African LanguagesHausa

Yadda bayanan da ba daidai ba ke kara fadada ajandar masu ra’ayin Biafra a shafukan sada zumunta tare da raunata dimokiradiyya

Getting your Trinity Audio player ready...

Ranar 21 ga watan Nuwamban 2024, mahukuntan kasar Finland suka cafke Simon Ekpa, wanda ke zamn daya daga cikin manyan kusoshin kungiyar ‘yan awaren Biafra, tare da wasu hudu wadanda su ma ake zarginsu da haddasa tashin hankali da daukar nauyin ta’addancin da ake dangantawa da tayar da kayar bayan da ake yi a yankin Kudu maso gabashin Najeriya. Ekpa wanda ke kiran kansa jagoran ‘yan kungitar IPOB kuma shugaban gwamnatin Biafra da ke gudun hijira ko kuma BGIE ya dade ya na amfani da soshiyal mediya wajen karfafa haramtacciyar dokar hana fita da kuma yada bayanan bogin da ke yawan haddasa tashin hankali a yankin.

Sai dai kamen da aka yi masa, bangare daya ne kawai na matakan da aka dauka wajen shawo kan yada bayanan da ba dai dai ba, wadanda ke jan hankali da ma kara yawan magoya bayan akidun ‘yan awaren na Biafra. Na wani tsawon lokaci yanzu, kafofin sada zumunta na soshiyal mediya sun zama dandalin yada bayanan da ba daidai ba, irin wadanda ke haddasa hargitsi irin na kabilanci, da kwaskware bayanan tarihi ta yadda za su harzuka jama’a da ma yada akidun ‘yan aware. Wannan habakar na akidu masu hatsari a dandalin yanar gizo ne ke sanya tambayar: Shin batutuwan da jama’a ke gani a intanet har suna yadda da su, nawa daga cikinsu ne gaskiya?

Sauyin da ke afkuwa a fagen bayanan da ke goyon bayan ‘yan aware

Biafra, ko kuma bayanan da ke goyon bayan ra’ayin ‘yan awaren Biafra, ba sabon abu ba ne wajen wadanda suka san tarihin Najeriya. Ana iya tushin tarihin kungiyar zuwa shekarun 1960 sadda Laftanan Kanar Odumegwu Ojukwu, wanda ya kasance gwamnan yankin gabashin kasar, ya ayyana rabuwar Biafra daga Najeriya, abun da har ya yi sanadin Yakin Basasar Najeriya (1967-1970). Duk da cewa an kammala yakin bayan da Biafra ta mika wuya ne, akidar ba ta taba gushewa ba. Ojukwu ya cigaba da kasancewa babban dan siyasa, mai rajin kare manufofin Inyamurai ko bayan da ya dawo daga samun mafakar siyasa a 1982.

Turjiyarsa da  hangen nesa da sa kai da ma guna-gunin da ya ke da shi na yadda ya ke ganin an nuna musu wariya su ne suka kasance tubalin da sauran masu ra’ayi irin nasa suka dora. ‘Yan gwagwarmaya irin su Nnamdi Kanu da Simon Ekpa sun gina kungiyoyinsu ne su ma a kan hakan – duk da cewa na su kungiyoyin  sun fi kaifin kishi sa’nnan sun faye amfani da kafofin sada zumunta na zamani.

Nnamdi Kanu ya yi suna ne bayan da ya hadasa tashe-tashen hankulan da ke da dnasaba da kabilanci ya kuma kalubalanci daidaiton dimokiradiyyar Najeriya. Ta yin amfani da gidan rediyon Biafra da dandalolin yanar gizo-gizo, ya yada bayanan da ba daidai ba, ya haddasa tayar da kayar baya, ya kuma janyo turjiya da boren bijirewa gwamnati.  Kalaman batancin da ya rika yi ne suka haddasa artabun da aka samu tsakanin jami’an tsaro da mambobin IPOB, wanda ya kara ta’azzara rashin tsaro a yankin Kudu maso gabashin. Mutun wanda gwamnatin Najeriya ta kira dan ta’adda, ya fara shiga hannun mahukuntan ne a shekarar 2015 inda aka kama shi da zargin cin amanar kasa amma ya tsere bayan da aka ba shi beli. Sai dai a shekarar 2021 an sake kama shi aka maido shi cikin kasar, wai daga Kenya bayan da ya cigaba da zurfafa kiraye-kirayen ballewa, abun da ya kara barazana ga zaman lafiya da kasancewar kasar dunkulalliya.

Bayan da aka kama Kanu nei shi kuma  Simon Ekpa ya mayar da kansa sabuwar muryar kungiyar, inda ya sake daukar wasu karin matakan da suka fi kaifi tare da amfani da  kafofin sada zumunta. Ba kamar Kanu ba wanda ya ja hankalin mutane ta yin amfani da gidan rediyon Biafra, Ekpa ya yi amfanni da kafofin sada zumuntan soshiyal mediya ne tamkar makamai, musamman dandalin X wanda aka fi sani da twitter, wajen tura akidun aware da kuma bayanan da ba daidai ba wahen haddasa rikici a yankin Kudu maso gabashin Najeriya. DUBAWA ta dade tana karyata yawancin da’awar da ya ke yi, wadanda suke tasiri sosai a ire-iren batutuwan da ke daure wa kungiyar gindi. Kuna iya ganin wasu daga cikinsu a  nan, nan, nan, nan, da nan.

