African LanguagesHausa

ZoomUpYourLife: Yadda masu zamba cikin aminci suka yi amfani da shirin garabasar Peter Okoye suka yaudari ‘yan Najeriyan da ba su ji ba su gani ba ta wayoyin da suka rika yi daga manhajar WhatsApp

Na tsawon wani lokaci yanzu, zarge-zargen da ba’a riga an tabbatar na dangane da zamba cikin amincin da ake yi wa Peter Okoye, shaharraren mawakin Najeriyar nan wadanda har yanzu ba su kai ga kakkautawa ba. A lokuta da dama, wasu ‘yan Najeriya sun yi amfani da shafukansu na soshiyak media suna zargin cewa mawakin ya cinye musu kudi ta hanyar wani shirin caca da ake kira Zoom Lottery Scheme ko kuma ZoomUpYourLife. Duk da cewa mawakin ya karyata wannan zargin sau da yawa ya kuma yi gargadin cewa masu amfani da shirin mazambata ne wadanda ba shi da wata alaka da su kuma a guje su, ‘yan Najeriya da dama sun cigaba da fadawa hannun mayaudaran – wadanda ke amfani da kasaitattun dabaru na zamani wadanda ke bayyana kamar gaskiya har ma mutane ba su iya gane cewa yaudararsu ake yi. A wannan rahoton, Elzabeth Ogunbamowo na DUBAWA ta kwance mana zare da abawar yadda irin wadannan barayin ke gudanar da ayyukansu.

Shafukan sada zumuntan Peter Okoye sun nuna cewa yana da wata dandali na soshiyal mediya wanda ke tallar wata garabasa mai suna Zoom Up Your Life. Kamar yadda aka bayyana a shafinsa na Instagram, wadanda ke da sha’awar su shiga na yi yin haka bayan sun sayi tikiti a shafinsa daga nan kuma sai su kalli shirin a talibijin inda mawakin ya kan sanar da lambar mai tikitin da ya yi nasara. Yawanci bayan sanarwar, ya kan kira wanda ya yi nasarar da kansa yana amfani da wayar bidiyo ya taya su murna.

An shafe watanni da dama ana yin hakan, amma a watan Yulin 2022, mawakin ya sanar cewa  zai daina kiran wadanda suka yi nasara da kansa inda ya ce mutane da yawa na yin shiga irin na sa su yaudari jama’a. A wancan lokacin Mr. Okoye ya sanar cewa manajansa zai cigaba da kiran zakarun.

Kafin nan, mawakin wanda aka fi sani da Mr P, ya sanar da masu bin sa a shafukan soshiyak media cewa ya daina yin waya ta bidiyo da zakarun gasar yayin da ya bayyana musu irin dabarun da masu yaudara ke amfani da shi wajen ayyukan zambansu a shafukan Facebook daban-daban ya ma ce sukan yi kokarin fid da kama su yi shiga irin na sa kamar yadda ya bayyana a nan, nan da nan

Ya kuma wallafa wasu daga cikin takardun kotun wadanda aka kama suna shiga irin na sa aka kai su kara. Bugu da kari, mawakin ya gargadi miliyoyin wadanda ke bin shi a shafukan sada zumuntan da su guji fadawa tarkon mayaudara.

Hawaye, nadama…wadanda abun ya shafa sun bayyana mawuyacin halin da suka kasance da masu shiga irin na Okoye

Wadansu daga cikin wadanda suka fada hannun mazambatan, wadanda suka yi hira da DUBAWA, sun bayyana mana yadda suka yi asarar dubban nerori saboda hujjojin da aka ba su – wadanda suka sanya su tunanin cewa a zahiri, mawakin ne suke magana da shi.

Yawancin lokuta mutanen sun ce sun dan yi shakkan sahihancin wasan amma bayan da suka sami waya daga mawakin da kansa ta WhatsApp – inda mayaudaran suka gamar da su dangane da sahihancin wasan – sai suka amince amma kuma aka yaudare su daga baya.

Wadanda suka zanta da  DUBAWA, sun ce lallai sun yi imanin cewa mawakin da kansa ne ya yaudare su tunda sun yi magana da shi.

Daya daga cikin su, Jude Ndu, wanda ke aiki a matsayin masin dan ya samu ya biya kudin makarantarsa ya hakikance cewa babu wanda ya yi amfani da wayar ya yaudare sa mawakin ne da kansa yana bayar da hujjar irin ma’amalar da suka yi da ma yadda ya rika amsa tambayoyinsa da sauransu.

Na tabbata da abin da na ke fada. Ya kira na da bidiyo kuma mun yi magana mai ma’ana sosai dangane da garabasar tasa. Har sai da na yi kwalla, ya rika ce mun ka da in yi kuka dan haka ba za ku ce mun ba P-Square (Peter Okoye) ba ne. Ina ce muku waya ta bidiyo, mun yi wayoyi da yawa wadanda babu hotuna, amma wannan wayar da bidiyo muka yi. Kada ku bari mutane su ce muku ba Peter Okoye ba ne; shi ne,” ya bayyana.

Ndu ya ce ya biya masu yaudarar N680, 000 sabida ya so ya biya kudin makarantarsa baki daya, amma a yanzu haka, kudin da ya sa da kudin da ya zaci zai samu duk sun tafi kuma dole yanzu ya dakatar da makarantar ta sa har zuwa wani lokaci nan gaba sadda zai sami kudin saboda wannan iftila’in da ya afka masa.

“Ranar 28 ga watan Fabrairu, ina dan bincike na a shafukan soshiyal mediya sai na ga shafi Zoom Lifestyle, sai na ce bari in shiga. Da na shiga sai ya kira ni kai tsaya ta waya a bidiyo. Na ga fuskarsa, ba’a gyara komai ba. Ya tambaye ni ya ce tikiti nawa na saya, na ce na sayi guda daya na N10,000; ni dalibi ne. Bayan da na biya sai ya ce na ci N250,000. Na yi murna sosai. Bayan nan sai ya tura mun sauko da sautin muryar sa ya ce in tabbata na yi amfani da kudin yadda ya dace kuma kada in bannatar da shi. Na yi masa godiya na nuna cewa ina cike da farin ciki.”

Ndu ya kara da cewa ‘Mr Okoye’ ya bukace shi ya biya wani karin kudi N22, 500. Sadda ya tambayi dalilin wannan karin kudin, sai mai yaudarar ya ce masa ya yi abun da aka ce ya yi tukuna kafin ya sami amsa. Ndu ya ce sai ya yi biyayya kawai saboda matsayinsa tauraro ya kuma yi imanin cewa Mr Okoye ba zai taba yaudararsa ba.

“Bayan haka, sai ya fada mun cewa wata mata za ta kira ni kuma idan ta kira, in bi duk umurnin da ta ba ni. Matar sai ta kira ni ta ce in ba ta N50,000 saboda an kara yawan kudin da zan samu zuwa N500,000.

Da ta fadi haka, ban yarda da ita ba, dan haka sai na kira Peter Okoye ta video kuma na fada masa cewa ni ban gane abun da ke faruwa ba, shi kuma ya ce mun in yi biyayya kawai; wannan wayar da na yi ta bidiyo sai ya kara mun karfin gwiwa. Daga nan jimilar kudin da na tura masa a ranar kawai ya kai N250,000. Layin yanar gizo-gizo ba kyau ranar, dan haka sai na yi amfani da POS. Washegari, sai na kira shi na ce ya tura mun kudi na, amma ya ce sai ya tuntubi wani tukuna. Daga baya sai ya sake kira na ta bidiyo ina kuka, ya ce ina da sa’a sosai domin na ci nera miliyan daya.”

Mutumin ya ce watakila sun yi mi shi magani ne saboda yadda ya rika biye musu ba tare da jayayya ba.

“Ba zan iya kwatanta abun da ya same ni ba, shi kansa mai na’urar POS din sai da ya tambaye ni ya ce ina lafiya kuwa. Na kuma tabbatar masa cewa lafiya ta kalau.”

Ya ce mayaudaran sun yi nasarar anshe mi shi kudinsa da kadan – da kadan ta hanyar wayar bidiyo da sakonnin WhatsApp.

Wata ita ma wadda abun ya shafa wadda ta rasa N350,000 ta fadawa DUBAWA cewa mawakin ne da kansa ya kira ta a bidiyo sau da yawa wanda a ra’ayinta shi ne ya ba ta tabbacin sahihancin shirin.

