Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wasu saƙonni da ke yawo a dandalin sada zumunta suna iƙirarin cewa an kara kudin yin rajistar BVN a banki zuwa ₦80,000, yin NIN ya koma ₦30,000, sai kuma dawo da layin waya da ya ɓata wato “Welcome Back” zuwa ₦50,000.

Hukunci: Dukkanin iƙirarin da ke cikin saƙon da ke yawo ba gaskiya ne ba. babu wani tabbaci daga hukumomi ko kamfanoni cewa an yi wannan kari.
Cikakken Bayani
A watannin da suka gabata ne gwamantin Najeriya ta amince kamfanonin sadarwa su yi karin kudin sadarwa da kashi 50 ga abokan huldarsu a Najeriya, to sai dai a ‘yan kwanakin nan wani saƙon da ke ƙunshe da da’awa uku ya fara yawo sosai a dandalin WhatsApp da Facebook.
Saƙon ya bayyana cewa an kara kudin wasu muhimman ayyukan gwamnati da sadarwa da suka hada da BVN da NIN da kuma welcome back.
Saƙon kamar yadda wani shafi na ALIB Hausa ya wallafa a Facebook na cewa:
“Yanzu idan zaka yi BVN a banki, sai ka biya ₦80,000.
Idan zaka yi NIN sai ka biya ₦30,000.
Idan ka ɓatar da layin wayarka, sai ka biya ₦50,000 domin welcome back.”
Ganin cewa iƙirarin zai iya jawo ce-ce-ku-ce da damuwa, musamman a tsakanin matasa da masu kananan sana’o’i da ke buƙatar amfani da wayar hannu da asusun banki kullum, DUBAWA ta yi bincike domin tabbatar da sahihancin labarin.
Tantancewa:
Da’awa 1: An kara kudin BVN zuwa ₦80,000
Binciken da DUBAWA ta gudanar ya nuna cewa har yanzu yin rajistar BVN yana nan kyauta ga masu buƙata ‘yan Najeriya, kuma babu wata sanarwa daga babban bankin kasar CBN da bankunan ƙasa da suka tabbatar da cewa an yi karin kudin.
Amma ga ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje, akwai buƙatar biyan $50 (kimanin ₦80,000) domin yin Non-Resident Bank Verification Number (NRBVN).
Wannan tsarin na musamman ne ga masu asusu daga ƙetare, kamar yadda CBN ya sanar a watan Mayun 2025.
Da’awa 2: Za a rika biyan ₦30,000 a matsayin kudin rajistar NIN
Shafin hukumar NIMC ya bayyana cewa yin rijistar NIN na farko da samun slip ɗin farko yana nan kyauta ga ‘yan Nijeriya.
Sai dai DUBAWA ta gano cewa hukumar yin rajistar katin zama dan kasa ta kara kudin yin wasu ayyuka kamar gyara suna, gyara ranar haihuwa ko sake jinsi, wadanda farashinsu ya karu matuka.
Babu wata sanarwa daga NIMC da ta ce ana biyan ₦30,000 don yin NIN daga farko.
Da’awa 3: SIM Welcome Back – ₦50,000
Kamfanonin sadarwa kamar MTN, Airtel, GLO da 9Mobile ba su fitar da wata sanarwa da ke nuna cewa dawo da SIM (welcome back) yana bukatar ₦50,000.
DUBAWA ta tattauna da wani dillalin layukan MTN a jihar Sokoto, Usamatu Hussaini, wanda ya ce:
“Yin welcome back yawanci bai fi ₦1,500 zuwa ₦3,000 ba, sai dai idan mutum ya rasa katin rijista ko kuma yana son yin sa da gaggawa.”
Bugu da ƙari, hukumar NCC mai kula da sadarwa ta Najeriya ba ta fitar da wani ƙa’ida da ke nuna sabon farashin nan ba.
A Karshe
Bayanin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kara kudin yin rajistar BVN da yin NIN yda kuma dawo da layin waya da ya ɓata wato “Welcome Backd” bai da tushe ko makama daga hukumomin da abin ya shafa.