada, wanda shima na ba da kariya ne ga ‘yancin dan adam da mutuncinsa.
Ya kara da cewa daya daga cikin ma’aurata ne ya fi dacewa ya gaji dan’uwansa idan mutuwa ta ratsa tsakaninsu, Idan mutuwar ta zo to shi kenan dayan na da damar sake yin aure ya kuma gaji dan’uwansa.
“Don haka idan ka nemi a rubuta wasiya a kuma fitar da matarka a ciki, wannan wasiya ba za ta yi aiki ba a kotu, muddin auren na nan lokacin da daya daga cikin ma’auratan ya mutu.”
“Ko da ace al’ada ce ta mijin matar da ya mutu, wacce ta ce mata ba za ta yi sabon aure ba muddin mijinta ya mutu idan tana son ta gaje shi, to wannan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya,” a cewar masanin dokar.
Haka nan ita ma Hadiza Alfa, lauya da ke zaune a Kaduna, ta bayyana cewa batun a ce mace ba za ta sake aure ba, muddin tana so ta gaji dukiyar mijinta abu ne da za a iya kalubalantarsa a gaban kotu, ganin yadda yayi karantsaye ga batun adalci da daidaito da tsarin rayuwar dan Adam.
“Karkashin dokar muhalli ko gida, miji da mata daya daga cikinsu zai iya gadar dan’uwansa, ”a cewarta.
A cewar masaniyar dokar ba da damar mallakar muhalli baya nufin kuma shi wanda aka bawa sai abin da ya ga dama zai yi, dole sai an yi amfani da doka wajen mallakar ko yin abin da za a yi da kadarar.
“Haka kuma gindaya sharadi cewa sai mace ta zauna ba tare da sake yin aure ba kafin ta gaji mijinta, wannan take hakki ne ga mace kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, abu ne da ba za a aiwatar da shi ba, ” a cewarta.
A Karshe
Abubuwa da DUBAWA ta gano sun nunar da cewa doka a Najeriya na ba da kariya ga mata, cewa mace ba za ta sake aure ba kafin mallakar gadon mijinta, wannan take hakkin mata ne karkashin doka. Wannan batu bai dace da doka ba, kuma ba za a aiwatar da shi ba, kuma za a iya kalubalantar batun a gaban shari’a.