Ta ce ta tura kudin amma ba ta sami komai ba bayan da ta gama tura kudin, duk da cewa ‘tauraron’ – ta na nufin Mr. Okoye – ya kira ta a bidiyo ya na mata alkawarin cewa za ta sami yawan kudin da ta ci. Ita ma ta ce da jin haka sai ta fashe da kuka, bayan da shi kuma ya yi alkawarin zai saki kudin da zarar ta biya N51,000 sau uku. Ta yi imani da shi saboda matsayinsa na tauraron da ake ji da shi a Najeriya amma duk da haka aka yaudare ta.

Shin Mr Okoye ne kan kira a wayar da kansa?

Nazari mai zurfi kan sautin muryoyin da aka nada wadanda DUBAWA ta samu daga masu zargin sun nuna banbanci sosai tsakanin ainihin muryar Mr. Okoye da ta wadanda ke yaudarar jama’a wanda bayan ya kammala magana da wadanda ya ke so ya cuta sai ya tsine wa kansa da rabin P-square dan mutanen su yarda, ya ce Allah ya la’anta shi idan har yana kokarin yaudarar su ne.

Shin ana iya magudi a yi waya da bidiyo a WhatsApp?

DUBAWA ta gano cewa akwai wadansu manhajoji da akan iya amfani da su wajen yin magudi idan ana amfani da wayar bidiyo; wadda aka fi amafni da ita wajen magudin ana kiranta ManyCam – Kyamara ce mai saukin amfani wadda ake yi amfani da ita wajen watsa bidiyoi kai tsaye a shafukan watsa bidiyoyi, da manhajojin da akan iya wayar bidiyo da ma kayayyakin koyon karatun da ake iya amfani da su a gida..

Idan har aka sanya ta a cikin komfuta, manhajar na bayar da damar dora bidiyoyin da aka riga aka nada, daga na sai a gyara bidiyon yadda za ta yi daidai da komfutar da ake amfani da ita. Daga nan ana iya sauya kyamarar komfutar da ta Manycam wanda zai rika nuna hoton bidiyon da aka nada a maimakon abun da ke faruwa a zahiri.

Akwai ma wasu abubuwa a manhajan da kan taimaka wajen cire ainihin muryar da ke cikin bidiyon sadda aka nade ta, wannan kan taimaka wa wanda ke amfani da bidiyon ya rika magana kai tsaye da wanda ya ke so a inda zai rika amsa tambayoyi yana kuma mayar da martani yadda ya kamata a sadda ake wayar.

Misali, yawancin wadanda aka damfara sun ce sadda suke magana da Mr Okoye ( ko kuma wanda ya yi shiga irin ta sa ya yaudari jama’a) sun yi kuka, kuma da suka fara kukan sai ya tambaye su abun da ke sa su kuka — wanda kuma shi ne ya kara karfafa su suka ga kamar da gaske shi ne.

Sakamakon binciken DUBAWA

DUBAWA ta gudanar da bincike a Facebook inda ta gano shafuka da dama da aka kirkiro a sunan Zoom Lifestyle – shirin garabasar ta Peter Okoye. Abun da ya fi tashe a sunayen da aka yi amfani da su wajen bude shafukan sun hada da “zoom”, “lifestyle” “Giveway” Mr P” “P Square da “Mr Okoye” na zaman kadan daga cikinsu.

Dukkansu na dauke da hoton mawakin a babban shafin wanda ke nuna cewa shafinsa ne. Yawancin shafukan da kan danganta kansu da Mr. Okoye su kan shawarci da a bayar da kudi mai yawa dan a fi samun kudi.

Kamar yadda aka bayyana a cikin sakonnin, idan mutun ya biya kudi da yawa wajen sayen tikiti, damar yin nasarar cin kudi da yawa za ta karu. Babban sakon da aka sanya a cikin shafukan shi ne babu wanda ke rasa kudi a wasan domin tauraron (‘yan damfarar da suka kirkiro shafukan) na amfani da dandalin ne ya taimakawa ma’abotansa.

Kamar yadda aka saba gani da shirye-shiryen damfara, akwai labarai daga shaidun da suke zargin wai sun yi nasara kuma an biya su kudaden a zahiri.

Bacin haka, akwai wani adireshin da aka hada da wata lambar WhatsApp daga karshen sakon wanda ke bukatar wadanda suke sha’awa su shiga wasar dan samun kira ta bidiyo daga mawakin. Yawanci budaddun shafuka ne a Facebook, abun da ke sa shi kasancewa da sauki jama’a su yi amfani da su, ko da shi ke akwai shafukan da ba kowa ke shiga ba amma kuma su kansu ana amfani da su wajen yaudara.

