African LanguagesHausa

Ba mu ga inda aka bayyana taka mai-mai cewa Burtaniya ta tasa keyar Emdee Tiamiyu ba, dan Najeriyar da ake zargi ya tsere da makudan kudaden da da kasar ya ba shi

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: An maido da dan gwagwarmayar Najeriya Emdee Tiamiyu, wanda ya tsere Ingila neman mafaka amma bayan da gwamnatin ƙasar ta bashi maƙudan kuɗaɗe don kula da kansa sai aka gano cewa tura kudaden garinsu a Najeriya ya ke yi, inda ake masa gini…

Ba mu ga inda aka bayyana taka mai-mai cewa Burtaniya ta tasa keyar Emdee Tiamiyu ba, dan Najeriyar da ake zargi ya tsere da makudan kudaden da da kasar ya ba shi

Hukunci: Karya ce! DUBAWA ta gudanar da bincike ta gano cewa da’awar karya ne ba’a maido Emdee Tiamiyu gida Najeriya ba.

Cikkaken Bayani

Wani shahararren  dan YouTube Emdee Tiamiyu wanda ya dauki hankalin jama’a sadda ya bayyana wa BBC cewar yawancin ‘yan Najeriyar da ke samun makaranta a Ingila su tafi da iyalinsu baki daya yaudarar mutane suke yi su ce za su karatu ne kadai alhali kuma ba su da niyyar dawowa. Da yawa kuma na hasashen cewa wannan ne ya yi sanadin da aka gindaya sabbin  sharuɗa aka kuma tsaurara dokokin da suka shafi ‘yan Najeriya masu niyar zuwa kasan waje karatu ko kuma tarewa. Hakan ya sa yan Najeriya suka tsani Emdee Tiamiyu.

Ana nan sai wani dan Laberiya a kafar sada zumunta ta TikTok mai suna  Kinzhal dan Monrovia ya ce ‘yan sandan Ingilar sun kama shahararren dan YouTube din wato Emdee Tiamiyu. 

Kinzhal ya ce sun kama shi da zargin yaudarar da yayi wa gwamnatin Birtaniya na fam (£) dubu 160, a matsayin irin bashin da ake baiwa masu neman mafaka ta siyasa saboda bakin jinin da ya samu daga ‘yan Najeriya da ma halin fargabar da ya shiga na cewa harzuka ‘yan Najeriyar da ya yi da bayanin da ya bayar zai sa su yi masa lahani. To sai dai daga baya an yi zargin cewa ya tura kudin gida an yi mi shi gina abun da ya sabawa dokokin Burtaniya dangane da bashin wadanda suka tanadi cewa idan har za ka yi amfani da kudin dole ne ka yi amfani da su duka  a kasar da ka ke samun mafakar siyasar. Ba’a yarda ka fitar da kudin ba.

Bayan da labarin ya bulla a shafukan sadarwa, an yi ta cece-kuce dangane da batun inda aka rika bayar da ra’ayoyi mabanbanta. Da yawa sun yarda da labarin a matsayin gaskiya inda suka rika cewa “Yau Allah ya kama shi, ashe da ma shi ma yana yin abubuwan da suka sabawa doka amma kuma ya je ya na kokarin hana ruwa gudu ma wasu?” Akwai kuma wadanda ba su yarda da labarin ba su kuma suke cewa babu yadda za’a yi Burtaniya ta dauki fam 160, 000 ta ba wani mai neman mafakar siyasa wai dan ya kula da kansa, kamar Mayor of Enugu @mayorofenugu wanda ya sa ayar tambaya kan sahihancin labarin ya ce “anya? Kun tabbata? Na ji an ce jita-jita ce kawai ake ta yadawa na tsawon watanni yanzu. Har wa yau wasu kuma suka ce bakin ciki ne kawai mutane suke masa tunda ya sa wa garinsu kasa, irin su Omotayo Olokede wanda ya ce “yaya za’a yi kuma labarin da ba shi da tushe.”

