African LanguagesHausaMainstream

Gaskiya ne wai Adamu na APC ya yaba wa Peter Obi kamar yadda ake zargi a Tiwita?

Zargi: Ana zargin wai ciyaman din jam’iyyar APC ya ce ko daya bai raina irin kwazo da himmar da Peter Obi ke da shi ba, domin da hakan yana iya kai labari

Gaskiya ne wai Adamu na APC ya yaba wa Peter Obi kamar yadda ake zargi a Tiwita?

Gaskiya ne, yayin da ya ke hira da Arise TV ciyaman na APC Abdullahi Adamu ya ce ba ya shakkun cewa Peter Obi zai iya jagorantar magoya bayansa ga nasara

Cikakken labari

Yayin da zaben 2023 ke kara matsowa kusa, masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar na cigaba da zuwa gidajen talbijin dan tattauna batutuwan da suka shafi jam’iyyunsu da zaben mai zuwa.

Kwannan nan aka fara yawo da wani hoton da ke zargin cewa shugaban jam’iyya mai mulki ta APC, Abdullahi Adamu ya yaba wa Peter Obi dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Leba.

Bayanin da ake dangantawa da ciyaman na cewa : “Na ziyarci Peter Obi lokacin yana gwamna a jihar Anambra, mutun ne mai kyakyawar nufi wa Najeriya dan haka ba ni da wani dalili mai kwari na raina kwarewar da ya ke da shi wajen jagorantar mutanensa zuwa ga nasara.”

Hoton bai nuna sunan mai shafin tiwitan da aka ga hoton ba sai dai akwai tambarin gidan talbijin din Arise abin da ke nuna cewa a wannan tashar ne Adamu ya yi hirar.

Da zarar aka fara shirye-shiryen zabe, yana da mahimmanci ‘yan siyasa su rika kulawa da abin da su ke fada domin ana iya juya maganar yadda za ta yadda zai taimaki wata jam’iyyar ta fi wata, shi ya sa mu ke so mu tantance wannan bayanin.

Tantancewa

Mun gano shafin wanda ya fara wallafa hoton da ke dauke da bayanin a shafin Tiwita. Sunar sa Olisamekalum OrakwyelumOdujwe (@ddukehmself). 

A wurin yin tsokaci wani mai amfani da shafin mai suna Edena MD ya ce a bayyana mi shi tushen labarin inda ya ce “Majiya In ka yarda.”

Wani kuma (@Tovinctokwy) cewa ya yi idan har akwai bidiyon inda Adamu ya ke wannan maganar ya kamata a sauke bidiyon domin ana iya amfani da shi a ci gyaransu.

Wani wanda ya amsa tsokacin da mutumin farko ya yi,  Will (@Free_dom237) ya bayar da adireshin shafin Arise a youtube inda ya ce “ga bidiyon, ku shakata”

Da muka yi binciken mahimman kalmomi, ya kai mu zuwa rahotannin da jaridun Daily Post, Legit da Top Naija su ka wallafa dangane da wannan zargin, inda suka yi amfani da hirar da Abdullahi Adamun ya yi da Arise a matsayin majiyarsu. 

Dan haka ne DUBAWA ta nufi shafin Arise a Youtube domin samun hirar da ya yi kwanan nan da ciyaman din APC. Mun gano wani bidiyo mai tsawon minti 59 wanda aka wallafa ranar lahadi 17 ga watan Yunin 2022.

An yi wa bidiyon taken “Ba ni da masaniyar cewa APC ta sha kaye a jihar Osun” ya yi tsokaci dangane da sakamakon zaben jihar Osun da tasirin da zai yi a zaben 2023 mai zuwa.

Bayan an kai minto 31 da hirar, an tambayi ciyaman din ko yana kallon  jam’iyyun hammaya na PDP da Lp a matsayin barazana, sai ya ce “ban raina jam’iyyun ko ‘yan takararsu idan ya zo maganar jagorantar magoya bayansu zuwa nasara.”

“Peter Obi, na san shi lokacin da ya ke gwamna a jihar Anambra. Ni ziyarce shi lokacin da na ke gwamna kuma wadannan mutane ne wadanda ke da kyakyawar nufi wa Najeriya a ra’ayi na. Daga ma yadda suke bayanai, ana iya gane cewa suna da nufi mai kyau.

“Suna da kwarewa, ba ni da wata shakkar cewa ba za su iya yin nasara ba sai dai mun fi so tsari kuma muna abubuwa a tsanake…” a cewar Abdullahi Adamu

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa ciyaman din APC ya ce baya shakkun cewa Peter Obi ko wani dan takara a jam’iyyar hamayya zai iya kai labari. Ya yi wannan furucin ne lokacin da ya yi wata hira da Arise TV amma ya ce na shi jam’iyyar ta fi su da tsarin da zai taimaka mata wajen lashe zaben 2023

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »