Getting your Trinity Audio player ready...
|
Tsoron EFCC ya shiga zukatan al’umma da dama a Najeriya, a watanni na baya-bayan nan ayyuka na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ya sake bayyana, ganin yadda ake ganin jami’an hukumar na dirar mikiya kan wasu fitattun mutane da ake zargi da tozarta naira (Naira abuse) da wasu da ake zargin suna aikata zamba ta hanyar intanet (suspected internet fraudsters), da alama dai wannan hukuma bata yin da sauki ga wadanda suka yi ba daidai ba kan sha’anin arzikin kasar.
Sai dai a baya-bayan nan an kara samun mutane na shiga wata sabuwar fargabar.
Wani mai amfani da shafin X a baya-bayan nan ya yi wata da’awa (claimed) cewa idan mutum ta hanyar amfanmi da wayar hannu ya aika da kudi da ya kai miliyan biyar daga asusun ajiyarsa zuwa wani asusun kowani kamfani ya tura kudi da suka kai miliyan 10 to duka laifi ne da ya shafi hada-hadar kudade.
Mai da’awar ya kara da cewa irin wannan hada-hada na iya jawowa mutum ya fada komar hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa wato (EFCC).
Hoton da’awar a shafin X.
Ya zuwa ranar Asabar 24 ga watan Mayu,2025, wannan da’awa ta samu wadanda suka sake yadata su 1,000 (retweets) da mutane 3,700 da suka nuna sha’awarsu (Likes) da mutane da suka kalla 548,000 (Views). Mun kuma gano wasu wallafar a shafukan Facebook da TikTok da Instagram.
Yayin da wasu kalilan mutane ke nuna shakku kan sahihancin wannan da’awa, wasu da dama na ganin haka batun yake gaskiya ne, kamar wannan @highmost369, da ke cewa kai al’ummar Najeriya na rayuwa cikin kunci da kayyade-kayyade.
“Nayi fatan ace ina rayuwa a Najeriya, amma abin da nake gani, ina ga zai fi min kyau na ci gaba da rayuwa ta a kasata wato Ghan, na yi rantsuwa cewa idan ka rayu a Najeriya ba makawa za ka iya rayuwa a wuta, babu wani laifi, kai ku fa ‘yan Najeriya kuna kokari.’’ Kamar yadda ya rubuta.
Wani mai amfani da shafin Richard Oladipo, na cewa ne, “Hakikanin masu zambar kudade basa amfani da asusun ajiyarsu na banki, suna yawo ne da kudade a cikin GMG.’’
Wasu kuma kamar @blackkarmae da @Olowe sun bayyana cewa “wannan sabuwar doka ” ana so ne a shigar da kabilanci kan batun shari’ar Martin Vincent’s (VDM) (recent case).
“… Tun da basu da wata hujja da za su kama shi da ita suna zuwa ne da abubnuwa da dama don su tuhume shi” kamar yadda Olowe ya rubuta.
Kana iya wadannan tambayoyi, “ Me zai sanya a kama ni saboda na kashe kudadena? “Wannan na nufi ba za mu shaki iskar ‘yanci ba a wannan kasa? Me ma ake nufi da almundahnar kudade?”
Wannan makala ta yi kokarin amsa wadannan tambayoyi da ma karin haske kan wasu laifukan wadanda baka san su ba.
Menene almundahnar kudade?
Almundahnar kudade (Money laundering) shine a rika yin hada-hadar haramtattun kudade da aka samu ko kudaden da aka samu daga wani kasuwanci da ke zama haramun, sai a nuna kamar an samo su ne ta hanya ta halak.
A hanya mafi sauki za a iya bayyana kudaden almundahna a matsayin kudade da aka samu ta haram, sannan a rika boye-boye a kokarin kada a gano asalin inda kudaden suka fito, a nuna na halak ne don a kashe su ba tare da wani zargi ba.
A Najeriya almundahnar kudade laifi ne babba, kuma akwai doka da aka tanada don hukunta masu wannan laifi wato dokar (Money Laundering (Prevention and Prohibition) Act, 2022.) Karkashin wannan doka a kwai wani sashi da aka tanada ( Special Control Unit Against Money Laundering (SCUML) wanda ya ba wa EFCC dama ta tabbatar da mutane sun mutunta dokar da lura da hada-hadar da ake yi ta kudade da gudanar da bincike kan abin da suka gano wani zargi a kansu da gabatar da wadanda aka kama da laifi zuwa gaban kuliya.
Yayin da wannan doka ta fito da mabanbantan ayyuka na almundahnar kudade da hukuncin da ke kansu, anan ga wasu abubuwa da ya kamata a sani:
- Musayar kudade da suka haure miliyan biyar ana gindaya masu ka’ida.
Sashi na biyu2 na dokar ya nunar da cewa mutum guda ba zai biya ko a biya shi kudi sama da miliyan biyar ba “kudi hannu” idan kana son yin haka to ya zama dole ka ziyarci banki sai ka kai kudaden. Idan kuma kamfani ne shima iyakar abin da zai kashe a “kudin hannu na zahiri’’ shine naira miliyan 10 a kowace rana.
Alalafia Qudus, Lauya ne da yayi magana da DUBAWA kan wannan batu ko doka, yace abin lura shine an tanadi wannan doka ne don takaita amfani da kudade a zahiri.
Wannan adadi na magana ne ta kudin da za a baka a hannu ba kudin da za a aika ta laturoni ba.
“Kudin da aka aika ta hanyar laturoni ba su zama na haram ba duk yawansu, ba za a ce kawai na laifi ba ne.” a cewarsa
2. Ana iya ba da rahotonka amma ba a ce a kama ka ba.
Kasancewar ka yi biyayya ga sashin na biyu na dokar, baya nufin ba za a ba da rahotonka ba. Me hakan ke nufi? Bankuna da ma’aikatun hada-hadar kudade suna aza ayar tambaya kan kudade da aka shigar ko aka fitar muddin sun haura miliyan biyar ko miliyan 10 cikin kwanaki 7. Wannan shi ake kira ba da rahoton hada-hadar kudade Currency Transaction Report (CTR). Wannan wani bangare ne na tsarin da ke iya gano wani abun zargi ko wata hada-hada da ke da ayar tambaya akanta.
Wani lauyan ma Idris Balogun, ya fada wa DUBAWA cewa ana ba da umarni ga bankuna daga lokaci zuwa lokaci su rika bincikar abokan huldarsu.
“Domin ganin an yi biyayya ga dokoki na yaki da almundahnar kudade da zarar an ga wasu kudade sun shiga asusu kuma aka ga alamun zargi a kansu to ana sanya masu alamar tambaya. Wasu bankunan ma kan rike kudaden har sai an tuntubi mai asusun ajiyar ganin kudaden sun kasance baki da ba a saba gani ba, Idan aka tabbatar nasa ne sai a sakar masa. Idan kuma mai asusun ya gaza ba da hujjoji da suka gamsar ya zama wajibi a shigar da hukumar ta EFCC cikin batun,” a cewar lauyan.
Duk da cewa an ba da rahotonka ga EFCC har yanzu baya nufin kai mai laifi ne, yana nufi ne za a duba hada-hadar don gano gaskiya, idan har ka gaza ba da gamsassun shedu sai EFCC ta gayyace ka don bayani.
3. Rarraba hada-hadar kudade wannan ma na iya jawo wa mutum matsala.
Wasu mutanen na tunanin cewa za su iya rarraba kudade suna turawa kadan-kadan don kaucewa tuhuma, wasu kuma sai su tura bankuna da dama , wannan ma na iya zama babban laifi, kasancewar ana bayyana wannan yunkuri da zama dabarar yaudarar masu sa idanu kamar yadda yake a sashi na 2(2).
Wannan sashi yace “Mutum kada yayi hada-hada sau biyu ko sama da haka da wata cibiyar hada-hada ko wasu cibiyoyin hada-hada ko ya tsara amfani da wasu cibiyoyi da ba na hada-hadar kudade ba da wasu kwararru da zummar (a) don kaucewa ba da rahoton wanda yake karkashin doka; (b)ko karya doka da aka tanada karashin wannan doka a fitar da wasu bayanai ko ta wane hali ko hanya.”
4. Za a iya daure ka
Dokar almundahnar kudade ta tanadi hukunci kan laifuka daban-daban. Idan mutum ya yi wa banki yankan baya yayi hada-hadar da ta haure miliyan biyar zaa iya daure shi tsawon shekaru uku ko a ci tararsa miliyan 10 ko a hada masa duka biyun. Idan kuma kamfani ne za a ci tara ta naira miliyan 25 za kuma ya iya rasa lasisinsa na gudanar da aiki.
Wasu laifukan kuma masu alaka da almundahnar idan aka kama mutum da shi zai iya fuskantar hukunci na ya kwashe shekaru 14 a gidan kaso ko a ci shi tara ta ninki hudu na kudin da aka kama shi da laifi akansu.
Abin bai tsaya a nan ba, idan banki ya gaza sanya alamar tambaya kan wata hada-hada da ta zarce ka’ida, za a iya cin tararsa, ko tarar ta koma kan ma’aikacin da yayi sakaci aka aikata zambar ko almundahna.
Karshe
Da’awar fargabar da ake da ita kan hada-hadar kudin na bankuna da batun kamun na EFCC ba baki daya haka bane kuma ba za a ce duka gaskiya ba ne, Abin da ke da muhimmanci shine ina kudaden suka fito da kuma dalilin hada-hadar, idan kudade ne halastattu babu dalilin fargaba, idan kuwa kudi ne na rashin gaskiya to ka tsammaci kwankwasa kofa daga jami’an EFCC.