|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani bidiyo da ake yaɗawa yana nuna cewa Dakarun Sojin Nijeriya sun kama wata babbar mota tirela ɗauke da bindigogi da harsasai a kan hanyar Kaduna.

Hukunci: Ƙarya ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa bidiyon na ƙirƙirar fasahar kwamfuta (AI) ne, ba wani ainihin kama da sojoji suka yi ba.
Cikakken Bayani
Wani gajeren bidiyo ya bayyana a dandalin Facebook, ya nuna tirela cike da wasu kaya ana cewa makamai ne sojoji suka kama.
Mutumin da ke cikin bidiyon, wani soja ne a tsaye yake nuna motar tirela da makamai a ƙasa tare da gabatar da wani da ake zargin cewa an kama tare da makaman a kan hanyar Kaduna.
Bidiyon wanda wata kafa ta Wakiliya ta wallafa (an adana a nan) ya jawo tattaunawa sosai, inda sama da mutum 335,000 suka kalla, zuwa ranar Laraba 10 ga watan Disamban 2025.
Sharif Yahaya ya yi sharhi cewa “ai (rundunar soji) tana kokari wajen kama batagari” abin da ke nuna yarda da wannan bidiyon.
Yayin da Abba Muhd ya yi sharhi cewa “Wakiliya Gaskiya kuna bamu kunya wallahi, Ace dan tsabar shirme ku dinga daukar AI generated video wai kuna kafa hujja dashi”
DUBAWA ta gudanar da bincike domin tabbatar da sahihancin bidiyon saboda irin tasirin da irin wannan zargi zai iya yi wa al’umma idan ba gaskiya ne ba.
Tantancewa
DUBAWA ta saka bidiyon a cikin manhajar gano hoton da aka ƙirƙira don yaudarar mutane mai suna Undetectable AI Video Detector.
Ta yanke hukunci cewa bidiyon na fasahar AI ne gaba ɗaya
Daga bayanin manhajar, ta gano sigogin AI a cikin bidiyon, tsarin gani (visual patterns) ya dace da salon bidiyon da AI ta ƙirƙira, hakama siffar hoton (frame analysis) ta nuna ba na zahiri ba ne.
Cikakken nazari da ya tabbatar da cewa bidiyon AI ne
Mun kuma yi amfani da manhajar Hive AI Detector da ita ma ta nuna kusan dukkan bidiyon cike yake da sigogin da ke nuna aikin AI ne.
Sakamakon ya nuna cewa kashi 99.4 cikin ɗari.

Sakamakon nazarin Hive AI
DUBAWA ta duba shafukan Facebook da X da Rundunar Sojin Nijeriya ke amfani da su wajen fitar da sanarwa. Sai dai babu babu wata sanarwa ko ɗaya da ta fitar da ya nuna kan kama mota tirela a Kaduna.
Kammalawa
Ikirarin cewa Sojin Nijeriya sun kama tirela ɗauke da bindigogi da harsasai a kan hanyar Kaduna ba shi da tushe.




