African LanguagesHausa

Bidiyon da ya bayyana a shafin Facebook ya na nuna Haaland na baiwa Arteta hakuri na bogi ne

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani shafin Facebook ya wallafa bidiyon da ke zargin wai Haaland ya fito fili ya baiwa Arteta hakuri.

Bidiyon da ya bayyana a shafin Facebook ya na nuna Haaland na baiwa Arteta hakuri na bogi ne

Hukunci: Yaudara ce! Rahotanni sun bayyana mana cewa hirar da aka yi a cikin bidiyon, an yi shi ne bayan wasan da aka yi tsakanin Manchester City da Aston Villa ranar Asabar 21 ga watan Disamban 2024 inda Haaland ke bayani kan damammakin da ya rasa sadda suka kara da Aston Villa.

Cikakken bayani

Bayan karawar Manchester City da abokiyar hamayyarta Arsenal a watan Satumban 2024, inda kungiyoyin biyu suka yi kunnen doki, dan wasan gaban Man City, Erling Haaland ya tinkari kocin bakin Mikel Arteta ya yi masa rashin kunya ya na ce masa ya yi kokari ya daina “girman kai”.

A matsayin martani ga wannan gaban da ke tsakanin mutanen biyu, wani shafin Facebook mai suna Arsenal Fantastic News, ranar Lahadi 29 ga watan Disemban 2024 ya wallafa wani bidiyon da ke zargin wai Haaland ya nemi gafara wajen Arteta bayan afkuwar lamarin a watan Satumba.

“Yi hakuri, idan ka yarda, ka yi hakuri. Zan daina girman kai daga yanzu. Ina neman gafara wajen Mikel Arteta. Tun sadda na ce mi shi ya daina girman kai abin ya kasance kamar an tsine mana. Ka gafarta mana ko tsinuwar za ta rabu da mu. Za’a sake yi mun rashin mutunci a Instagram kuma yau da daddare,” aka yi zargin cewa an jiyo dan wasan gaban Man City din ya na bayyanawa.

“Da gaske har ina so in yi kuka Arteta, na roke ka dan uwa idan ba haka ba zamu cigaba da fama. Ban san ko za mu sake nasara a wata wasar ba. Na yi alkawari zan daina girman kai,” Haaland ya jaddada.

Daga ranar litinin 30 ga watan Disemba mutane sama da dubu 12 sun latsa alamar like, an yi shari sama da 1,200 sa’anan an sake rabwa sau 1,700.

DUBAWA ta sake gano wasu labarai makamantan wannan a shafukan Facebook  (a nan, nan, nan, da nan), da kuma Instagram (nan, nan, nan, da nan), da kuma YouTube.

Ganin yadda wannan bayanin na dan wasan gaban Man Cityn ya shuhura a shafukan sada zumanta sakamakon rashin jituwar manyan jiga-jigan kwallon kafar biyu, DUBAWA ta ga kamar ya cancanta da binciki sahihancin wannan batun.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da gudanar da binciken hoton bidiyon ta yin amfani da manhajar  Google Reverse Image kan wasu daga cikin hotunan da ta dauka. Sakamakon ya nuna cewa hoton na da alaka da bidiyon da aka dauka bayan da Man City ta lallasa Aston Villa ranar 21 ga watan Disemban 2024.

Da muka cigaba da binciken, DUBAWA ta sake ganin wani bidiyon makamancin wannan a shafin Sports Tab ta YouTube amma sautin maganar da ya ke yi ya banbanta da abin da wanda ya wallafa hoton ke cewa. A cikin bidiyon Haaland na bayani ne kan yadda kungiyarsa ta fiskanci koma baya da ma yadda ya rika kura-kurai a wasannin da suka yi a karshen shekarar da ta gabata.

“Ban yi wasan yadda ya kamata ba kuma ban bai wa Man City irin damammakin da ya kamata a ce na ba ta ba. Ya kamata in inganta kai na. Wannan ko daya bai dace ba,” Haaland ya bayyana.

Ya kuma yi magana kan kocin Manchester City Pep Guardiola wanda ya rike wata a nasarorin da ya ke yi a gasar Premiere League inda ya dauki kambun har sau shida kuma ma zai iya sake samun nasara duk da irin koma bayan da gefen na sa ke fuskanta.

“Shi(Guardiola) ya yi nasara a Premier League har sau shida a cikin shekaru bakwai dan haka abu ne da ba za mu iya taba mantawa ba. Zai samar mana mafita. Abun da ya ke yi ke nan kowace shekara. Kuma mun yi imani da shi.”

DUBAWA ta sake yin amfani da wata manhajar dan tantance bidiyon abun da ya sake nuna cewa an kwaskware bidiyon ne kadai. Bisa sakamakon da ya nuna kashi 60 cikin 100 na bidiyon duka kagawa aka yi ba gaskiya ba ne.

Facebook video showing Haaland apologising to Arteta, manipulated

Hoton sakamakon da aka samu daga manhajan bincike na Deepware

DUBAWA ta kuma sake gudanar da binciken mahimman kalmomi daga hirar da Haalan ya yi bayan wasasu da Aston Villa, wannan ne ma ya kai mu ga rahotanni na gida da na waje amma kowannensu da inda ya sa gaba.

Sky Sports ya rawaito cewa dan wasan gaban Manchester City din ya yi bayani kan rashin kokarinsa sadda suka yi wasa da Astin Villa.

Jaridun Daily Mail, Premier League, The Mirror, da Daily Post su ma sun rawaito rahotanni irin wannan ranar 21 ga watan Disemban 2024.

Mun sake dubawa dan mu gani ko Haaland ya baiwa shugaban Arsenal hakuri mu ga ko wata kafa mai nagarta ta dauki labarin amma ba mu ga komai ba.

A Karshe

Binciken DUBAWA ya bayyana cewa Haaland bai baiwa Arteta hakuri kamar yadda bidiyon ya yi bayani ba. Ana zargin an gyara bidiyon ne ba na gaskiya ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »