African LanguagesHausa

Ba gidan Wike ne ya kama da wuta ba hotunan kikirarriyar basira ne wato AI ake yadawa

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya yada labarin da ke cewa matasa sun kone gidan Nyesom Wike dake jihar Rivers.

Ba gidan Wike ne ya kama da wuta ba hotunan kikirarriyar basira ne wato AI ake yadawa

Hukunci: Karya ce! Binciken Dubawa ya gano cewa hotunan da ake yadawa fasahar AI wato kirkirarriyar basira ce

Cikakken Bayani

Rikicin siyasar jihar Rivers na kara zafafa, sakamakon ƙoƙarin faɗaɗa ikon da Gwamna Siminalayi Fubara ya yi a jihar, ta hanyar shiga takun saka da tsohon ubangidansa kuma ministan Abuja Nyesom Wike.

Rikcin nasu ya kai ga tarwatsa kan majalisar dokokin jihar tsakanin magoya bayansu. inda har aka samu kakakin majalisa biyu kafin daga baya shugaban kasa ya ayyana dokar ta baci a jihar da kuma nada gwamnan rikon kwarya.

Ana cikin haka ne wani labari da wani mai amfani da Facebook ya wallafa ya karade shafukan sada zumunta.

Labarin na cewa fusatattun matasa a jihar Ribas sun ƙone gidan Ministan Abuja Wike yayin da Wike ya kama hanyar zuwa mahaifar sa jihar Ribas.

Ba gidan Wike ne ya kama da wuta ba hotunan kikirarriyar basira ne wato AI ake yadawa

Hoton da aka zakulo a Facebook

Wannan labarin da aka sake wallafawa ya dauki hankalin masu amfani da shafin Facebook, zuwa ranar 20 ga watan Maris na 2025 sama da mutane 640 ne suka yi sharhi (comments) a kan labarin yayin da mutane 160 suka yada shi (share).

Dubawa ta yi bincike domin tabbatar da sahihancin labarin, ganin cewa labarin na iya haddasa hargitsi da tashin hankali.

Tantancewa

Mun yi binciken hotunan da ake yadawa cewa na gidan ministan Abuja ne dake jihar Rivers, inda muka gano cewa an hada su ne ta hanyar amfani da kirkirarriyar basira.

Ba gidan Wike ne ya kama da wuta ba hotunan kikirarriyar basira ne wato AI ake yadawa
Ba gidan Wike ne ya kama da wuta ba hotunan kikirarriyar basira ne wato AI ake yadawa

Sakamakon binciken da muka yi da manhajar sight engine

Binciken tsanaki da muka yi mun gano cewa mutanen da ke cikin wadannan hotunan ba su yi kama da mutanen gaskiya ba, domin irin wannan wutar da aka nuna cewa ta kama babban gida zai yi wuya mutane su kusance a yadda aka nuna a hotunan.

Hakama Dubawa ta ga wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta fitar, inda ta yi watsi da rahotannin da ke cewa wasu ‘yan daba ne sun kai hari a gidan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike tare da kone shi.

Jami’ar hulda da jama’a ta ‘yan sandan, Sufeto Grace Iringe-Koko, ta bayyana labarin a matsayin karya da yaudara da kuma yunƙurin tada tarzoma da kuma sanya tsoro ga al’ummar jihar..

A Karshe

Karya ce! Binciken Dubawa ya gano cewa hotunan da ake yadawa fasahar AI wato kirkirarriyar basira ce aka hada su kuma rundunar ‘yan sandan Ribas ta karyata labarin cinna wa gidan Wike wuta.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »