African LanguagesHausa

Bago: Shin gwamna na da ikon sanya sharudan yin wa’azi a Najeriya?

Getting your Trinity Audio player ready...

A baya-bayan nan labari ya karade cikin al’umma (news circulated) cewa gwamnan jihar Niger Umar Bago, ya gabatar da tsare-tsare kan sharudan yin wa’azi a jihar.

    Gwamna Umar ya bayyana cewa wannan yunkuri ba na cusa wata da’awa bane face fitar da wasu sharuda ga malamai kan wa’azi da suke wa al’umma don gudun kada su cusa masu tsatstsauran ra’ayi a yankin.

    A shafukan sada zumunta (On social media), wasu daga cikin masu amfani da shafin sun amince da matsayar gwamnan inda suke cewa hakan zai kawo zaman lafiya tsakanin mutane da ke da banbanci na addini, sai dai kuma wasu na da ra’ayi na daban  (others argued) wadanda ke ganin hakan zai kawo kutse na ‘yansiyasa a harkokin wa’azi.

    A wani bangare na aikin iimantarwa kan harkokin yada labarai na DUBAWA, mun duba irin karfin iko da gwamna ke da shi wajen sanya sharuda kan yadda zaa yi wa’azi na addinai.

    Me doka ke cewa? 

    Domin sanin ko matakin na Bago na kan matakin shari’a. Zai yi kyau sanin  wane abu ne gwamna ke iya yi karkashin doka da ta shafi harkoki na addini.

    Bincike dai ya tabbatar da cewa gwamna a Najeriya ba shi da dama ta yin doka kan sha’anin abin da ya shafi addini.

    Kai tsaye idan aka duba sashi na goma (Section 10) cikin kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayyana cewa babu hurumi na cewa ga addinin wata jiha a duk fadin kasar, Najeriya kasa ce da ba za a ce ga addininta ba.

    Duba da cewa Najeriya ba wanda zai ce ga addininta, don haka a bangaren na gwamna ma ba za a ce kai tsaye yana da dama ba kan kababawa al’umma wani abu da ya shafi addini, amma a harkar zamantakewa ana iya cewa zai iya duba yanayi ya ga idan ana yin wani abu da ya wuce kima da zai kaawo matsala a cikin al’umma ya taka birki. Kamar yadda sashi 11(1)) na kundin tsarin mulki ya bayyana cewa cikin jerin irin wannan dokoki wata kila ana iya samu a wata jiha don tabbatar da tsaro da samar da zaman lafiyar al’umma.

    Haka nan a sashi na 38 na kundin tsarin mulkin na Najeriya ya bayyana ba da ‘yanci na addini da fadin albarkacin baki, sannan sashi na 39 ya ba da dama ta yin wa’azi da yada manufar abin da wani yayi amanna da shi. Kai tsaye ma dai sashi  38(3) ya bayyana cewa babu wata al’umma mai bin addini ko masu bin wani tafarki da za a hana su gabatar da wa’azi a cikin al’ummarsu da ke bin wannan tafarki.

    Sai dai kuma mun lura cewa wadannan hakkoki na da iyaka, A sashi na 45 na dai wannan kundin tsarin mulki ya ba da dama ta sanya ka’ida  kan batu kuma na ba da kariya ga al’umma da mutuncinsu da lafiyarsu, irin wannan ka’ida akwai bukatar ganin ta samu goyon bayan doka. 

    Sharhi kan matsayar doka

    Binciken DUBAWA ya nunar da cewa kotu a Najeriya za ta iya haramta dakatarwar gwamnan jiha ko wata hukuma idan kotun ta gano cewa kokarin dakatarwar ba shi da wata ma’ana.

    Yayin da gwamnatin jihar Niger ke iya amfani da karfin iko na ganin ta hana yin wa’azi da ka iya harzuka al’umma ko furta kalamai na batanci, wannan karfin iko ba shi da karfi karkashin doka.

    DUBAWA ta tattauna da Abdulhameed Kamaldeen, lauya da ke zaune a Abuja inda ya bayyana cewa yin wa’azi baya bukatar samun lasisi daga gwamnatin jiha karkashin tanadin doka, duk wata da’awa da ka iya yin kutse a nan za a iya kalubalantarta a kotu. 

    Don haka duk wani yunkuri na cewa sai mutane sun nemi lasisin wa’azi ko kafin fara wa’azi sanya takunkumi ne ga hakkin da al’ummar ke da shi, ko da yake al’ummar na da ‘yanci karkashin doka wannan ‘yanci na da iyaka.

    “Har sai majalisar dokoki ta jiha ta amince da dokar ba da lasisi ga duk mai yin wa’azi, in ba haka ba duk kokari na mahukunta na kakaba masu ta hanyar fito da wani tsari wannan abu ne da za a sa idanu a kansa ko a ce takaita hakki ne da al’ummar ke da shi,” a cewar Abdulhameed 

    Wani lauyan Ibrahim Moshood, yace duk da cewa gwamnan a gwamnatance abin da yayi daidai ne, hakan ya sabawa kundin tsarin mulki idan aka kalli abin ta fuskar shari’a.

    “Gwamnati za ta iya sanya takunkumi kan abin da masu wa’azi za su ce a wajen wa’azinsu hakan na iya takaita hakkinsu,” a dan haka gwamnati na da hakki ta tabbatar da ganin cewa a yayin wa’azin babu cin mutunci ko tozartawa, wannan ma ya kamata a yi shi a bisa tsari na doka.”

    Ya kara da cewa masu yin wa’azi suna da dama su garzaya kotu duk lokacin da aka ta ke hakkinsu.

    A Karshe

    Abubuwan da DUBAWA ta gano shine duk da cewa gwamnati na da damar taka burki ga malaman da ke wa’azi da neman wuce gona da iri akwai kuma bukatar ganin gwamnati tana yin duk abin da ya dace a bisa doran doka, don kada ko da ta yi a kalubalance ta a gaban kotu. Wacce ke iya rushe matakin gwamnatin.

    Show More

    Related Articles

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    Back to top button
    Translate »