Bayan da muka sami wadannan bayanan tare da na abubuwan da su ka faru da wadanda suka fada hannun ‘yan damfaran, sai ni ma na zama sojan gona na yi amfani da sunaye biyu na yi rajista na bude shafin WhatsApp. Sunayen sun hada da Titilayo Adedunmoye da Titilayo Oladunjoye.

Da wannan lambobin na WhatsApp sai na fara bin adiresoshin da aka yi talla na fara magana da barayin da ke kiran kansu “taurari” a lokuta da dama.

Na fara da lura da salon da suke amfani da shi su tattauna da ni. Bayan da na tura sako na ce ina da sha’awar shiga garabasar, wanda ya amsa ni sai ya turo rukunnai daban-daban na azuzuwan shirin da suke saidawa zuwa ga ‘player’ ko dan wasa – abun da suke kiran wanda ke da niyyar shiga. Wadannan rukunnan sun hada da ‘dalibi’, lu’u-lu’u, zinari da sauransu wanda kowanensu na da nasa farashin.

Daga nan sai suka ce in tura bayanai na tare da lambobin asusun banki na domin ya taimaka musu wajen tura kudi maza-maza ina yin nasara bayan an bayyana wadanda suka ci.

Sai na tura na bogi na ce musu akwai matsala da nawa asusun shi ya sa na ke bayar da na wani abun da kuma suka amince da shi ba su yi wata gardama ba. To sai dai wannan wata hanya ce na samun bayanan bankin dan in tabbatar ko suna Mr Okoye ne ke kai.

Daga nan sai suka kira ni da fuskar Mr Okoye dan su tabbatar mu cewa da shi na ke harka kai tsaye. Ana iya ganin bidiyon hirar mu a nan. Yawancin lokuta sautin muryar ba ta zuwa daidai da yadda bakin shi ke motsi, kuma wayar ba ta taba wuce sakiku 30, watakila dan kada a dago su.

Wata sa’a kuma wanda ke kira zai rufe muryar wanda mutun zai iya gani a kan hoton bidiyon, ta yaada zai gyara muryar zuwa wadda ke kama da ta tauraron (wato Mr Okoye). Wannan ya afku akalla sau biyu sadda na yi ma’amala da su.

Yayin da mu ke tattaunawa, masu amfani da fiskar Mr Okoye wadanda ke amfani da shafukan facebook daban-daban sun kira ne sau uku a lokuta daban-daban da shafukan WhatsApp su ma daban-daban.

Haka nan kuma a daya daga cikin bidiyoyin, Mr Okoye ya fito a sunkuye.

Akwai abu daya da sukan fada daga sun dauki waya: “Barka da rana, Titilayo Oladunjoye daga jihar Ogun, yaya muka same ki yau? Ki kwantar da hankalinku da ni ki ke magana kai tsaye…. Ba ki da wata damuwa… bari in kira wanda ke bayan ki.”

Wayar ta kan dauki tsawon dakika 20 zuwa minti daya, inda daga nan kuma sai ta katse. A gani na yawancin mutanen wadanda ba su ji ba su gani ba, sukan ga kamar rayuwarsu za ta sauya baki daya zuwa wani abun da zai kare su har abada.

DUBAWA ta iya gano wani hoton bidiyo  a matsayin daya daga cikin bidiyoyin da suke gyarawa su yaudari jama’a yayin da take gudanar da wannan binciken.

Wannan ‘yar jaridar ta lura cewa akwai matsaloli da yawa a sunaye da lambobin bankin da suka rika bayarwa, kuma abun mamaki akwai guda daya cikinsu da ke da sunan mawakin watao Peter Okoye wanda ke bankin Guaranty Trust Bank da lambar 0762974909

Sauran sunayen banki da lambobin da aka bayar sun hada da Esther Sylvester 1718406713, Access Bank; Peter PSquare 9167298763 Palmpay; Peter Ekuoye, 2736898131, Paga Bank; Samuel Paul, 9037263811, Palmpay; Okoyes Okoye Peter, 9064598785, Palmpay; Pawa (Charity Uwakwe), 9985154483, Providus Bank and David Abraham, 9550452794, Palmpay.

