African LanguagesHausa

Wani kiyasi da ya bazu cewa matan Najeriya basu da biyayya ba haka bane

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wasu masu amfani da shafin Facebook da dama sun bayyana cewa bayanan da Durex survey ya fitar ya nunar da cewa Najeriya ce ke kan gaba a duniya da mata marasa mutunta aure/zamantakewa.

Wani kiyasi da ya bazu cewa matan Najeriya basu da biyayya ba haka bane

Hukunci: YAUDARA CE. Bayanan da aka fitar abu ne da za a yi taka tsan-tsan kasancewar bayanai ne da aka fitar a 2012 kan batun amfani da kwaroron roba don ba da kariya ga lafiyar al’ummar duniya.

Cikakken Sako

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi sharhi da cewa mata a Najeriya su ke kan gaba wajen rashin yin biyayyar zamantakewar aure a duniya.

Wani mai amfani da shafin Facebook Untamed, yayi wata wallafa (posted) ta sunaye na kasashe da matansu ke zama masu cin amanar zamantakewar aure, Najeriya kuma ita ke kan gaba da yawan mata masu wannan dabi’a inda suka samu kaso 62% sauran kasashe sun hadar da Thailand (59%), Italy (50%), United Kingdom (42%), Russia (33%), Spain (30%), da France (16%).

Mai amfanin da shafin na Facebook ya kuma sanya Najeriya da samun kaso 30% da yin yaudara ta batun daukar ciki kuma ya kafa hujja da binciken da kamfanin samar da kwaroron roba ba Durex ya fitar bayan nazartar mutane 29,000 daga kasashe 36.

Ya zuwa ranar 18 ga watan Oktoba,2024 wannan wallafa ta samu martani 448, wadanda suka yi tsokaci 140 da masu sake yadawa 19 tun daga lokacin da aka wallafa labarin a ranar 5 ga watan Oktoba,2024 kamar yadda yake nan here da here.

Ganin yadda wannan da’awa ka iya illa ga mutuncin mata a Najeriya hakan yasa DUBAWA shiga aikin bincike.

Tantancewa

Mun yi amfani da hanyar gano hakikanin abuwawa ta DUBAWA Chatbot, hanyar gano bayanai da kirkirarriyar basira ta AI, kan batun na yaudara a fagen daukar ciki. Ta bayyana cewa da’awar karya ce kasancewar babu wasu bayanai da aka tattara a hukumance ko wani bincike da kasa ta yi wanda zai mara baya ga wannan da’awa, dama dogaro da wasu sahihan kafofin yada labarai kamar nan here, here da here.

Mun kuma yi amfani da wasu muhimman kalmomi kamar neman bayani game da bincike da Durex ya gudanar , Mun gano cewa kamfanin da ke samar da kwaroron na roba Durex ya gudanar da bincike kamar nan here, amma babu wata kafa da ya fitar da bayanai kan wasu mutane don tabbatar da abin da ake fadi kamar yada aka yada abun tamkar wutar daji.

DUBAWA ta kuma gano cewa wani bincike da yayi kama da na Durex  shine bincike kan jima’i a duniya Global Sex Survey, wani nazari ne da ake gudanar da shi kan harkokin da suka shafi lafiya da aikata jima’i inda aka nazarci mutane 29,000 daga kasashe 36, Ana nazarin duk bayan shekaru biyar. Wannan ya sabawa labarin rashin da’a ko biyayya da ake yadawa da kuma ake raba shi da Durex .

Wannan da’awa ana ci gaba da yada ta daga lokaci zuwa lokaci tun  daga 2012, “Jima’in farko da kwaroron roba da irin tasirinsa kan yadda mutum zai ci gaba da jama’i nan gaba” Mun gano cewa ‘yan Najeriya da Afurka ta Kudu ne kadai a kan jadawalin kasashen, kuma Najeriya ta samu maki 62.8% daga mutane 500 da suka ba da bayanai a binciken, babu inda aka ce mata a Najeriya su ke kan gaba wajen cin amanar aure ko zamantakewa a binciken ko sune mata da ke gaba masu cin amana a duniya.

Ko da muka tuntubi Durex Nigeria a ranar 14 ga Oktoba,2024 sun ce sun tura wannan da’awa ga wadanda suka dace ta hanyar shafin Instagram page. Ya zuwa ranar 18 ga Oktoba,2024 babu wani martani da suka samu.

A Karshe

Bincike da Durex ya gudanar babu inda ya alakanta Najeriya da cewa matan kasar sune kan gaba wajen iya cin amanar zamantakewar namaji da mace a duniya, don haka da’awar yaudara ce kawai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »