African LanguagesHausa

Shin da gaske ne ‘yansanda a Afirka ta Kudu sun kama wata mata da surikinta dan asalin Najeriya wanda ya ba da kudin bogi a matsayin sadaki?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wata dattijuwa da mambobin iyalinta ‘yansanda sun kama su a Afurka ta Kudu bayan da sirikinta dan asalin Najeriya ya biya  R95000 lobola ( A matsayin sadakin aure) kudin da ke zama na bogi.

Shin da gaske ne ‘yansanda a Afirka ta Kudu sun kama wata mata da surikinta dan asalin Najeriya wanda ya ba da kudin bogi a matsayin sadaki?

Sakamakon bincike: Karya ne! Hoton da aka makala a labarin an dauko shi daga wata wallafa da aka yi a 2021 daga hukumar ‘yansanda a Afurka ta Kudu. Kuma ma ‘yansandan kasar sun fito sun nesanta kansu da labarin na karya.

Cikakken sakon

A shekarun baya-bayan nan akwai labarai da ake yadawa da ke zama na bace ga ‘yan Najeriya inda ake alakanta su da aikata zamba ta fuskoki da dama , duk da cewa babu hujja da ake dora tunanin ‘yankasar akai.

Wannan baya rasa nasaba da yadda aka dauki kasar da cewa tayi kaurin suna a harkokin cin hanci da rashawa an kuma samu wasu tsofafin jagorori a kasar da laifukan cin hanci da rashawa.

Dalilin wannan ya sanya wannan da’awa ta rika samun amincewa a shafukan sada zumunta. 

I dan ba a manta ba a watan Satumba 2023, wani mai amfani da shafin ( X user ) ya wallafa cewa shirin kulawa da lafiya na (NHS) a Burtaniya ya gano ma’aikatan jinya Nas-nas 700 ‘yan Najeriya  suna da takardun karatu na bogi a wata cibiyar jarrabawa.

” Ya kara da cewa “Najeriya an daga mata ‘jan kati idan ana magana ta daukar aikin ma’aikata a fannin lafiya, ma’ana idan ana zuwa ana dauke kwararru a fannin lafiyar kasar wannan na iya illa ga tsarin lafiyar kasar.’”

Da dama irin yadda wasu suka rika tsokaci kan wannan labari ya nuna cewa sun aminta da abin da aka wallafa. Sai dai bincike (investigation) da kafar yada labaran Reuters ta gudanar ya nuna cewa wannan da’awa karya ce.

DUBAWA ya lura da yadda labarin karyar da aka alakanta da Najeriya ke zagayawa a shafukan sada zumunta.

Wasu sun rika yada labaran da basu da sahihanci, musamman wadanda ke nuna ‘yan Najeriya a matsayin mazambata.

A ranar 27 ga watan Janairu wani fitaccen shafin blog ya wallafa (tweeted) cewa wata tsohuwar mata daga Jukulyn a birnin Pretoria na Afurka ta Kudu da wasu mambobi na iyalanta an kama su da kudade na jabu.   

An yi zargin cewa sirikinsu wanda dan asalin Najeriya ne Kelechi Adegoke Johnson,  ya biya kudi R95 000 zuwa ga wannan iyalai a matsayin  lobola (kudin sadaki kenan a Afurka ta Kudu), sai dai kudaden da ya bayar na bogi ne. Sannan iyalan cikin rashin sani suka rika kashe kudaden.

A cewar mai shafin na blog, matar ta dauki wani bangare na kudin ne inda taje kantin ShopRite don yin siyayya anan aka kamata.

DUBAWA ya lura cewa mutane sun amince da labarin  kamar yadda suke nunawa a tsokaci da suke yi. Wani mai amfani da shafin sada zumuntar @Dilika_ yayi tambaya da cewa “Shin ta yaya ‘yan Najeriya ma ke amfanar da Afurka ta Kudu?“ Za a iya ganin yadda wadannan mutane ke nuna amincewarsu kamar a nan da nan da nan (here, here da here.)

An kuma sanya wannan labari a shafin  Facebook, kamar yadda za a iya gani anan (here).

Duba da irin hadari da irin wannan wallafa shafin na DUBAWA yayi aikin bincike

Tantancewa

DUBAWA yayi amfani da dabarar sake nazartar hoto kan hoton da aka yi amfani da shi a ranar 27 ga Janairu, ya kuma gano cewa an dauko shi ne daga wani labari da aka wallafa a 2021 post, wallafawar da ma’aikatar ‘yansanda ta Afurka ta Kudu ta yi.

A wancan lokaci jawabin da ya fito daga ‘yansanda ya nuna cewa an kama mutane hudu da ake zargi da kudin jabu R2 milyan. 

A cewar jawabin matan guda biyu masu shekaru 57 da 58 da maza biyu masu shekaru 36 da 48 an kama su, za a kuma gurfanar da su a kotu cikin kwanaki biyu kamar yadda takardar da aka raba wa manema labarai ta nunar.

A jawabin ‘yansandan babu inda ya nunar da cewa wadanda ake zargin ‘yanuwa ne ballantana ma batun na cewa wani siriki ne dan asalin Najeriya ya biya sadaki da kudi. 

Har ila yau DUBAWA ya sake bin diddigi inda ma ya gano cewa ‘yansanda sun fitar da wata sanarwa inda suka nesanta kansu da wannan labari na karya.

‘Yansanda suka ce babu inda wasu mambobinsu suka kama wata mata tsohuwa a wani shago a Jukulyn. Babu inda aka shigar da wannan a rijistarsu a Rietgat (Jukulyn) ko a wasu ofisoshin ‘yansanda a yankin.

Hukumar ‘yansandan har ila yau ta yi alawadai da masu amfani da shafukan sada zumuntar suna yada labaran karya dama wadanda ke sake yadawa ba tare da sun gudanar da bincike ba.

“Yada irin wadannan labaran karya nakasu ne ga hukumar ‘yansanda ta Afurka ta Kudu, tun da ko ba komai sai ta gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi. Wanda wannan ke nufin sai an kashe kudade da bata lokaci don gudanar da binciken da dama a ce na gaskiya ne da ya fi. An bata lokaci da ya kamata a ce an yi amfani da shi na bincikar wadanda suka yi laifi na gaske” A cewar ‘yansanda.

A Karshe

Labarin da aka wallafa cewa ‘yansanda a Afurka ta Kudu sun kama wata dattijuwa da wasu mambobi na iyalanta saboda wani dan Najeriya da ke zama siriki a gare su ya ba su kudin jabu na  sadaki (lobola) R95000, labarin kanzon kure ge ne karya ce tsabarta.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »