Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Ajiye abinci a firij na tsawon kwana uku zai iya kashe mutum
Hukunci: Yaudara ce! Abincin da ya yi kwana uku a firji ba zai iya kashe mutum ba.
CIKAKKEN BAYANI
Ba da dadewan nan ba ne Jaridar Leadership Hausa a Nijeriya ta ruwaito Darakta Janar ta NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye na kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar samar da abinci da su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da ingancin abinci da kuma kawar da duk wata barazana da za ta iya jawo hatsari game da ingancin abinci.
A wannan labarin da muka tsakura daga shafin Leadership Hausa daraktar ta yi wannan jawabi ne a taron Ranar Kula da Amincin Abinci ta Duniya wadda ke da laƙabin: Amincin Abinci: Ku shirya wa abin da ba ku yi tsammani ba,’ inda ta jaddada cewa amincin abinci ya rataya ne a wuyan kowa.
Ta bayyana cewa akwai rawar da kowa zai iya takawa domin tabbatar da ingancin abinci tun daga masu samar da shi zuwa masu cin sa.
A cewar darakta janar ɗin a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na hukumar, Sayo Akintola ya fitar a ranar Talata, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kiyasta cewa a duniya, ɗaya daga cikin mutum 10 na fama da rashin lafiya, kuma 420,000 ke mutuwa a kowace shekara saboda cin gurbataccen abinci.
TANTANCEWA
DUBAWA ta ga wannan labarin ne a shafin DDL Hausa a manharajar Facebook sai mu ka dauka domin mu gano gaskiyar labarin. Mun yi amfani da manharajar Google in da muka ga da cewar babu wasu sahihiyar shafukan yada labarai da suka dauki labarin nan a haka sai dai yawanci kaman Leadership Hausa ta ruwaito cewar daraktar NAFDAC ta shawarci yan Najeriya da su guji ajiye daffefen abinci a firij na fiye da kwana uku saboda haɗarin kamuwa da cututtuka.
Dan karin bayani akan lamarin mun tuntunbi wani masanin abincin (nutritionist) mai suna Umar Salisu dan mu san idan gaskiya ne yana yiwuwa mutum ya mutu bayan ya ci abinci da aka ajiye a firji na tsawon kwana uku, ya shaida mana cewa hakan yaudara ce.
“Idan har aka sami batu irin haka toh zai zamanto an yi ajiyar abincin haɗe da wasu abubuwa masu illa ko lahani a cikin firij hankan ne zai iya jawo mutuwa. Ko kuma yawan cin abincin da aka ciro daga firij ba’a ɗuma ba aka ci da sanyi nan ma yana iya janyo lahani cutar daji ga dan adam idan aka cigaba da yi,” ya bayyana.
Ya ce yana kyautata zaton daraktar NAFDAC ta shawarci yan Najeriya ne da su guji cin daffefen abincin da aka ajiye fiye da kwana ukun saboda gudun illa a gaba ba wai tana nufin a take ba ya kara shaidawa cewa yana iya ma yiwuwa illar taƙe idan akwai abubuwa masu lahani a cikin firij kaman kyankyasai ko idan ba’a goge firji har ya tara datti sosai masu illa za’a iya samun guba abinci.
Bugu da kari mun tuntunbi sakatariya daraktar NAFDAC dan karin bayani ta shaida mana cewar darakta Mojisola Adeyeye bata fadi haka ba kuma ta shaida mana da cewar in ma karin bayani muke so akan lamarin, mu tuntunbi shafukan su zamu ga mu ga da cewar ba fadi wani abu makamanci haka.
Sai mu ka garzaya shafukan su kaf muka dai babu inda Farfesa Mojisola Adeyeye ta fadi cewa idan aka ci daffefen abinci daga firij bayan kwana uku za’a mutu.
Mun yi wannan binciken ne saboda wayar da kan al’umma da su guje cecekuce da yaɗe yaɗen abubuwan da ba gaskiya ba, idan ma za’a fadi abu a faɗe shi yadda aka ji shi ba tare da kari ba ko yaudarar Jama’a. Muna kuma bada shawara ga yan Najeriya da su zama an ankare da karyace karyacen wasu kaffofin yaɗa zumunta.
A KARSHE
Da’awar a ake yi cewar daraktar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce idan aka ci daffefen abincin da ya kwana uku a firij na kisa Yaudara Ce! Domin mun bincika mun gani cewar da’awar ba haka yake ba.