African LanguagesHausa

Yaya gaskiyar batun wai jariri zai iya rayuwa a wata jaka ta musamman a maimakon mahaifar mace yadda aka fi sani? 

Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargin wai akwai sabuwar fasahar da za ta iya taimakawa wajen rayar da jariri a cikin jaka a maimakon maihafar mace.

Yaya gaskiyar batun wai jariri zai iya rayuwa a wata jaka ta musamman a maimakon mahaifar mace yadda aka fi sani? 

Karya! Jarirai ba za su iya rayuwa a wata jaka ta musamman ba domin bincikenmu ya nuna mana cewa ba’a taba amfani da jakar a kan dan adam ba sai dai tumaki

Cikakken bayani

Jarirai kusan miliyan 15 ake haifa kowace shekara kafin su kai wata tara a ciki ko kuma daidai wa’adin da ya kamata, a yayin da wadansu milliyan guda kuma su kan rasa rayukansu sakamakon matsalolin da ke tattare da ciki da kuma haihuwa.

Matsalolin da ake samu da ciki ko kuma haihuwa kafin ciki ya kai watanni taran da ya kamata, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) su ne ke janyo mutuwar da ake gani a tsakanin yara masu shekaru biyar zuwa kasa na haihuwa.

Wani mai amfani da shafin Facebook Chief Yuma ya wallafa wani kabarin da ke zargin wai ana iya sa jariran da ba su isa lokacin haihuwa ba a cikin wadansu jakuna na musamman domin su cika wannan wa’adin. Yuma ya ma kara da cewa an dade ana amfani da wannan fasahar.

“Nan gaba, ba sai mata sun dauki ciki da kansu ba. Ana iya san jinjirin a jaka har ya kai lokacin haihuwa. A cewar Whistles Blisters an shafe shekaru da dama ana amfani da wannan fasahara,” kamar yadda ya bayyana a cikin labarin da ya wallafa.

Kiwon lafiya na cigaba da fuskantar kalubale na labarai marasa gaskiya kuma yana da mahimmanci jama’a su sami bayanai na kwarai wadanda za su taimaka mu su wajen daukar matakai masu amfani wajen gudanar da abubuwan da suka shafi kiwon lafiyarsu da rayuwarsu ta yau da kullun.

Tantancewa

Mun fara bincikenmu da yin amfani da mahimman kalmomin da su ka bulla a wannan labarin. Wannan ne ya kai mu ga wata kalma mai suna ectogenesis wanda wani salo ne na rayar da jariri a waje, wato wani wuri banda mahaifar mace.

Salo irin wannan wanda jama’a suka fi sani shi ne rayar da jariri a kwalba (abin da ake kira incubator da turanci) irin wanda ake sanya bakwaini a ciki a yawancin asibitoci. Yawanci idan jariri bai yi girman da zai iya rayuwa da kan shi ba a kan sanya shi a cikin kwalban a ajiye har sai sadda zai iya rayuwa da kan shi misali numfashi, cin abinci da sauransu.

Bincikenmu ya nuna mana cewa wata kungiyar masu bincike da ke asibitin yara a Philadelphia sun kirkiro wani abin da ake kira Biobag. Sun kirkiro wannan jakar ne domin rayar da jariran tumaki tun suna cikin suffar kwai, wannan jaka ita ce ke maye gurbin mahaifa wacce ke dauke da wani karamin bututu,  wanda zai rika daukar iska yanan kaiwa jaririn ta igiyar cibiya. Bayan haka a kan sanya ruwa na musamman mai suna amniotic fluid wanda da ma ake samu a cikin mace ko dabba mai ciki wanda zai rika taimakwa jaririn wajen numfashi da hadiya.

Akwai wani bidiyon YouTube wanda asibitin ya wallafa shekaru biyar da suka gabata tare da cikakken bayani dangane da yadda wannan jaka ta musamman ke ai mai taken “Sake kirkiro mahaifa: Sabon ci-gaba ga jarirai.” To sai dai asibitin sun bayyana cewa an gwada wannan a kan jarirai ne kadai ba kan dan adam ba.

Ko da shi ke bayan nasarar da aka yi da tumakin ana cigaba da yunkurin kirkiro wanda zai taimakawa dan adam wajen rayar da jariran da ba za su iya kai wa’adin da ake bukata a cikin iyayensu ba.

Wani labarin da aka wallafa cikin jaridar The Guardian a shekarar 2020 ya yi nazarin yiwuwar amfani da wannan fasahar a dan adam, to amma kawo yanzu, ba’a taba amfani da shi a akan dan adam ba. Yana da mahimmanci a kuma fayyace cewa jakunan na Biobag ba a yi su dan maye gurbin daukar juna biyu ba ne domin dan tunkiyar da aka yi amfani da shi daga cikin uwarsa aka cire ba wai an hada shi a waje ba ne.

Bayanin Kwararru

Wani likitan yara a asibitin Cedar Crest da ke Abuja, Alabi Olukayode ya yi watsi da wannan abun da ya kira hasahse.

“A tunani na ba na ji gaskiya ce, wannan hasashe ne ko jita-jita. Na ji duk ire-iren wadannan labaran tun kafin in shiga makarantar koyon aikin likita. Duk da cewa ban nemi tantance gaskiyar wannan batun da kai na ba, da irin illimin da na samu a makaranta na gane cewa wannan ba gaskiya ba ne,” ya bayyan.

Jeremiah Agim, likitan mata kuma babban likita a asibitin National Hospital da ke Abuja ya ce bai ma san akwai irin wannan fasahar ba.

“Ba ni da wata masaniya dangane da wannan batun. Idan yana maganan cloning ne (wato wata hanyar amfani da kwayoyin halitta wajen kirkiro dabba ko mutun) wani wani abu ne daban,” ya ce.

Wani likitan matan kuma mai suna Sunday Idoko ya ce ya san a kan jariran kwalba amma bai san wannan fasahar ba.

“A kashin gaskiya, wannan ne karon farko da nake samun labarin wannan fasahar. To ammam yana iya yiwuwa domin a aikin likita ba mu cewa faufau.

Mun sami jariran kwalba da sauransu a baya. Wannan kamar fasahar IVF ne da mu ke ji kullun, sai dai a yayin da IVF a kan sanya kwayayan namiji da na mace a cikin mahaifar mace ne, a wannan komai a waje a ke yi kafin a sanya shi a mahaifa,” ya bayyana.

A karshe

Ba za’a iya rayar da jarirai a wani abin da ake kira Biobag ba, an kirkiro jakar ne dan taimakawa jariran da ba su cika wa’adi ba amma kuma kawo yanzu a dabbobi kadai aka yi  amfani da jakar dabbobin ma tumaki. Duk da cewa ana cigaba da yunkurin kirkiro wanda za’a iya amfani da shi a kan dan adam, batun ko jarirai za su iya rayuwa cikin irin wadannan jakuna a zahiri ko kuma ma kowace irin jakar da aka yi da wannan burin abu ne da ke bukatar karin bincike da gwaji.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »