Zargi: Wani sako da ke yawo a WhatsApp na zargin wai Hukumar Kula da Wutar Lantarkin Najeriya na (NERC) na daukar ma’aikata
Bincikenmu ya nuna mana cewa NERC ba ya daukar ma’aikata, kuma adireshin shafin da ake zargin nan ne ake tura takardun neman aikin ba shi da nagarta
Cikakken bayani
Masu zamba na cigaba da amfani da labaran daukar ma’aikata su yaudari wadanda ba su ji ba su gani ba su kuma saci bayanan jama’a.
Kwanan nan aka turowa DUBAWA wani sakon da ke cewa Hukumar Kula da Wutar Lantarkin Najeriya na daukar ma’aikata domin ta tantance.
Wannan sakon na dauke da adireshi da aka kwatanta a matsayin shafin da hukumar ke bukatar masu sha’awar samun aikin su shiga su bayar da bayanansu dan samun damar kasancewa daga cikin ma’aikatan da za’a dauka a bana wato shekarar 2022
Tantancewa
DUBAWA ta fara da bude adireshin da ake yadawa a WhatsApp wanda ya kai ta zuwa wani shafi mai suna recruitment.online amma ba a rubuta kalmar recriutment daidai ba, sai dai aka rubuta ta kamar haka recruitment a cikin adireshin wannan babban alamar tambaye ne bisa sahihancin shafin.
Daga nan sai muka bi shawarwarin da aka bayar na yin rejista wanda aka raba shi zuwa kashi uku. Na farko ya bukaci masu neman aikin su bayar da bayanansu kamar suna, lambar waya, shekaru da makarantar da suka yi sa’anan jihar da suka fito.
A kashi na biyu akwai tambayoyin da ya kamata a amsa sai a kashi na uku, an bukaci masu neman aikin su gayyaci ‘yan uwa da abokai kafin a basu ainihin fam din neman aikin da ya kamata su cika. Wannan ya zo daidai da dabi’ar shafukan masu damfara da zamba a cikin aminci.
Mun yi binciken mahimman kalmomi wanda ya kai zuwa shafin da ke da ke dauke da sanarwar da hukumar NERC ta yi dangane da mazambatan da ke cewa suna daukar ma’aikata. Hukumar ta yi gargadin cewa masu irin wadannan tallace-tallacen su kan bukaci kudin rajista.
Baya ga haka mun kuma gano cewa lallai hukumar ta fitar da sanarwar neman ma’aikata a shafinta na Tiwita, amma tun a watan Yuni kuma wa’adin ya riga ya cika tun 15 ga watan Yulin 2022.
A wancan lokacin, adireshin shafin da suka yi amfani da shi na daukar ma’aikatan shi ne careers.nerc.gov.ng, wanda ya banbanta daga wanda aka bayar cikin wannan sakon.
Daga nan mun je shafin daukar ma’aikatan na NERC inda muka tarar da babban sanarwar da ke bayanin cewa an kammala daukar ma’aikta.
Bacin haka mun sake sanya adireshin cikin manhajan tantance sahihancin adiresoshi wanda ke iya gano shafukan zamba ya kuma yi amfani da alkaluma ya auna sahihancin shafin da maki bisa 100. A nan ma shafin ya bayyana shi a matsayin mara gaskiya ya kuma ba shi maki 1/100
A Karshe
Binciken da muka yi ya nuna mana cewa NERC ba ta daukar ma’aikata. Adireshin da aka bayar a sanarwar da ake yadawa a WhatsApp ba daidai ne da na hukumar ba.