Getting your Trinity Audio player ready...
|
Cikakken Sako
Kewayen Tafkin Chadi (The Lake Chad Basin), wuri ne da miliyoyin al’umma ke rayuwa a cikinsa daga kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Nijar, yanki ne da Allah Ya azurta da tarin albarkatu da al’adu wanda ke da muhimmanci ta fannin tattalin arziki, sai dai labaran da ake yi a kan yankin na zama wanda ba a zurfafa ba a bayyana cikakkun abubuwa da yankin ya kunsa.
Wasu kanun labaran na ba da bayanai ne kawai kan yadda tafkin ke janyewa wasu kuma labaran ta’addanci, yayin da bayanan al’ummar yankin suka takaita daga bangaren kafafan yada labarai da ‘yansiyasa. Rashin samun cikakkun bayanai su suka jawo ake yada jita-jita sabanin jin bayanai na hakika kan halin da al’ummar yankin suke ciki na rayuwarsu yau da kullum.
Wannan makala ta fayyace abubuwa bakwai da ake da fahimta a kansu baibai, ta kuma warware fahimtar masu karatu kan yadda za su kalli ainihin yadda yankin na Tafkin Chadi yake, yankin da ke da kalubale ta fuskar yadda yanayin muhallin yake da yadda yake farfadowa a zamantakewa cike da kalubale da siyasar yankin ke ciki.
Jita-jita ta 1: Mayakan sakai su ke da iko da yankin Tafkin Chadi baki daya

Hukunci: Karya ne!
Mayakan Boko Haram da mayakan IS a yammacin Afurka ta Yamma (ISWAP) ba su ke da iko da yankin na Tafkin Chadi ba, sai dai ana ci gaba da ganin tasirisnu a yankin inda ake ganinsu a wasu yankunan, (presence in various regions) musamman a Arewa maso Gabashin Najeriya da Arewacin Kamaru da wani yanki na Chadi da Nijar.
A Najeriya jihar Borno anan ne Boko Haram ke cin karenta babu babbaka, haka nan ayyukansu sun shiga jihar Adamawa da Yobe inda ake samun rahotannin ayyukansu a yankunan karkara iyaka da Kamaru da Chadi. A Kamaru, Boko Haram na dabdalarta a yankin Arewa mai nisa musamman a yankunan kauyikan Mora da Kolofata inda suke kai hari a kan iyaka da ma yin garkuwa da mutane.
A kasar Cahdi mayakan na gudanar da ayyukansu a yankin da ke kusa da Tafkin Chadi musamman a yankunan da ke zama tsibirai, abin da ke zama tarnaki ga dakarun soja su kai masu farmaki.
Haka kuma a kasar Jamhuriyar Nijar Boko Haram na gudanar da ta’addancinta a yankin Kudu maso Gabshin kasar musamman a yankunan da ke da iyaka da Najeriya.
Jita-jita ta 2: Ayyukan ta’addanci na karuwa saboda yadda Tafkin Chadi ke janyewa

Hukunci: Yaudara ce!
Duk da cewa akwai wasu sauye-sauye na muhalli da ke faruwa a yankin ciki kuwa har da janyewar ruwa a Tafkin Chadi wannan ya jawo matsaloli na tattalin arziki da zamantakewa, wadannan kalubale ba su kadai ba ne suka jawo ayyukan ta’addanci. Bincike da aka yi da dama (Various studies) sun tabbatar da cewa ayyukan ta’addancin na da alaka da nuna wariya ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki da sauyi na yanayi da ke shafar yankin da nuna wariya ta fuskar siyasa, ba kawai a ce janyewar da Tafkin Chadi ke yi shine sila ba.
Sauye-sauyen rikicin (dynamics of conflict) a yankin Tafkin Chadi yana da fuskoki da dama. Wannan yankin tsawon lokaci yana fama da rikice-rikice daga wadannan al’umma zuwa waccen da rikicin makiyaya da manoma, wanda a wasu lokutan ya kan fi ma rikicin na ta’addanci. Wadannan rikice-rikice sun kara ta’azzara, dalilin sauyin yanayi da rashin abubuwan da al’umma ke bukata don rayuwar yau da kullum wanda hakan ya sanya mutane da dama suke rikici kan wani abu da suke bukata don rayuwarsu, abubuwan da ke zama kadan.
Don haka duk da cewa sauyi da ake samu a yankin da al’ummar da ke zaune, yana da kyau idan ana so a fahimci rikicin da ke faruwa a yankin dole sai an kalle shi ta wasu fuskoki da suka hadar da dalilai na zamantakewa da tattalin arziki da siyasa.
Jita-jita ta 3: Yadda al’umma ke kara yawaita a yankin shi ne kai tsaye ya kawo rikici a yankin.

