Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wasu masu amfani da shafin Facebook sun yada labarin dake da’awar cewa Sarkin Kano Muhammad Sanusi II yace idan mijinki ya mareki ki rama.
Hukunci: Yaudara ce! Bincike ya nuna cewa wannan tsohuwar magana ce da sarkin yayi tun a shekara ta 2017, kuma ‘yar sa yace ya gayawa hakanan.
Cikakken Bayani
A yayinda ake ci gaba da cece-kuce kan sabuwar dokar da ta rushe Masaurautu da Sarakuna biyar na jihar Kano da kuma sake nada Sarki na 14 Muhammad Sanusi na biyu a matsayin Sarkin Kano, an rika yada wata magana da ake alakantawa ga Sarki Sanusi na cewa Sarkin yace duk wadda mijinta ya mare ta to ta rama.
Mutane da dama sun wallafa wannan labarin a shafin Facebook kamar yadda muka zakulo a nan, da nan, da nan da kuma nan.
Hotunan da’awar da muka zakulo a Facebook
Labarin ya ja hankanlin mutane da dama kasancewar Sarki Muhammad Sanusi ya shahara wajen yin kalamai dake janyo ce-ce-ku-ce a cikin al’umma.
Domin cire al’umma a cikin shakku kan ko Sarkin yayi wadannan kalaman, Dubawa tayi bincike akan haka.
Tantancewa
Bincike ya nuna cewa an tsakuro wannan maganar ce “idan mijinki ya mareki ki rama” a cikin wani labari da kamar yada labarai ta BBC Hausa ta wallafa a ranar 27 ga watan Fabrairun 2o17, inda Sarki Sanusi ke gargadin masu dukan matansu, inda yace babu inda addinin musulunci ya bai wa namiji damar dukan matarsa..
A cikin jawabin Sarkin wanda ya gabatar a wurin auren zawara 1,500 da gwamnatin jihar Kano ta yi, ya ce ya shaida wa ‘yarsa cewa idan mijinta ya mare ta to ta rama.
BBC ta dora sautin muryar Jawabin Sarki Sanusi kuma abinda Sarkin ke cewa shine “ni na gayawa ‘ya ta idan mijinki ya mare ki mare shi ki fito”
Ko me ya sa aka zakulo wannan maganar?
Wani mai lura da al’amurran da ke faruwa a shafukan sada zumunta, Nasiru Chindo ya ce wannan bai rasa nasaba da batun sake mayarda Sarkin akan karagar mulki.
“Ka san akwai ‘yan adawa da kuma wadanda basu so hakan ba, ta hanyar zakulo irin wadannan maganganu suna ganin zasu iya shafawa Sarkin bakin fenti ga al’umma.” inji Nasiru
A Karshe: Wannan labarin Yaudawa ce! Sarkin Kano Muhammad Sanusi II yayi wadannan kalaman ne tun a shekara ta 2017 kum yana magana ne akan abinda ya shaidawa ‘yar sa.