African LanguagesHausa

CBN ya fitar da sabbin katunan banki sai dai ba’a kai matakin da za’a fara amfani da su ba

Zargi: Wani labarin da aka wallafa a shafin Facebook na zargin wai babban bankin Najeriya zai fitar da katin bankin da kowa zai iya amfani da shi ko da ma wani banki ya ke, domin zai dakatar da bankuna daga bayar da na su katin sai dai kowa ya yi amfani da wanda ya fitar

Wannan gaskiya ne. Babban bankin Najeriya ya kaddamar da wani katin bankin da za’a rika amfani da shi a cikin gida daga watan janairun 2023. Sai dai ba’a riga an fara amfani da su ba.

Cikakken labari

Yayin da fagen hada-hadar kudi a duniya ke kokarin zurfafa matakin tafiya da kowa da kowa domin inganta sayayya da kati maimakon takardun kudi ko tsaba, manyan bankunan kasashe na kokarin ganin su ma ba’a bar su a baya ba, abin da ya sa su ma su ke neman hanyoyin tabbatar da kasuwanci ba tare da wata matsala ba.

Kwanan nan aka ga wani labari a shafin Oluwatofunmi Wisdom, shafin wanda ke da ma’abota da yawa sun kai 400,000, ya bayyana cewa babban bankin Najeriya za ta fitar da wani katin banki wanda shi kadai tilo za’a iya amfani da shi a duka bankuna, sa’anan za ta dakatar da sauran katunan sauran bankunan.

Da su ke mayar da martani dangane da batun Ohegam Iyob Fruitfulness ya yi tambaya dangane da yadda wannan zai shafi katin dan kasa da ma yadda matakin zai yi tasiri kan ma’amalolin kudi.

Saura ma sun yi tambayoyi makamantan haka suna alhinin zuwan matakun tare da yin tambayoyi da yawa wadanda ke bukatar amsoshi.

Mahimmancin wannan zargin ne ya sa za mu tantance gaskiyar batun domin mu kawar da jita-jita mu kuma fadakar da ‘yan Najeriya.

Tantancewa

Binciken da mu ka yi a shafin google ya bayyana mana cewa babban bankin Najeriya tare da hadin giwar da tsarin sulhunta tsakanin bankuna a Najeriya sun kaddamar da wani shiri na katunan cikin gida.

Ana sa ran wannan shirin zai daidaita tsarin biyan kudi a Najeriya ya kuma janyo wadanda ba su amfani da banki zuwa cikin tsarin kudin kasar. Ana sa ran katin zai yi karfin da ma zai yi hammaya da manyan katunan banki irinsu Mastercard da visacard.

Nwanisobi Osita shi ne darektan sadarwa da kamfanoni a CBN wanda a wata sanarwa da ya fitar ya ce, “Samar da shirin kati irin wannan a cikin gida zai kara ingancin bayanan mu, wanda zai kuma taimaka wajen bunkasa yanayin samar da kayayyakin da ake iya sarrafawa a cikin gida da ma ayyuka ta yadda zai rage yawan bukatar da ake gani na kudaden kasashen ketare.”

Jaridun Premium Times da Vanguard sun dauki labarin tun a watan Oktoban 2022 kuma kwanan nan jaridun Punch da Sun Online su ma sun yi labarin.

A hirar da mu ka yi ta wayar tarho da Emmanuel Idenyi Shaibu wani mai nazarin harkokin banki, ya tabbatar ma na cewa lallai an kaddamar da shirin ranar 16 ga watan Janairu. Sai dai ya ce za’a fara raba katunan ne bayan babban bankin Najeriya ya gana kwamitin bankuna. A bayaninsa, sabbin katunan ba za su hana tsoffin aiki ba.

Ya kara da cewa katunan ba za su yi dogaro da mastercard ko visa ba sai dai babban kalubalen da zai iya fuskanta shi ne idan har aka yi amfani da zamba aka yi banna da katin. Emmanuel Idenyi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da katin sadda su ka bulla wajen yin ayyukan yau da kullun ne kawai.

A karshe 

Bisa bayanan da babban bankin Najeriya tare da NIBSS su ka bayar a hukumance, sabon katin zai fara aiki 16 ga watan Janairun 2023. Sai dai babu tabbacin sadda za’a fara amfani da su da ma sadda za’a daina amfani da tsoffin katunan.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button