Hukunci: Akasari gaskiya ce
Ga misali akwai karuwar fafutuka kan wasu abubuwa na bukata kamar kasar noma da ruwan amfani saboda yadda ake samun bunkasar yawan al’umma da sauyin yanayi.
Yayin da wannan ke zama a kwai gaskiya a cikinsa, zaa iya cewa ba a zurfafa ba a kalli tarin abubuwa a dangane da rikicin da ke zama mai murdiya ko wanda ba za a fahimta ba kai tsaye. Fiye da maganar bunkasar jama’a akwai tari matsaloli na zamantakewa da tattalin arziki da ma batu na muhalli da za a alakanta su da rikicin. Ga misali rashin isassun abubuwan bukata da al’umma ke nema kamar filaye da ruwa sun karu saboda karuwar jama’a da ake samu a yankin da kuma sauyin yanayi. Akwai rahotanni da suka nunar da alaka (linked) ta karuwar tashin hankali a yankin saboda ayyukan gona da kamun kifi da kiwon dabbobi.
A kwai wasu tarin kullaceceniya (grievances) da ake alakantawa da talauci da rashin aikin yi da nuna wa wasu wariya wadanda suma ana ga suna da ta cewa kan rikicin na tafkin Chadi. Bayyanar masu tsatstsauran ra’ayi irin na Boko Haram ya kara jawo sarkakiya kan batun tsaro a yankin, kasancewar suna amfani da tashin hankali da ake fama da shi a yankin su kara jawo sabbin rikice-rikice. Don haka yawaitar jama’a daya ne daga cikin tarin matsaloli da ke jawo tashin hankali a yankin.
Jita-jita ta 4: Mayakan Boko Haram na wakiltar dukkanin Musulmi a yankin

Hukunci: Karya ce!
Yayin da Boko Haram ke da’awar cewa tana ayyuka ne da sunan addinin Islama, wasu nazarce-nazarce sun nunar da cewa akasari mabiya addinin na Islama a yankin basa goyon bayan wannan kungiya ta masu tsatstsauran ra’ayi da ayyukan da suke na ta’addanci. Shirin Raya Kasa na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) (documented) ya tattara bayanai da ke nuni da cewa su akansu al’umma Musulmi sune kan gaba cikin wadanda Boko Haram ke kaiwa hari.
Haka nan wani bincike (study) mai zurfi da Alex Thurston yayi ya nunar da cewa yayin da Boko Haram ke da’awar cewa ta fafutuka da sunan addinin Islama ce, ayyukan da take yi sun sabawa akidar mabiyan na addinin Islama, wadanda ke adawa da yadda mayakan ke gudanar da ayyukansu da ma fahimtarsu ga addinin.
Jita-jita ta 5: Al’ummar da ke yankin na Tafkin Chadi suna goyon bayan ayyukan ta’addancin.

Hukunci: Yaudara ce!
Al’umma da dama sun fuskanci gallazawa daga ayyukan ta’addancin kungiyar da raba su da muhalllansu da tilasta masu shiga ayyukan ta’’adancin (forced recruitme), sannan suna nuna turjiya (resist) ko kin kasancewa da kungiyar. Sannan batun cewa duk matasa a yankin suna tausayawa mayakan Boko Haram a yankin ba haka bane, kasancerwar da dama suna adawa da tsarinsu, kuma sun fi so a samar da zaman lafiya a yankin.
Kamar yadda ake nunarwa a kafafan yada labarai, wasu al’umma a yankin basu da zabi (have no choice) face su yi biyayya ga mayakan ko su rasa rayukansu.
Jita-jita ta 6: Farfado da Tafkin Chadi zai kawo karshen ayyukan ta’addanci

Hukunci: Yaudara ce!
Yayin da farfado da Tafkin Chadi da inganta muhallin yankin zai taimaka wajen shawo kan wasu daga cikin matsaloli na zamantakewa da tattalin arziki da suke ta’’azara rikicin, wannan ba shi zai kawo karshen ta’addanci ba. Yankin Tafkin Chadi na fama da tarin kalubale saboda ayyukan Boko Haram wanda ya karu dalilin sababai da dama da suka hadar da talauci da rashin tsayayyen tsarin shugabanci da zama cikin yanayi na cin dunduniyar juna da lalacewar muhalli.
Kamar yadda hukumar da ke kula da yankin na Tafkin Chadi da tallafin shirin Raya Kasashe na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) suka nunar, kokari na daidaita lamura a yankin sai ya hadar da (must include) bin hanyoyi da dama (multi-faceted approach).Wannan kuwa ya hadar da farfado da muhallin sannan al’umma su yi hakurin zama da juna da samar da damarmaki na tattalin arziki.
Jita-jita ta 7: Amfani da karfin sojan kasa da kasa shine mafita

Hukunci: Yaudara ce!
Dama akwai daukar matakai kala-kala da suka hadar da hadakar dakarun tsaron kasa da kasa na Multinational Joint Task Force (MNJTF) don kawar (clear out) da Boko Haram da burbushinta. Wadannan kungiyoyi sun dade suna gudanar da ayyukansu a yankin. Rahotanni (reports) a baya-bayan nan sun nunar da ci gaba da kai hare-hare, kamar wanda ya faru a Chadi, dakarun soja 17 da mayakan sakai 96 suka mutu, sai dai babu daya daga cikin wadannan matakai da ya kawo karshen tarin matsalolin da suka ta’azzara ayyukan ta’addancin.
Wasu lokutan ma ayyukan sojan na yin sanadi na kisan fararen hula da sanya su kauracewa muhallansu. Ga misali (For instance,) ayyukan na MNJTF sun jawo tarin kalubale ga al’umma.
Shirin (CONOPs) na dakarun na MNJTF ya gano (recognised) cewa amfani da karfin soja kawai ba zai warware matsaloli na siyasa da zamantakewa da tattalin arziki ba wanda ke jawo rashin zaman lafiya, maimakon haka an yi amanna sai an shigar da yunkuri ta fuskar siyasa da samar da ci gaba hadi da ayyukan na soja don samar da waraka a yankin.
Yayin da ake ganin amfani da karfin sojan kasa da kasa zai samar da waraka ta yanzu-yanzu, kwararru (experts say) sun bayyana cewa dole sai an dauki matakai da dama da za su hadar da daidaito na siyasa da zamantakewa da tattalin arziki don samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin na Tafkin Chadi.