|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X said ya bayyana cewa ‘yan Najeriya ke biyan mafi karancin haraji a duniya.

Hukunci: Karya ce. Yayin da ake kallon Najeriya a matsayin guda daga cikin kasashe da ke samun kudade kadan daga haraji, wannan baya nufin al’ummar kasar suna biyan mafi kankanta na haraji.
Hamshakin dan kasuwar nan mai taimakon al’umma Bill Gates kuma shugaban Gidauniyar Bill and Melinda Gates, a baya-bayan nan ya ziyarci Najeriya inda yayi magana (speak) a shirin samar da abinci mai gina jiki na Nutrivision 2024, shirin tattaunawa da matasa na Afurka kan samar da abinci mai gina jiki, a wajen taron Mista Gates yace haraji da ake karba a Najeriya “Bashi da yawa” wannan kuma zai iya zama kalubale wajen daukar nauyin wasu muhimman ayyuka.
”Tsawon lokaci akwai tsare-tsare na Najeriya, ta dauki nauyin ayyukan gwamnati fiye da abin da take yi a yau, hakikanin harajin da take karba a zahiri yayi kadan,”a cewar Gates.
Bayanan nasa sun jawo martani da dama daga ‘yan Najeriya wasu suna shawarta da ya ja bakinsa yayi shiru kan batun na karbar haraji da ke zama kadan, inda suke kafa hujja da yadda jami’an gwamnati ke wawashe dukiyar al’umma a Najeriya, wasu kuma sun amince da bayanan dan kasuwar.
Wani daga cikin masu goyon bayan hamshakin mai kudin da ke amfani da shafin X user, @AdloveGlobal inda yayi da’awar cewa ‘yan Najeriya na biyan kudin haraji mafi kankanta a duniya.
“ ‘Yan Najeriya na biyan mafi kankantar haraji a fadin duniya, wannan mai amfani da shafin na Twitter na martani ne a dangane da tsokaci da Mista Gates yayi kamar yadda gidan talabijin na Channels ya wallafa.”
Ana dai yawan cece-ku-ce a dangane da Mista Gates a Najeriya inda ake zarge-zarge da dama kan shigarsa harkoki da suka shafi tattalin arzikin kasashe na Afurka.
Duba da yadda wannan da’awa ke daukar hankali da ma irin tasirin da za ta iya yi, jaridar DUBAWA ta yanke shawarar zurfafa bincike don tabbatar da sahihancin da’awar.
Bayani a dangane da haraji a Najeriya
A kwai banbance-banbance a game da haraji ga misali wanda ake dauka daga kudaden da ke shigarwa mutum , da haraji da ake sanyawa kayan amfanin yau da kullum (consumption tax) da haraji da ake sawa idan mutum ya samu kudade da sauransu. Domin kara fahimta an yi bayani dalla-dalla kan rabe-raben harajin kamar yadda za a gani a kasa:
Haraji daga kudaden da ke shigar wa daidaikun mutane
Action Aid ta bayyana haraji kan daidakun mutane na (PIT) a matsayin kudade da ake cira kai tsaye daga kudaden mutane kamar albashinsu da kudaden da ake ba wa daraktoci da kudaden da ake samu na riba da kudaden da aka samu bayan amfani da abin mutum da kudaden da ake samu daga kudin haya.
Kamfanin kwararru na Lawpadi yayi bayani cewa kudin haraji da ake biya bayan shigar kudade ga mutum ya danganta da adadin “kudaden shigar da harajin ya hau kansu” na (daidaikun mutane ne ko na kasuwanci ko al’umma ko iyalai) za su biya.
Bayanin ya kara da cewa kudaden da ake cire masu haraji, sune ‘wasu ko duka kudade da aka shigar idan aka kwashe kudaden kashe yayin gudanar da wasu aikace-aikace da aka amince.
Kudaden da ake cirewa daidaikun mutane ana yi ne ta hanya biyu: Kudi na shigar maka ka biya (PAYE) da kudin da kake kiyasi ka biya. PAYE shine harajin da ake daukarwa ma’aikaci daga albashinsa dayan kuwa masu zaman kansu ne da kansu suke biyan harajinsu.
