Zargi: Ana zargin wai Najeriya ce kasar da ta fara kaddamar da shirin One Health wanda shiri ne mai haka kan bangarorin gwamnati daban-daban wajen tabbatar da tsarin kiwon lafiya mai nagarta.
Sauyin yanayi ya zama babban batu wanda ke kan gaba a mahawarorin kasashen duniya inda masu ruwa da tsaki su ke neman hanyoyin dakile matsalolin da ya ke janyowa. Daya daga cikin hanyoyin da aka samar ita ce One Health. Wannan salo ne da kasashe suka dauka na tsarawa da aiwatar da shirye-shirye, manufofi, dokoki da bincike ta yadda bangarorin gwamnati daban-daban za su yi aiki tare da inganta lafiyar al’umma.
Duk da cewa kalmomin “One Health” sabbi ne ba’a cika amfani da su ba, tun ba yau ba aka fara amfani da tsarin da ake kwatantawa da hakan kuma duk duniya ta san da shi. Ana iya bin diddigin shi zuwa lokacin da aka tabbatar da dangatakar da ke tsakanin lafiyar dabbobi da na dan adam a tsakanin shekarun 1821 da 1902.
Babban taron da aka fara yi dangane da One Health an gudanar da shi ne a birnin Davos da ke kasar Switzerland a shekarar 2012, daga nan ne ya samu karbuwa a kasashen duniya a matsayin kwakwarar hanyar yaki da matsalolin lafiyar da kan afku sakamakon cudayyan da ake samu tsakanin dan adam-dabbobi- da muhalli, hatta cututtukan da dan adam kan kama daga dabbobi wato zoonotic diseases a turance.
Ministocin lafiya da muhalli na kasashen Afirka na daga cikin wadanda suka nuna sha’awarsu tun da wuri bayan da suka sanya hannu a yarjejeniyar Libréville lokacin babban taron farko na ministocin lafiya da muhalli, wanda aka gudanar a 2008, daga baya kuma su ka nuna amincewarsu da tsarin dabarun aiki na shekaru 10 (10 Year Strategic Action Plan) domin inganta matakan aiki a sassan lafiya da muhalli a nahiyar Afirka daga 2019 zuwa 2029 lokacin babban taron ministocin kasashen duniyar karo na ukun da aka gudanar a 2018.
Ranar laraba 20 ga watan Afrilu lokacin taron kara wa juna sanin Cibiyar Sabbin Dabarun AIkin Jarida da Cigaba (CIJD) dangane da dauko rahotannin lafiya, muhalli da suayin yanayi, jami’in shirye-shriyen lafiya a cibiyar Adebowale Adedigba ya ce karamin ministan lafiyar Najeriya, Adeleke Mamora ya yi zargin cewa Najeriya ce kasar da ta fara kaddamar da tsarin dabarun aikin na One Health a Afirka.
Shin Ministan ya fadi haka da gaske? Idan ya fada, yaya gaskiyar wannan zargin? Dalilin da ya sa mu ke so tantance wannan batun ke nan.
Tantancewa
Domin tantance ko ministan ya yi wannan furucin, mun fara da binciken mahimman kalmomi inda muka gano wani rahoton da aka wallafa a shafin reliefweb wanda ya tabbatar cewa ministan ya kasance a babban taron da aka kaddamar da tsarin a shekarar 2019.
“Najeriya ta kirkiro tsarin dabarun aikin One Health wanda zai cimma kalubalen da kasar ke fiskanta a fannonin lafiya, dabbobi, da muhalli. Wannan salon na amfani da sabbin dabarun da ke da mahimmanci wajen shawo kan irin matsalolin da mu ke fuskanta sa’annan yana bayar da damar kulla dangataka ta aiki tsakanin ma’aikatun gwamnati daban-daban. Fatanmu shi ne aiwatar da wannan shirin a Najeriya zai zama abin koyi ga sauran kasashen Afirka,” rahoton ya rawaito ministan na cewa.
Wani rahoton da jaridar Business Day ta rubuta, ita ma ta rawaito ministan na fadin hakan.
Bayan da muka tantance lallai ministan ya yi wannan furucin, sai mu ka bukaci mu san ko maganar gaskiya ce, dan haka sai mu ka fara binciken shirye-shiryen One Health na sauran kasashen Afirka dan ganin ko su na da shi da ma lokacin da su ka kaddamar da su.
Mun gano wani labarin da ke nazarin nasarori da kuma irin kalubalen da shirin na One Health zai fiskanta nan gaba a nahiyar Afirka ta yin amfani da kasashe uku a matsayin misalai. Kasashen sun hada da Najeriya, Tanzaniya da Uganda. Dan haka sai mu ka binciki wadannan kasahse uku.
Tsarin Najeriya na One Health wanda ke da shafuka 80 shiri ne na tsawon shekaru 5 wato daga 2019 zuwa 2023.
Tsarin Tanzaniya kuma na kunshe a cikin wani littafi mai shafuka 66 wanda aka shirya dan ya yi aiki na tsawon shekaru 5 daga 2015 zuwa 2020.
Mun kuma gano shirin Uganda wanda shi ma na tsawon shekaru biyar ne amma daga 2018 zuwa 2022. Littafin mai shafuka 52 hadaka ce tsakanin Ma’akatar kiwon lafiya(MoH), Ma’aikatar noma, kiwon dabbobi da kifaye (MAAIF), Hukumar Kula da dabbobin dawa (UWA) da Ma’aikatar Ruwa da Muhalli (MWE) tare da tallafin kudi da fasaha daga Hukumar Kula da Ci-gaban Kasa da Kasa na Amurka (USAID) da shirinta na P&R wato shirin mayar da martani.
Bisa la’akari da wadannan litattafan da muka gano muna iya ganin cewa Tanzaniya ce ta fara kirkiro na ta shirin a shekarar 2015 sai Uganda a 2018 sa’annan Najeriya a 2019.
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa ba Najeriya ce ta fara kaddamar da shirin One Health a Afirka ba domin mun gano wadanda aka fara amfani da su a Tanzaniya 2015 da kuma Uganda 2018.