A cikin watan Fabrairu, DUBAWA ta sanya ido sosai kan shafukan da ke yada akidun Biafra a Facebook wadanda yawanci suke sukar mulkin dimokiradiyyar kasar, suna dore laifin ta’addanci kan wadansu yankuna tare da  rashin daidaito, da kuma yada bayanan  karya.

Wadansu daga cikin shafukan sun hada da Nwa Biafra InfoTv, Biafra Republic, Biafra Republic 2, Biafra Freedom, Biafran Airlines, Biafra People Worldwide, Freedom Channel,da ma wasu da dama wadanda suka rika yin irin wadannan bayanan

Rabar 7 ga watan Fabrairu, DUBAWA ta wallafa wani binciken da ya karyata wata da’awar da Nwa Biafra InfoTv ta yi. Shafin ya wallafa wani bidiyon karya wanda ya  nuna wai wani abin da ya faru a jihar Oyo inda aka kama wasu matsafa sun yanyanka gabobin mutane. To sai dai bincike ya nuna cewa bidiyon wani tsohon abu ne da ya faru a shekarar 2024.

Haka nan kuma wasu karin bayanan wadanda ba daidai ba su ma sun bulla a cikin wadannan shafukan. Bayan da aka sace  Prince Eniola, shugaban kungiyar matasa ta Afenifere ranar 17 ga watan Fabrairun 2025 yayin da ya ke kan hanyar sa na zuwa Abuja, tsakanin jihohin Ondo da Kog, shafin Facebook na  @Biafran Airlines ya wallafa wani bidiyon mutumin da aka kama ya na neman tallafi ana rike da bindiga a kirjinsa.

Tsokacin da aka yi a karkashin batun ya bayyana wannan abun da ke faruwa. A maimakon nuna fushi ko takaici, yawanci daga cikinsu sun nuna halin ko in kula ne kawai ba su ma dauki abun da mahimmanci ba, a maimakon haka ma sai dai suka mayar da hankali kan wanda ke da laifi. Wani mai amfani da shafin, @AlohInnocent, cewa ya yi: “Ku kira Tinubunku mana, shi ne shugabanku.”

Ganin yadda mutane ke ma’amala da wadannan shafukan, inda dubbai ke bin shafukan wasu da dama kuma suke raba ire-iren abubuwan da suke wallafawa ne DUBAWA ta ga cewa irin wadannan akidun na da hadari. Yada irin wadannan bayanan marasa gaskiya na kai ga rashin uadda, kuma saurin yaduwar bayanan na iya dakile bayanai masu sahihanci ta yadda zai kare mahawarori masu lafiya wanda kuma zai iya haddasa rikicin kabilanci, rashin tsaro da kuma mafi mahimmanci hari a kan mulkin dimokiradiyya.

Da me da me ya kamata a yi?

  1. Fadawa mutane gaskiya: Bai kamata a ce binciken gaskiya ya kasance dan karyata zarge-zarge ne kadai ba. Ya kamata zama hanya ta bayyana gaskiya. Labarai ne ke tasiri a kan jama’a ba alkaluma kadai ba. Idan har aka tantance gaskiya a cikin labarai, hotuna da ma harsunan gargajiya, bayanan gaskiya za su fi samun karbuwa fiye da yadda bayanan da ba daidai ba ke samun gindin zama.

  1. Idan har aka tsabtace manhajojin an tsabtace matsalar: Kafofin sada zumunta na taka rawar gani sosai wajen yaduwar bayanai, domin wasu manhajojin sun fi bai wa yawan masu ma’amala da shafin fifiko a kan gaskiya ko fahimta. A maimakon barin bayanan da ba daidai ba su yi tasiri ya kamata dandalolin su mayar da hankali kan kafofi masu nagarta. Idan har suka yi aiki da masu binciken gaskiya da masu bincike, da kamfanonin fasaha da duk sauran fannonin da za su iya tasiri a wannan fannin.

  1. Kawo tattaunawar ga jama’a: Bayanai wadanda ba daidai ba sukan yi tasiri ne inda mutane sukan ji kamar ba’a sauraronsu. A maimakon yin watsi da wadanda suke kawo bayanan karya, ya kamata a rika tattaunawa mai ma’ana tare da su. Tattunawa a majalisu, da ma a kan intanet da sauran hanyoyin ganawa da al’umma za su taimaka wajen shawo kan irin wadannan matsalolin yayin da a hannu guda kuma za’a rika ba su bayanai masu sahihanci. Infuluwensas da malaman addini da kuma masu ruwa da tsaki a al’ummomi za su iya kasancewa kawaye wajen yaki da tasirin bayanan da ba daidai ba. Mutane za su fi yarda da mutanen da suka riga suka saba sauraro.

A Karshe

Bai kamata a yi wa bayanan karya dangane da Biafra kallon cewa yankin kudu maso gabas ya shafa ba ko kuma ma matsala ce da ba ta da tasiri a sauran yankunan Najeriya. Bayanai marasa gaskiya ba haka nan suke ba, musamman a wannan zamanin na soshiyal mediya inda bayanan kasashen ketare ma ke tasiri a kasashen da ko kusanci ba su da shi. Shawo kan matsaka irin wannan na bukatar hadin kai tsakanin kwararru, masu binciken gaskiya, masu rubuta manufofin kasa, da dandalolin fasaha dan shawo kan yaduwar bayanan karya ta yadda za su tabbatar da daidaito a fannin demokiradiyya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »