African LanguagesHausa

Shin kamfanin man Burtaniya na BP na daga cikin Kamfanonin da su ka fi gurbata muhalli a duniya?

Zargi: Kamfanin man fetur na Burtaniya, BP ne kamfanin da ya fi gurbata muhalli a duniya. 

Sakamakon Bincike: Gaskiya. Kamar yadda muka gani a bayanai da dama BP na daga cikin kamfanonin da suka fi gurbata muhalli a duniya.

Cikakken Bayani

Tattaunawar da ake yi dangane da sauyin yanayi na ta daukar hankali, kuma wannan ba cikin kuskure ne ya ke faruwa ba.

Daga wannan tattaunawar ne ake samun tabbacin ko dan adam zai iya rayuwa cikin kariya a wannan duniyar saboda yadda sauyin yanayin ke tasiri kan ayyukan dan adam, a hanyoyi da yawa, na cigaba da kasancewa barazana ga rayuwar duniyar ma baki daya.

Ire-iren wadannan ayyukan sun yi sanadin cigaban da ake sami a karuwar yanayin zafi a duniya, musamman saboda hayakin masana’antu, da sauran abubuwa masu gurbata yanayi da muhalli.

Tasirin wadannan ayyukan ne suka bayyana a matsayin karuwar da ake samu na zafi da da fari, da karancin ruwa, da gobarar daji mai tsanabi, da tumbatsar ruwa, da ambaliya, da narkewar kankara, da guguwa da kuma raguwar da ake samu a adadin tsirai da dabbobi

Sai dai mahawarar da ake yi danganeda sauyin yanayi ya fuskanci tsaiko kwanan nan. A shafin Twitter misali, gwagwarmaya aka rika yi kan ko sauyin yanayi yaudara ce. 

Lokacin da aka yi mahawarar wani mai amfani da shafin Twitter D Dr Eli David (@DrEliDavid), cewa ya yi tun farko da ma batun sauyin yanayi abu ne da kamfanin man Burtaniya ta BP ta kirkiro dan ya sami damar dora laifin illolin sauyin yanayi a kan wani banda su. Wannan batun ya ja hankalin al’ummar twitter sosai domin mutane kusan 18,000 suka yi ma’amala da sakon a cikin kankanin lokaci amma kuma mutanen sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta.

Shafin ya bayyana kamfanin BP a matsayin daya daga cikin manyan kamfanonin da ke da alhakin gurbata yanayi a duniya baki daya.

Wani tsokacin da ya musanta wannan ya fito ne daga wani mai suna The Magnesium guy Scott Henrie (@10mm_404) wanda ya ce: “me ya sa kake karya? China ce kasar da ta fi gurbata yanayi a duniya. (ainihin gurbata yanayi).”

Duk da cewa mutumin bai bayyana bangaren da ke da alhakin gurbata yanayin ba, ba zai yi ma’ana ba a kintata a ce ga wanda ke gurbata yanayi ba tare da an yi la’akari da alkaluman da ake amfani da su ba da ma yadda ake sanya bangarori daban-daban cikin rukunnai.

Misali, bacin rukunin kamfanoni, ana iya kasa masu gurbata yanayi bisa kasashe da masana’antu ko kuma fannoni, dan haka ne ya ke da mahimmanci mu fayyace wannan mu sa shi kowa ya fahimci abun da ake yi.

Tantancewa

Da farko, mun binciki duka labaran da aka wallafa, wadanda ke bayani dangane da batun gurbata yanayi da muhalli, inda muka gano wannan rahoton da BBC ta yi a watan Nuwamban 2022 wanda ke bayyana yadda ayyukan fitar da iskan gas din da kamfanin BP ke yi ke kasancewa barazan ga kiwon lafiyar mutanen, Rumaila.

Baya ga shi, mun sake gano  wani rahoton da jaridar The Guardian ta rubuta a watan Oktoban 2019 mai taken “An bayyana: Kamfanoni 20 da ke haddasa kashi daya cikin uku na hayakin masana’antu.” BP na daya daga cikin kamfanonin da aka bayyana a rahoton.

Da muka cigaba da bincike a majiyoyin bayanai na duniya,mun gani wani rahoton wanda aka wallafa a 2019. Cibiyar tabbatar da adalci a harkokin da suka shafi sauyin yanayi ce tawallafa.Rahoton ya bayyana cewa tsakanin 1965 da 2017 BP na daga cikin kasashe 6 a duniya wadanda ke da lhakin kusan ton biliyan 34 na hayakin masana’antu.

Haka nan kuma, a rahoton shi na watan Afrilun 2023, jaridar kwararrun muhalli na Eco Experts sun tabbatar cewa BP na daga cikin manyan kamfanoni tara da suka fi gurbata yanayi a duniya

Bisa bayanan wata mujallar cibiyar nazarin shugabanci wanda ya fita a watan Afrilun 2023, BP na mataki na 6 a cikin kamfanonin da a hade suke da alhakin ton biliyan 34 na hayakin masana’antu a duniya.

Mun kuma sake gudanar da bincike dangane da wanda ke kalubalantar zargin a cikin wurin rubuta tsokaci wato The Magnesium Guy Scott Henrie wnada ya ce China ce ta fi gurbata yanayi a duniya.

Ganin cewa BP kamfani ne dan haka ba zai kasance cikin rukuni daya da kasar China wadda kasa ce ba, sai muka nufi bayanan da za su ba mu karin bayani dangane da kasashen da ke gurbata yanayi.

Kasashen da ke gurbata yanayi

Shirin Majalisar Dinkin Duniya dangane da Muhalli ya fitar da wani rahoto a watan Nuwamban 2021 wanda ke bayani kan yadda kasashe ke gurbata yanayi. Kamar yadda ya ke a hoton da ke kasa.

A karshe

Zargin cewa BP kamfanin hakar man Burtaniya na daga cikin kamfanonin da suka fi gurbata yanayi gaskiya ne, bisa yawan hayakin masana’antun da suke fitarwa. Bisa bayanan UNEP mun kuma gano cewa da gaske kasar Chinar ce ta fi gurbata yanayi tun da ita ce ta fi fitar da hayakin masana’antu.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button