Kudaden haraji da ake daukarwa mutane gwamnatin tarayya ce da hukumar tattara haraji na jiha ke yi
Har ila yau Hukumar karbar haraji ta kasa Federal Inland Revenue Service kan karbi haraji daga mazauna birnin tarayya Abuja da ma’aikata da ke yawan tafiye-tafiye kamar ma’aikatan ma’aikatar harkokin kasashen waje da ‘yan Najeriya wadanda ke zaune a ketare, amma suna samun kudadensu a Najeriya da sauransu.
Ga irin kudaden haraji da ake yankewa ma’aikaci (PAYE) a Najeriya mataki-mataki:
- Farko ₦300,000 – 7%
- Nagaba ₦300, 000 — 11%
- Nagaba ₦500, 000 — 15%
- Nagaba ₦500, 000 — 19%
- Nagaba ₦1,600,000 — 21%
- Sama da ₦3,200,000 — 24%
A wasu lokutan kuma ma’aikata da ke da kudin shiga (income) ₦30,000 ko (₦ 70,000 daga 1 ga Mayu 2024) ko kasa da haka, ba a bukatar su tattara bayanan harajin nasu.
Kamar yadda aka tattara bayanan tattalin arziki, ya nuna ba kudaden haraji na Najeriya ba ne mafi kankanta idan aka kwatanta da wasu kasashe. Ga misali Kuwait, da United Arab Emirate, da Oman basa dora haraji ga ma’aikatansu, haka kuma kasashe kamar Saudi Arabia, da Bahamas basa dora haraji ga kudaden da ke shigarwa daidaikun mutane, duk da haka akwai wasu daidaiku da ba haka abin yake ba kamar anan (here da here)
Idan aka kwatanta da Najeriya da harajin kan kai kaso 24% mafi kololuwa, akwai kuma wasu kasashe da ke da harajin kasa da haka kamar Romania, wacce ke da harajin da ake sawa al’umma 10%.
Kudin haraji a Belarus ya kai kaso 13%, akwai banbance-banbance kamar anan here. A kasar Hungary ana sanya kaso 15% cikin dari ga harajin daidaikun mutane,
A kwai kasashe da dama da harajin da suke sanyawa (PIT) yafi na “yan Najeriya, Ana iya fadin cewa harajin da ake sanyawa na PIT a Najeriya yana cikin kanana a duniya amma ba a ce shine mafi kankanta ba.
Harajin Amfani da Kayayyaki
Wannan (This) na nufin harajin da ake caja ko ake cirewa idan mutum ya sayi wani abu wanda ya hadar da harajin siyarwa da amfani da harajin kayayyaki na VATs.
Harajin kayayyaki na Value-added tax ana karbarsa ne daga kayayyaki da ayyuka wanda ake dauka a matakai daki-daki har zuwa ga mai bukata tun daga kamfanin da ke samar da kayayyakin da dillali da mai siyarwa da kuma mai siye.
Ya banbanta da harajin siyarwa sales tax, wanda shine akasari ake caja a hannun mai amfani daga mai siyarwa.
Abin lura anan shine ya banbanta daga kasa zuwa kasa kan abin da suke kira harajin wasu kan ce abin da ake caji na kaya da ayyuka da harajin abin da aka yi amfani da shi da sauransu.
Bayanai da aka samu daga PwC reveals ya nunar da cewa kasashe da dama na karbar haraji kasa da na Najeriya kamar yadda ake gani a Oman da Daular Larabawa (United Arab Emirates) suna da kaso 5 cikin dari 5% yayin da Tsibirin Jersey Island ke da kaso 5%. A kasar Timor-Leste, suna sanya harajin shigar da kayayyaki 2.5%. A Myanmar duk da cewa babu harajin na VAT akwai wani haraji da ba na kai tsaye ba da ake kira harajin kasuwanci (commercial tax) baki daya ana karbar kaso 5%.
