African LanguagesHausa

Ba masu garkuwa da mutane ba ne a bidiyon nan

Zargi: Wani bidiyo a TikTok wanda aka yi ta yadawa a kafofin sada zumunta na soshiyal mediya na zargin wai wasu ‘yan sandan Ghana sun anshe wasu makudan kudade daga wasu masu satar mutane a Najeriya da ke kokarin shigar da shi kasar ta barauniyar hanya

Ba masu garkuwa da mutane ba ne a bidiyon nan

DUBAWA ta gano cewa an dauki bidiyon nan ne a Ghana a titin da ke tsakanin garuruwar Techiman da Kumasi, lokacin da wata motar da ke dauki da kudin banki ta yi hatsari da tankar man fetur. Wannan bidiyon ba ta da wata alaka da masu garkuwa da mutane daga Najeriya. Zargin ba gaskiya ba ne

Cikakken bayani

A Najeriya kungiyoyin ‘yan ta’adda wadanda ake kira bandits su kan saci mutane su yi garkuwa da su dan samun kudin fansa. Neman kudin fansa yanzu ya zama ruwan dare kuma duk da cewa haramun ne abin ya zama wata hanyar samun kudi wa ‘yan ta’adda a duk fadin Najeriya.

Wannan shi ya wasu masu amfani da shafukan soshiyal mediya su ma su ke amfani da damar da suka samu suna yada wani bidiyo a TikTok da zargin cewa ‘yan sandan Ghana sun kama wadansu ‘yan Najeriya masu garkuwa da mutane suna kokarin shigar da kudin fansa Ghana. 

An yi wa bidiyon taken, “‘Yan sandan Ghana sun kama wasu ‘yan bindigan Najeriya suna kokarin fitar da biliyoyin nera daga kasar.”

Bayan tantance bidiyon da kyau, DUBAWA ta gano cewa akwai wadansu manyan robobin da ke dauke da wasu abubuwan da suka yi kama da takardun kudi, duk an baza a kan hanya. Ana kuma iya ganin wata mota mai ruwan bula da wata farar tankar mai da kuma wadansu jami’an tsaro masu dauke da makamai.

Da DUBAWA ta karanta irin tsokacin da aka yi a karkashin bidiyon, da gano cewa akwai rudani tsakanin masu amfani da soshiyal mediyar. Yayin da wasu su ka bayar da gaskiyar cewa bidiyon na da dangantaka da Najeriya wasu suna shakkun inda aka samo bidiyon.

Domin kaucewa irin wannan rudanin ne DUBAWA ta ke so ta gano gaskiyar lamarin.

Tantancewa

DUBAWA ta yi nazarin hotunan bidiyon dalla-dalla cikin manhajar tantance bidiyo na InVid inda sakamakon ya nuna cewa an fara wallafa bidiyon a wata tasha mai suna Chasm TV a YouTube a shekarar 2019. Sadda aka fara wallafa bidiyon an yi mi shi taken “Kudi ko’ina bayan da motar kudin bankin Ghana ta yi karo da tankar mai.”

Da DUBAWA ta kalli bidiyon mai tsawon dakiku 29 ta gano cewa iri daya ne da wanda ake yadawa a sunan wai an kwace kudi daga hannun masu satar mutane a Najeriya.

Bincike ta yin amfani da mahimman kalmomi irinsu “Motar kudin Ghana ta yi karo da tanka” sun kai DUBAWA zuwa wani rahoton da wata kafar yada labaran Ghana ta wallafa dangane da hatsarin. Kafofin yada labarai irin su Joy Oline, Pulse Ghana da Ma wasu a cikkin Najeriya sun yi labarin hatsarin.

Wani rahoton da aka yi wa taken “Kudi ko’ina motar kudin bankin Ghana ta yi karo da tankar mai, an tabbatar da mutuwar mutun gida (bidiyo) ya bayyana cewa bidiyon ya nuna hatsarin motar wanda ya afku a titin da ke tsakanin Techiman da Kumasi a Ghana.

A cewar rahoton, hatsarin wanda ya afku ranar 4 ga watan Satumbar 2019 ya yi sanadiyyar mutun guda kuma da dama sun jikkata.

Rahoton ya kara da cewa: “Wata hadakar Sojoji, ‘Yan sanda da jami’an kwana-kwana, da jami’an kula da shige da ficci da ma ofishin bincike na kasa sun killace wajen da hatsarin ya afku sun kwashe kudaden da suka zube sun sanya su cikin motocin tsaro daban-daban. Za’a ajiye duk kudaden da aka kwashe daga wurin hatsarin a daya daga cikin dakunan hedikwatar ‘yan sanda a karkashin kulawar sojoji, ‘yan sanda da jami’an tsaron babban bankin Ghana.”

A Karshe

Bidiyon TikTok din da ke ikirarin wai ‘yan sandan Ghana sun anshe kudade daga wajen wasu masu satar mutane a Najeriya ba gaskiya ba ne. DUBAWA ta gano cewa an dauki bidiyon ne asali a shekarar 2019 a Ghana lokacin da Motar Babban Bankin kasar ta yi karo da wata tankar mai tsakanin Techiman da Kumasi. Bidiyon ba shi da wata alaka da masu satar mutane a Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »