African LanguagesHausa

Sojoji sun yi watsi da da’awar cewa shugaban sojan kasa ya mutu

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Akwai kafafan yada labarai da dama a shafin Facebook wadanda ke da’awar cewa shugaban sojan kasa a kasar Taoreed Lagbaja, ya rasu.

Sojoji sun yi watsi da da’awar cewa shugaban sojan kasa ya mutu

Hukunci: KARYA CE. Shelkwatar sojan Najeriya ta yi watsi da da’awar da ake fadi cewa shugaban sojojin ya rasu, haka nan suma wasu kafofin yada labarai sahihai sun tabbatar da cewa shugaban na nan da ransa yana kuma karbar kulawar likitoci.

Cikakken Sakon

Rundunar sojan kasa ta Najeriya ta gamu da tarin suka kan suka (commendations da condemnations) tun bayan watanni 18 da Taoreed Lagbaja ya dare kujerarsa ta shugaban sojan kasar Najeriya (COAS) a ranar 19 ga Yuni,2023, inda ya kasance shugaban sojojin karo na 27.

Sai dai ganin yadda aka ga ba a ganshi ba a wasu taruka muhimmai kamar ranar tuni da samun ‘yancin kai ta 2024 da ranar da aka yaye sojoji karo na 71 a makarantar koyar da aikin soja ta NDA wannan ya haifar da gutsiri tsoma kan ingancin lafiyar shugaban.

A ranar 20 ga watan Oktoba,2024 wani mai amfani da shafin X Jackson Ude, yayi da’awa (claimed) cewa Mista Lagbaja Lutanal Janar ya rasu dalilin cutar kansa ko daji.

Ga abin da wallafar ke cewa “Shugaban rundunar sojan kasar Najeriya Lutanal Janar. Taoreed Lagbaja, ya rasu. Lagbaja ya rasu a wani asibiti a kasar waje kusan sa’oi 48 da suka gabata dalilin cutar kansa wacce ke a mataki na uku kamar yadda wani babban jami’i na gwamnati ya bayyana.

Wannan da’awa ta yadu kamar wutar daji a shafin Facebook kamar yadda aka gani a wadannan wurare (here, here da here.)

Girman wannan da’awa da irin rudani da za ta iya haifarwa a cikin al’umma ya sanya DUBAWA shiga aikin bincike.

Tantancewa

 Mun duba sahihin shafin X  na rundunar sojan (Nigerian Army) sai muka ga an dauko hoton  wannan labarin tare da dambara alamar sheda da ke nuna cewa labari na karya ne “Fake News,” wanda ya zuwa  6:16 p.m na yammacin ranar 20 ga Oktoba,2024 rundunar ta karyata labarin. Haka nan wasu fitattun kafafan yada labarai sun yin watsi da wannan da’awa kamar a wadannan wurare (here, here, da here.)

A jawabi (statement) dauke da sa hannu a ranar 19, ga Oktoba, 2024, mai magana da yawun rundunar sojan ta Najeriya Onyema Nwachukwu, yace Lagbaja yana can ana duba lafiyarsa a daidai lokacin da kuma ke hutunsa. Yace shugaban sashen tsare-tsare a rundunar Abdulsalam Ibrahim, shi ke rike da mukamin na shugaban rundunar sojan kasa ta Najeriya COAS har lokacin da zai dawo.

A Karshe

Duk da cewa an samu rahotanni na kafafan yada labarai da dama da ke nuna cewa Taoreed Lagbaja shugaban sojan kasa a Najeriyar bashi da isasshiyar lafiya, labarin da aka yada cewa ya rasu labarn karya ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »