African LanguagesHausa

Mutanen da ke hijira a tsohon bidiyon da ke yawo, ‘yan Burkina Faso ne ba wani wuri a jihar Nejar Najeriya ba

Zargi: Wani mai amfani da shafin facebook ya wallafa wani tsohon bidiyo yana zargin wai wasu al’ummomi ne a kauyukan da ke jihar Nejar Najeriya suke tserewa daga hare-haren Boko Haram da ‘Yan bindiga

A shekarun da suka gabata, ‘yan Najeriya sun yi ta fama da matsalolin tsaro. Daga kungiyar Boko Haram zuwa ‘yan bindigan da ba’a san ko su wane ne ba, ‘yan Najeriya da dama sun rasa rayuka da dukiyoyinsu.

Kwanan nan jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an kashe mutane 2,968 sa’anan an sace wasu 1,484 tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2022.

Sakamakon wadannan abubuwa, a kullayaumin ‘yan Najeriya ke bayyana ra’ayoyinsu a soshiyal mediya domin samar da bayanai ga ma’abotansu na shafin dangane da lamuran tsaron da suka addabi kasar. Wani misali mai kyau shi ne labarin da wani mai amfani da shafin Facebook da sunan Exodus Biafra TV ya wallafa mai tsawon sakan 30 wanda ke zargin cewa mutane na barin gidajensu domin Boko Haram da ‘yan bindiga na kashe su kowace rana.

Mun kuma sake gano wani shafin na Olamide Sulaimon TV wanda shi ma ya sanya bidiyon yana zargi wai mutanen sun fito jihar Neja ne. Wannan labarin ya ja hankali sosai, dubban mutane suka kalla bidiyon a yayinda wasu sama da 100 kuma su ka yi tsokaci. 

Bisa la’akari da yawan ma’abotan shafin wadanda su ka kai sama da 4,000 da ma yawan mutanen da suka yi ma’amala da wananan labarin ne ya sa muke so mu fayyace gaskiya.

Tantancewa

Da muka yi amfani da manhajar tantance hotunan bidiyo na Invid WeVerify, DUBAWA ta gano cewa reshen binciken gaskiyar rahotanni da labarai na Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ta riga ta bincika sahihancin bidiyon..

AFP ya gano cewa harshen da aka yi amfani da shi a bidiyon ba na Najeriya ba ne. Yaren Moore ne wanda ke daya daga cikin harsunan da aka fi amfani da shi a Burkina Faso.

Mun kuma gano cewa tun 2021 aka yi bidiyon kuma a yanzu haka yana kan wani shafin YouTube mai suna Lobs Paalga TV.

Bidiyon na YouTube na dauke da taken da aka rubuta kamar haka “Vidéo d’un exode attribué aux habitants de Solhan” wanda ya nuna cewa ba harshen Najeriya ba ne. 

Dan haka sai muka yi amfani da manhajan fassarar Google dan tantance ma’anar abin da aka rubuta. Da turanci ma’anar ta kasance kamar haka “Video of an exodus attributed to the inhabitants of Solhan.” Wanda a hausa ya ke nufin : Ana danganta bidiyon da ficcewar da mazauna Solhan ke yi.

Ranar 6 ga watan Janairun 2021, BBC ta rawaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 160 a wani harin da suka kai kan wani kauye a yankin arewacin Burkina Faso. Solhan na daga cikin wuraren da ‘yan bindigan suka kai harin,

A ranar da labarin BBCn ya bulla aka sanya wannan bidiyon a YouTube, kuma gidan talbijin na Al Jazeera ma ya rawaito cewa iyalai sama da 7, 000 sun kauracewa gidajensu da ke yankin arewacin Burkina Fason sakamakon hari mafi munin da aka taba kaiwa yankin na tsawon shekaru masu yawa yanzu

A karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa bidiyon na mazauna kauyen Solhan ne a Burkina Faso ba mazaunan jihar Nejar Najeriya kamar yadda mai amfani da shafin Facebook din da ya wallafa ke zargi. Dan haka wannan labarin ba gaskiya ba ne

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button