Hadakar kungiyoyin tantance gaskiyar bayanai a Najeriya wato Nigerian Fact Checkers’ Coalition (NFC) a wani mataki na sauke alhakin da ya rataya a wuyarsu ta yadda ya danganci taimakawa jama’a ta hanyar yakar bayanai marasa gaskiya a Najeriya, kungiyoyun sun bayar da gudunmawarsu a mahawarar da aka shiryawa ‘yan takarar shugabancin Najeriya ranar 13 ga watan Nuwamban 2022
Hadakar kungiyoyin sun rika bincika duk wani zargi da ‘yan takarar suka yi a lokacin mahawarar dan karyata shi ko kuma amincewa da shi kai tsaye a lokacin da ake mahawarar.
Taron na ranar lahadi ya sami bakuncin ‘yan takarar shugaban kasa daga jam’iyyun African Action Congress, Omoyele Sowore, Action Democratic Party, Yabagi Sani, All Progressive Grand Alliance, Prof. Peter Umeadi da Social Democratic Party, Prince Adewole Adebayo.
Babban editan Cibiyar Kasa da Kasa na Gudanar da Bincike a aikin jarida Ajibola Amzat ya kwatanta taron a matsayin wata dama ta musamman da ‘yan takarar za su yi musayar bayanai da ‘yan Najeriya. Inda ya ce:
“Kada mu dauka ko da wasa cewa bayanai da ‘yan takara za su bayar nagartattu ne. Shi ya sa rawar da hadakar kungiyoyin binciken gaskiya ya ke da mahimmanci ga wadannan mahawarorin da mu ke yi.”
Editan DUBAWA Kemi Busari ya bayyana gamsuwarsa da irin gudunmawar da masu binciken su ka bayar kawo yanzu.
A hankali a hankali muna ganin ‘yan siyasa na hankali da irin kalaman da suke furtawa. Wannan na nuna irin aikin da masu binciken gaskiyar bayanai a Najeriya su ka yi wajen kara inganta dimokiradiyya
Ya ce hadakar a shirye ta ke ta bayar da bayanai masu mahimmanci lokacin zabe kuma muna fata wannan zai taimaka wajen rage bazuwar labaran bogi dan bai wa ‘yan kasa bayanai masu sahihanci wadanda za su taimaka mu su wajen yanke shawarwarin da su ka shafi siyasa.