African LanguagesHausa

Keyamo ya yi kuskure a furucinsa na hauhawar farashin kayayyaki

Zargi: Najeriya ta yi fama da hauhawar farashin kayayyaki mafi tsanani a tarihinta, lokacin da Obasanjo da Atiku ke mulki

<strong>Keyamo ya yi kuskure a furucinsa na hauhawar farashin kayayyaki</strong>

Hauhawar farashi mafi tsanani ya afku a Najeriya ne a shekarar 1995, a yayin da wa’adin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fara a 1999 ya kuma kammala a 2007. Don haka wannan zargin ba gaskiya ba ne. 

Cikakken bayani

Mai magana da yawun majalisar yakin neman zaben shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC Festus Keyamo ya sake sukar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da jam’iyyarsa inda ya ce a tarihin Najeriya, lokacin da Atiku ya mulki da tsohon shugaban kasa Olusegin Obasanjo ne aka ga hauhawar farashin kayayyaki mafi muni a kasar.

Mr Keyamo ya fadi haka ne yayin da ya ke hira da gidan talibijin na Arise TV ranar 16 ga watan Janairun 2023.

Haka nan kuma jaridar Vangauarf ta yi rahoton cewa Keyamo ya ce hauhawar farashin kayayyakin da ake gani a karkashin gwamnatin Buhari, ba shi ne mafi munin da aka taba gani a kasar ba.

“Ba wannan ne hauhawar farashin kayayyaki mafi muni ba. A shekarar 2005 a karkashin Obasanjo da Atiku, mu ka sami mafi muni,” ya bayyanawa jaridar ta Vanguard.

Wannan na zuwa ne bayan da jam’iyyun biyu suka yi ta sukan juna a lamuran siyasa, ganin yadda su ka fara ja-in-ja tun da su ka gane irin tasirin da jam’iyyunsu biyu ke da shi a fagen siyasar kasar.

Domin sarkakiyar da wannan batun ke da shi, da ma irin tasirin da ire-iren wadannan maganganun za su iya yi a zabukan masu zuwa, DUBAWA ta ce za ta tantance.

Tantancewa 

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar mataimakinsa sun jagoranci Najeriya daga 1999 zuwa 2007. Tsakanin wannan lokacin da suka yi wa’adi biyu, a shekarar 2001 ne tattalin arzikin kasar ta fuskanci koma baya har aka sami hauhawar farashin kayayyaki inda aka samu karin kashi 18.87 cikin 100 aka kuma cigaba da samun karuwa da kashi 11.94 cikin 100 kowace shekara.

A yanzu haka, wato daga karshen watan Disembar 2022 hauhawar farashin kayayyakin na kan kashi 21.34 cikin 100, inda ma bisa bayanai ya ma sauka ke nan da kadan a watan jiya,  abin da ya dakatar da karuwar da ya cigaba da yi na tsawon shekaru 17 yanzu.

Binciken da aka yi kan yadda sauye-sauye a halayen al’umma wajen sayen kayayyaki, an sami jerin abubuwa da dama da suka yi nazarin yanayin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya tun bayan da ta sami ‘yancin kanta a 1960. Karin binciken bayanan da alkaluman suka bayar ya nuna mana cewa tun da Najeriya ta zama kasa mai cin gashin kanta, kasar ta fuskanci hauhawar farashin kayayyaki mafi tsanani a shekarar 1995 da kashi 72.84 cikin 100 bayan da rika karuwa da kashi 15.80 cikin 100 a shekarar da ta gabata.

Haka nan kuma WorldData info ita ma ta bayar da rahoto makamancin wannan yayin da ta ke gwada yanayin hauhawar farashin kayyaki a Najeriya da na Amurka da Turai. A rahoton, ita ma 1995 ta rubuta a matsayin shekarar da aka yi fama da hauhawar farashin kayayyaki, da kashi 72.84 wanda dadain shi ne kadai irin shi a tarihin kasar.

A Karshe

Bayanin Mr Keyamo ba daidai ba ne. A tarihin hauhawar farashin kayayyaki na Najeriya, shekarar 1995 ce ta samun adadi mafi muni, wanda kuma ya kasance shekaru hudu kafin Obasanjo ya kama mulki a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button