African LanguagesHausa

Wai shin birnin Legas ne mafi karfin tattalin arziki a mataki na uku a Afirka kamar yadda Shettima ke zargi? 

Zargi: Dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC Kashim Shettima na zargin wai a cikin jerin biranen da ke da karfin tattalin arziki, Jihar Legas na mataki na uku

Wai shin birnin Legas ne mafi karfin tattalin arziki a mataki na uku a Afirka kamar yadda Shettima ke zargi? 

Ba gaskiya ba ne! Bincikenmu ya nuna cewa ba Legas ne birni na uku a cikin jerin biranen da su ka fi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka ba.

Cikakken bayani

A babban taron shekara-shekara ta kungiyar lauyoyi wato NBA na shekarar 2022, wadansu daga cikin wadanda ke takarar shugabancin kasar sun tattauna wadansu mahimman batutuwa ranar 22 ga watan Agusta, 2022.

‘Yan takarar jam’yyar PDP Atiku Abubakar, Jam’iyyar Leba Peter Obi da Kashim Shettima dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyya APc ne su ka kasance manyan baki a babban taron.

Mr Shettima ya wakilci Mai gidansa tsohon sanata Tinubu a taron inda ‘yan takarar su ka gabatar da kadan daga cikin irin shirye-shiryen da za su aiwatar idan har aka zabe su.

Lokacin da ya ke jawabi, Mr. Shettima ya yi zargin cewa jihar Legas ce ta fi karfin tattalin arziki a mataki na uku a nahiyar Afirka.

“Lokacin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama gwamnan jihar Legas a shekarar 1999 motar kai mutane asibiti wato ambulance daya ce rak a jihar baki daya, sa’annan kowace wata, jihar na samun milliyan 700 a matsayin kudaden shiga, amma a halin da ake ciki yanzu, jihar Legas na samun billiyan 51 kowace wata daga sana’o’in da take da su a cikin jihar kawai. Legas ce jiha mafi tattalin arziki a mataki na uku a cikin jihohin da ke Afirka,” tsohon gwamnan jihar Bornon ya bayyana.

Wannan zargin lallai yana iya yin tasiri kan irin shawarwarin da masu zabe za su yanke dangane da wanda za su zaba, dan haka ne DUBAWA ta ga yana da mahimmanci ta tabbatar da gaskiyar wadannan kalaman.

Tantancewa:

DUBAWA ta fara da tantance mahimmanc kalmomi sa’annan ta nemi alkaluman da za su iya fayyace gaskiyar wannan batun.

A shekarar 2017, tsohon gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode ya ce yana hasashen jihar Legas za ta kasance a mataki na uku na jihohin Afirka masu karfin tattalin arziki a shekarar 2020

A bayanan da aka yi a kundin bayanan yanayin tattalin arziki na duniya, kasashei masu karfin tattalin arziki a Afirka sun hada da Najeriya, Afirka ta Kudu da Masar. Jaridar Satistics Times ma ta bayyana haka.

A cewar rahoton wadannan kasashen uku kadai ne ke da kusan rabin tattalin arzikin kasashen Afirka. Jimilar abin da Masar ke samu kowace shekara ya ninka abin da kasar Aljeriya ke samu sau biyu, kuma Alheriyar ce a mataki na hudu. Kasa mafi karancin tattalin arziki a Afirka baki daya ita ce Sao Tomé and Principe.

Shafin statista wanda ke bayani kan biranen kasuwanci na duniya shi ma ya sanya birnin Alkahirar Masar a matsayin birnin da ya yi fice a duk fadin Afirka inda birnin Legas ke zaune a mataki na 8.

Shafin ya kai ga wannan sakamakon ne bayan da ya yi nazarin biranen da ke taka rawar gani a fanin tattalin arziki a duniya ta yin amfani da bayanan da ke da mahimmanci wajen yanke shawara a matakin shugabancin manyan kamfanoni. Haka nan kuma sauran abubuwa kamar yawar al’umma da yawan abin da kasa ke samu kowace shekara su ma sun taka rawa wajen gano ko biranen suna cikin yanayin da ya dace da kasuwanci.

Statista ya kuma bayyana cewa Najeriya ce ta fi yawan abin da kasa ke samu kowace shekara a Afirka a shekarar 2021 inda ta sami dalan Amurka billiyan 441.5. A yayin da Afirka ta Kudu ke biye da ita a baya da dalan Amurka biliya 418.

Idan muka lura, kasashen yankin arewacin Afirka biyu, wato Algeriya da Morocco suna biye da Masar wadda ta kasance a mataki na uku cikin jaddawalin jerin kasashen Afirkan da ke da karfin tattalin arziki.

Ma’aikatar kula da tsare-tsaren tattalin arziki da kasafain kudi na jihar Legas wato (MEPB) a rahoton da ta fitar dangane da ayyukanta daga shekarar 2013 zuwa 2021 ta bayyana cewa jihar Legas ta na a mataki na hudu kan jaddawalin jerin kasashen da ke da karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka a shekarar 2020 bayan da aka lissafa yawan abin da suke samu kowace shekara. Wannan jaddawalin da aka yi ya sanya biranen Masar, Johannesburg da Cape Town a matakai uku na farko.

Sabanin zargin da aka yi, ba Legas ce jiha ko birni  a mataki na uku daga cikin jihohi da biranen da ke da karfin tattalin arziki a Afirka ba amma dai Najeriya ce ke da tattalin arziki mafi girma a anahiyar Afirka. Bacin haka, a nazarin statista, Legas na mataki na takwas a jerin birane/jihohin da ke kan gaba a tattalin arziki a Afirka.

Baya ga wannan bincike, mun tuntubi Mr. Shettima da mataimakinsa Ahmed Ningi dan samun karin bayani danganeda majiyarsu sai dai yunkurinmu ya ci tura.

A Karshe

Bincikenmu ya nuna cewa ba Legas ne birni na uku a cikin jerin biranen da su ka fi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button