Harajin Kamfani
Wannan haraji ne da ake karba na kamfanoni, Ana cirewa ne daga ribar (profits) kamfani. Investopedia ta yi bayani (explains) da cewa kudade ne “ kudin shiga daga kudaden da ake cirewa na haraji, wanda ya hadar kudaden shiga idan aka cire kudaden da aka kashe’.
Karkashin (Under) dokar harajin kamfanoni (CIT) kowane kamfani da yayi rijista karkashin dokar kamfanoni ta (CAMA) ya cancanci ya rika tattara bayanan harajinsa na shekara ba tare da la’akari da riba ko faduwa da ya samu ba a shekara.
Harajin kamfanonin CIT kaso 30% ne na abin da ke shigarwa kamfanin na riba a shekara idan kudin sama da miliyan 100 ne (Haraji kan ribar da kamfani ya samu a shekarar da ta gabata)
Harajin kamfanonin CIT kaso 20% ne na kudaden da yake samu daga miliyan 25 zuwa miliyan 100. Kamfanin da ke samun kasa da miliyan 25 baya cikin wannan kason haraji.
Sai dai kuma harajin albarkatun manfetir (PPT) ana cajinsa ne daga kudaden da ke shigarwa kamfanoni da ke hako albarkatun mai karkashin harajin kamfanoni, kamar yadda za a gani anan kasa.
- 50% ga masu aikin hako albarkatun mai da ake yarjejeniyar raba daidai wato (production sharing contracts (PSC) da kamafanin Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC).
- 65.75% ga kamfanonin da basa cikin PSC wannan kuwa ya hadar da masu yin hadaka ta (JVs), a shekaru biyar na farko da kamfanin bai iya kammala biyan kudaden da yake kashewa ba a kokari na samo albarkatun.
- 85% ga wadanda ba sa a tsarin (PSC operations) bayan shekaru biyar..
- 30% daga ribar masu hako albarkatun iskar gas
A wasu kasashe na duniya harajin na CIT yana kasa da na Najeriya kamar a Daular Larabawa UAE inda ake samya harajin kaso 9% na kudaden shiga sama da AED 375,000; da kaso 0% ga kudaden da za a fitarwa haraji kasa da AED 375,000 akwai kuma “wani harajin (da ba a fayyace ba) na manyan kamfanoni da suka cika wasu sharuda karkashin tsarin (Pillar Two) na hadakar ci gaban tattalin arziki ta OECD”.
A kasar Amurka kudaden haraji ga kamfanonin cikin gida an sanya masu kaso 21%, wanda ya fara aiki tun daga Disamba, 2017.
Harajin na CIT a Poland da Mauritius sun kasance 19% da 15% ko da yake akwai wasu da aka ware kamar nan (here da here)
Duk da cewa akwai cece-kuce a game da tsarin biyan harajin a Najeriya a wani rahoto da aka fitar (issued) a watan Yuli 2024, ya nunar da cewa kaso 89% na kamfanoni marasa rijista suna biyan wani nau’i na haraji ga kananan hukumominsu da wasu hukumomi.
“Idan aka hada, baki daya kasuwanni da ba sa tsarin gwamnati su ke ba da rabi kaso na abin da kasa ke samarwa na GDP wannan ya nunar a harajin da suke fitarwa mai yawa (72.3%) wanda a kowane wata suke ba da sama da N1,000,000 ,” kamar yadda rahoton na Monie Point ya nunar a wani sashe.
A watan Mayu,2024 Gwamnatin Tarayya ta nunar da cewa tana aiki ta yadda za ta samar da saukin haraji da kaso 95% ga fannoni da basa tsarin hukuma (informal).
Karshe
Yayin da kalaman Mr. Gates kan tsarin karbar haraji a Najeriya zai iya zama gaskiya musamman idan aka yi la’akari da abin da kasar kan samar da abin da ke shigarwa kasar na haraji (tax-to-GDP ratio,) Da’awar mai amfani da shafin na X cewa ‘yan Najeriya sune mafi kankanta wajen biyan haraji a duniya wannan kalaman ba daidai ba ne yaudara ce.




