African LanguagesFeaturedHausa

Al’adu da Zamantakewa: Marinar kofar mata guda cikin wuraren tarihi muhammai a Kano

Getting your Trinity Audio player ready...

Marinar Kofar Mata wuri mai dadadden tarihi da aka kafa ta a shekarar 1498 kamar yadda littafan tarihi da makaloli na masana suka nunar, an kafa ta a cikin birnin Kano ma’ana a cikin badala ko ganuwar Kano, tana nan daf da bakin Kofar Mata daya daga cikin kofofi na birnin Kano masu dinbin tarihi, tana nan gabas da babban masallacin Juma’a na birnin na Kano. Littafan tarihin ma sun nunar da cewa ita wannan MarinarKofar Mata da take da shekaru sama da 500 an kafa ta tun kafin ma a gina ganuwar da ta zagaye birnin na Kano.

Da dama shugabanni a duniya sun ba da tarhin cewa sun san da zaman wannan marina in da ke da tarin rijiyoyi wadanda aka haka, ake amfani da su wajen sauya launin tufafi daga fari zuwa wata kala musamman shudi wanda ke zuwa a kala-kala. Da fari Marinar Kofar Mata wuri ne da yake a bude babu wata Katanga da ta zagaye wajen, ana ganin masu aikin rinin kowa ya sa rijiyarsa gaba yana aiki, kafin daga bisani zamani da ke zuwa da shugabanni kala-kala ya kawo sauyi da aka kewaye wannan wuri.

Wanda ya kafa wannan marina shine Malam Muhammadu Dabosa kamar yadda tarihi ya nunar, ya assasa masana’antar da ta girmi zuwan Turawan mulkin mallaka, masana’antar da har kawo yanzu ke ci gaba da rike kambunta na aiwatar da ayyukan sarrafa launin tufafi a hanyoyi na gargajiya.

Irin wannan marina a baya akwai su sosai a garin Zariya na jihar Kaduna amma har kawo yanzu wacce ke zama dadaddiya da kuma ke aiki ita ce ta Kofar Mata a Kano, Za ka ga matasa da tsofaffi na aiki a wannan marina da wasu kan kira Karofin Kofar Mata, wasu na aikin rini wasu na aiki bugu duka cikin marinar.

Al'adu da Zamantakewa: Marinar kofar mata guda cikin wuraren tarihi muhammai a Kano

Wani dattijo na shirin maida farin tufafi zuwa launin shudi: Wanda ya dauki hoto Yusuf Bala: DUBAWA 2025

Haruna Baffa Magatakarda na kungiyar marina a jihar Kano yayi mana karin haske kan wannan marina mai dadadden tarihi.

“Marinar Kofar Mata waje ne da ake sarrafa hajja, wato fari ya zuwa wata kala wato shudi wanda tun a lokacin Larabawa suke kawo kayansu da suke sakawa a can Magrib, su kawo mana nan Kofar Mata a zo a rina masu su dauka su koma can kasashensu na Gabas sama da shekaru 526, wadannan ramukan ma duk basu bane a lokacin ana amfani ne da manyan tukwane na kasa da kwarya a cikinsu ne ake hada wannan ruwan sinadaran da ake wannan sana’a. 

A cikin wannan tukunya a kan sanya toka da katsi  da itacen baba da ruwa, saboda kasancewar wurin hadawar ko a tukunyar ba ta da zurfi sai ruwan sinadaran ya sane ko ya salance cikin kankanin lokaci, a lokacin da Larabawan suka zo ne suka ba da shawarar cewa idan ana so ruwan ya dade sai an yi rami mai zurfi a zuba sinadaran da ruwan da haka ne zai dade. A lokacin ne aka fara yin rami mai zurfin mita biyu zuwa mita uku anan ne aka ga ruwan sinadarin na daukar tsawon wata uku har zuwa wata shida daga nan sai aka ce a kara zurfin da mita uku sai ya ke kaiwa wata takwas, wannan ne ke sawa sai ruwan sinadarin yake kaiwa shekara daya ba tare da ya salance ba.” a cewar Baffa.