Tantancewa 

Mun fara da binciken mahimman kalmomi inda muka gano cewa kafofin yada labaran Najeriya da ma masu bayanai a tsakokinsu cikin shafukan sada zumunta sun dauki labarin sosai kamar Leadership, News Central TV da Times Now  da dai sauransu.

Bincike ya nuna mana da cewar Karya ne gwamnatin Birtaniya ba ta ba Emdee Tiamiyu fam £160, 000 ba saboda babu yadda za’a yi ta bada tallafi na fam £160, 000 dan mabukatar mafaka su na dai bada fam £49.18 so daya a sati ga mabukata mafaka. Mun gano a shafin yanar gizo na  gwamnati da cewar ana ba da wannan kudin ga mubukata mafaka in da su da nasu suke amfana da wannan tallafin. 

Ba mu ga inda aka bayyana taka mai-mai cewa Burtaniya ta tasa keyar Emdee Tiamiyu ba, dan Najeriyar da ake zargi ya tsere da makudan kudaden da da kasar ya ba shi

Da wannan bayanan, babu yadda mabukacin mafaka ko a makonnai 52 ba zai kai fam £160, 000 in aka hada gaba daya tallafin zai zama fam £2557.36 a shekara.

DUBAWA ta kara tantance hoton da aka turo a yanar gizo da kazafin shine gidan da yake ginawa kenan a jihar Ogun da manharajar Google Reverse Image sai ta gano cewar karya ne, hatta wannan ginin ma ba a kasar Najeriya take ba, a kasar Thailand wadda aka daura a google ran 20 ga watar Febwari 2018. 

Ba mu ga inda aka bayyana taka mai-mai cewa Burtaniya ta tasa keyar Emdee Tiamiyu ba, dan Najeriyar da ake zargi ya tsere da makudan kudaden da da kasar ya ba shi

Google reverse search ya nuna mana cewa a kasar Thailand ake wannan ginin ba Najeriya ba

DUBAWA ta kara tantancewa domin kara zakulo gaskiyan lamarin akan cewar an maido shi gida Najeriya baya an kama a Ingila in da ya boye sai DUBAWA ta gane cewar karya ne babu wani labari makamancin haka. Dan a kaffar sada zumunta ta Facebook mai suna A Yau mu ka ga labari. Bacin haka, ita kanta a shafinta na turanci ta yi bayani kan yadda wani dan Laberiya mai amfani da TikTok ya yaudara da jama’a kan batun kama mai amfani da YouTube din a nan, kuma mun ma tsakuri labarin mun yi amfani da shi cikin wannan labarin

Mun yi amfani da muhimman kalamai muka duba kafafan yada labarai na kasa da na waje duk da hakan ba mu ga wani rahoto akan wan lamarin ba, sai mu ka zo ga haƙiƙancewa labarin karya ne. 

Muka kara duba kaffofin sada zumunta daban daban duk da haka, babu komi sai dai a X in da ake ta tozarta shi wasu ma farin ciki suke akan lamarin saboda suna ganin ya cutar da ya Najeriya da abinda ya yi dan haka gani su hukunci maido shi gida dai dai ne wasu masu ma dai basu yadda da labarin cewar an maido shi ba suna gani cecekuce ne kawai na kafar yada zumunta.

DUBAWA ta yi wannan bincike ne mai zurfi dan fahimtar da al’umma baki daya akan al’amuran yau da kullum da kuma wayar da al’umma akan yaudarar yanar gizo da ayi taka tsantsa da yaɗa labarin da ba shi.

A Karshe

DUBAWA ta yi zurfin bincike akan maido Emdee Tiamiyu gida Najeriya akan maƙudan kuɗaɗe da aka bashi don ya kula da kanshi wannan lamarin kuma ta gani ce Karya ne!

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button