DUBAWA ta tuntubi wasu daga cikin bankunan da suka ce sun yi rajista dan jo ko ma’aikata sun lura da wani abun da ba daidai ba da ke gudana a asusun da ke dauke da wadannan lambobin, sai dai sa’o’i 48 da rubuta mu su wasika ta imel babu wanda ya amsa tambayramu.

Shafukan Facebook din da muka san suna da alaka da ‘yan damfarar 

DUBAWA ta lura da wasu daga cikin shafukan da aka kirkiro a Facebook kawanan nan da niyyar damfarar jama’a wasu daga cikin shafukan na da mabiya biyar ne kadai. Masu amfani da shafukan yawanci sukan yi talla ne wanda zai kai ga dubban jama’a da tsohon bidiyon Okoye yana magana da wadanda suka yi nasara a garabasar ta sa.

Sukan kuma wallafa labarin nasarar da aka yi bayan sun dauko shi daga nagartacciyar shafin soshiyal mediyar Peter Okoye, ta yadda za su ji dadin yaudarar jama’an da ba su ji ba su gani ba.

Haka nan kuma, bayanan shaidu wadanda suka yi nasara a garabasar sun cika shafin a daidai wajen da maziyarta shafin kan yi tsokaci ta yadda jama’a za su ga kamar komai gaskiya be. ‘Yar jaridar ta kzma lura da cewa wasu shafukan ma musamman dan wannan shiri na Peter Okoye aka kirkiro su.

Duk da cewa ire-iren shafukan na da yawa, ‘yar jaridar ta yi gano wadansu daga cikin shafukan kuma sun hada da: Zoom Lifestyle Giveaway By Mr Peter Okoye, Zoom Lottery Mr P, Zoom Lottery Giveaway, Zoom Lottery giveaway, Mr P Zoom Lifestyle Giveaway, Zoom lifestyle ticket, Mr p Zoom lifestyle giveaway, zoomlifestyle lottery giveaway, Zoom lifestyle’s giveaway, Zoom lottery giveaway, Gotv, Peter okoye Zoom giveaway, Peter okoye zoom giveaway.

Daya daga cikin su wanda ke da mambobi sama da 7, 000 wanda kuma ake kira Mr P Zoom Giveaway LIfestyle, shi ma na amfani da salo irin na sauran yana ingiza mabiya su biya kudi kalilan dan samun kudi mai yawan gaske.

Truecaller/manhajar tantance bayanan mai waya na gaskiya: Su wane ne ke bayan wannan makarkashiyar? 

DUBAWA ta yi amfani da manhajar da ake kira Truecaller, wanda ke taimakawa masu amfani da shi wajen gano bayanan wanda ke kira na zahiri.

Da na sanya wadansu daga cikin lambobin mutanen da suka kira ni a cikin manhajar, wasu daga cikin sunayen da suka bayyana sun hada da: Momin, Ope Malas, Kawu Umar Auta, Mr P, Mr P Zoom, P, Amir K Mata, Mr P Okoye, Mr P Okoyi, Xpark Nigeria. 

Daga binciken da na yi wadannan sunayen ba su ne sunaye na zahiri na wadanda ke amfani da wadannan lambobin wayar ba.

Masu aiki da Mr Okoye sun mayar da martani

Da DUBAWA ta tuntubi wadanda ke aiki da Mr Okoye ta wayar tarhon da ke dauke da lambobin da suka sanya a shafinsu, wani daga cikin mambobin ya ce tauraron ya yi magana a kan masu damfarar sau da yawa.

Ma’aikacin wanda ya ki bayar da izinin amfani da sunansa ya ce “Mr Okoye ya yi magana da mabiyansa a soshiyal mediya, inda ya gaya musu cewa shi ya daina kira ta waya kuma a ko da yaushe yana cigaba da wannan gargadin, amma duk da haka mutane suna fadawa tarkon ‘yan damfarar duk da yawan gargadin da ya ke yi.”

Yawancin wadanda abun ya shafa wandanda kuma suka zanta da DUBAWA sun yi kira ga Facebook da ya cire shafukan wadannnan ‘yan damfarar inda kuma suke kira ga jami’an tsaro da su ma su tabbatar an kama su sun fuskanci shari’a, dan a kamanta adalci.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button