Magatarkadan Baffa yace marinar na da rijiyoyi 144 wanda yanzu haka akwai guda 50 da suke aiki, suna kuma da rijiyoyin masu zurfin mita uku da mita hudu da mita shida. Ya kara  da cewa nau’ikan shudin da akan samar a marinar ta Kofar Mata sun banbanta wani shudi mai haske, wani shudi mai duhu da shudi mai duhu sosai (Turkudi) da ake kira Dan Kura irin sa ne ake ganin Buzaye na amfani da shi, irin wannan shunin da ake kira Dan Kura shi ne ke daukar tsawon awa shida ana tsoma shi an fitowa da shi har sai yayi bakikkirin “ko da masana’antar sarrafa tufafi ta Manchester United kaje ba za ka ga irin wannan kalar ba har sai ka dawo nan marinar Kofar Mata,” a cewar Baffa.

Al'adu da Zamantakewa: Marinar kofar mata guda cikin wuraren tarihi muhammai a Kano

Haruna Baffa Magatakarda na kungiyar Marina a jihar Kano daga hagu: Hoto: Haruna Baffa 

A cewar Haruna Baffa har kawo yanzu baki daga kasasahen ketare Turawa da Larabawa na zuwa Marinar Kofar Mata don ganin yadda wannan marina ke gudanar da ayyukanta na rinin  kaya na gargajiya ba tare da amfani da wasu sinadarai na Bature ba.

“Koda a ce ruwan sinadaran da aka hada ne ya salance ko ya sane baya iya rina kayan marini kan duba ya ga me yake bukata idan toka ce sai ya kara idan itacen baba ne yayi karanci  ya kara da sauran kayayyakin da muke amfani da su. ”

Al'adu da Zamantakewa: Marinar kofar mata guda cikin wuraren tarihi muhammai a Kano

Yadda Turawa ke shiga ana bugun kayan da aka rina a mabugar da ke cikin Marinar Kofar Mata a Kano Hotto: Haruna Baffa

A cewar Haruna Baffa shekaru 15 baya zuwa yau wannan marina ta Kofar Mata ta samu ci gaba sosai ganin yadda matasa suka rungumi wannan sana’a. Kafin wannan lokaci sana’ar ta yi baya saboda in ka zo mutum biyu ko daya za ka gani suna aiki sabanin wannan lokaci.

Al'adu da Zamantakewa: Marinar kofar mata guda cikin wuraren tarihi muhammai a Kano

Matashi da ke aikin rini a Marinar Kofar Mata. Hoto: Yusuf Bala

Kira ga gwamnati

Ganin muhimmanci da wannan sana’a ke da shi wajen samar da ayyuka ga dimbin matasa har ma da wadanda suka manyanta a cewar Haruna Baffa magatakardan kungiyar marina a Kano akwai bukatar gwamnati ta bawa fannin kulawa yadda ya kamata; “duk wanda ya bawa al’adarsa muhimmanci za ka ga ta samu ci gaba don haka nake kira ga gwamnati ta bawa wannan fanni na sana’ar hannu muhimmanci ganin yadda yake taimaka mana matasa da samun kudade abin da zai bunkasa tattalin arziki ba kawai na Kano ba har da Najeriya baki daya. Wannan sana’a iyaye da kakanni muka tashi muka ga suna yi shi yasa wajen nan har yanzu yake wanzuwa da tuni an gine shi. Ni wannan sana’a ba zan iya barinta ba duk da cewa nayi karatu duba da irin rufin asiri da nake samu a cikinta.” A cewar Baffa.

A Karshe

Akwai dai bukatar masu ruwa da tsaki a fanni na tattalin arziki su ba wa sana’oin hannu irin na rini kulawar da ta kamata ganin yadda wannan sana’a ke ci gaba da jan hankali na al’ummar kasashen duniya, abin da ke nuna cewa za ta iya zama silar samun kudaden ketare ba kawai ga daidaikun jama’a ba har ma da gwamnati abin da zai kawo bunkasar tattalin arziki ba kawai ga jihar Kano ba har ma da Najeriya baki daya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »