Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook kwanan nan ya yi da’awar cewa jiragen kasa a Najeriya sun fi na ko’ina gudu a nahiyar Afirka.

Hukunci: Da gaske ne! Jan layin na jiragen kasan Legas wanda ke da gudun kilomita 330 cikin sa’a guda shi ne mafi gudu a Afirka.
Cikakken bayani
A duniya baki daya Globally, samar da cigaba a bangaren da ya shafi ababen more rayuwa ita ce babbar manuniyar cigaba. Dan haka ba abun mamaki ba ne wai dan gwamnatoci masu sanin ya kamata suka kashe babban kaso na kasafin kudinsu a kan ababen more rayuwa.
Kara yawan jarin da ake zubawa a bangaren sufuri, mysamman a birane na daga cikin abubuwan da aka yi imanin cewa suna tasiri mai ma’ana kan tattalin arzikin kasashe.
A nahiyar Afirka, gibin da ake samu wajen ababen more rayuwa babban abun tattaunawa ne a duk sadda aka yi la’akari da ayyukan gina kasa, musamman tsakanin ‘yan kasa da masu ruwa da tsaki.
Kwanan nan wani marubuci na taskar blog, a shafin Facebook mai suna Africa View Facts, ya yi da’awar cewa jiragen kasa na sufurin Najeriya sun fi kowanne gudu a nahiyar Afirka baki daya.
“Najeriya ce ke da jirgin kasa mafi suari a Afirka, jirgin Red Line. Yanzu ana fadada samun layin sau biyar da safe da hudu da yamma kowace rana daga sau biyu da safe. Jirgin na tafiyar kilometa 330 cikin sa’a daya,” a cewar mawallafin.
Wannan ya janyo ra’ayoyi mabanbanta inda da yawa suka nuna cewa ba su gaskata da labarin ba.
Wani mai amfani da shafin mai suna, Atunde Akanbi Wasiu, cewa ya yi, “Ku je kasashen Afirka ta Kudu, Kenya, Ethiopia da sauransu. Za ku ga jiragen da suka fi wadannan sayri.
Shi kuma, Zaidu Aliyu, cewa ya yi, “A ina jirgin ya ke? Mr Man, ba mu ma da jirgi a Najeriya.”
Sauran masu amfani da shafin kuma sun yabawa kasar saboda wannan gagarumin cigaba suna fatan cewa cigaban zai shafi sauran yankunan kasar su ma.
DUBAWA ta sanya ido kan wannan mahawarar kuma ta yanke shawarar tabbatar da sahihancin wannan lamarin
Tantancewa
Layin dogon na jihar Legas mai Red Line Mass Transit rail system (LRMT) a ranar 29 ga watan Fabrairun 2024 shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da shi bayan da aka shafe shekaru uku ana ginawa.
Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwoolu ya ce fasinjoji sama da dubu 500 za’a rika dauka kowace rana a matakin farko na shirin, wanda ke da tsawon kilometa 27 daga Agbado zuwa Oyingbo, da tshoshi takwas a Agbado, Iju, Agege, Ikeja, Oshodi, Mushin, Yaba, da Oyingbo.
Saboda layin dogon na LRMT, gwamnatin ta sayo jirage biyu kirar Talgo Series 8, kowannensu mai gudun 330kmph.
Jiragen dama can an kera su dan su hada garuruwan Madison da Milwaukee a Amurka.
An gina su da fasahar zamani, da jiki mara nauyi wadda aka yi amfani da karfen aluminium cikin salon da zai kawar da hadari bisa tanadin hukumar kula da jiragen kasa na gwamnatin tarayya dan gudanar da ayyukansu ba tare da wata matsaa ba. Wannan kirar ta Talgo series 8 kyma ta yi tanadi wa wadanda ke amfani da keke.
Wasu fasahohin da suka banbanta jirgin da sauran kuma sun hada da kofofin da ke bude kansu su kuma rufe kansu a ciki da wajen jirgin, da kofin da suke hada dakunan jirgin da wuraren cajin komputoci da wayoyi da duk ma dai wani abin da ke amfani da wutar lantarkin da ake so a yi amfani da shi, akwai kuma intanet, sa’annan da jaridu da mujallu dan fasinjoji, bacin haka akwai ban daki babba daya a tsakiyar jirgin yayin da sauran kuma na zamani ne.
Kafin nan, layin jirgin Al-Boraq na Morocco ne mafi guda wanda ke iya yin kilometa 320 cikin sa’a guda. A watan Nuwamban 2018 aka kaddamar da layin jirgin dan ya rika hada biranen Tangier da Casablanca. Ko da shi ke tilas a yi bayanin cewa sadda ake gwaji, layin na Albaroq ya yi gudun kilometa 357 cikin sa’a daya.
To sai dai har yanzu ana gudanar da shirin da zai ga kamfanin Alstom ya kawo jiragen da ke gudun kilometa 357 guda 12 a kasar. Za su yi haka be saboda gasar cin kofin kwallan kafa na duniyar da za’a yi a kasar a shekarar 2030, kuma ana sa ran kamfanin zai fara shigar da jiragen a shekarar 2027.
A waje guda kyma gwamnatin jihar Legas din ta sake kaddamar da wani shirin na Blue Line wanda shi ma kilometa 27 ne kuma ya fara aiki a shekarar 2023 da jiragen da ke tafiyar kilometa 80 cikin sa’a daya
Kwannan nan, gwamnatin ta sa hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya dan fara aiki kan wani layin mai tsawon kilometa 68 wato Green Line, wanda ake kyautata zatin shi ma zai kara habbaka fannin sugurin.
Wasu karin jiragen kasar masu gudun gaske a wasu sassan duniya na da yawa, inda mafi gudu ya ke samuwa a kasar China, wanda ke gudun kilometa 460. Jirgin mai suna Shanghai Maglev shi ne ya ke daukar fasinjoji da fasahar magnetic levitation (Maglev) a maimakon irin tayoyin da aka sani.
A Karshe
Da’awar cewa Najeriya ce ke da jiragen kasar da suka fi gudu a nahiyar Afirka gaskiya ce. Jiragen legas na Red Line na iya tafiyar kilometa 330 cikin sa’a daya har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan labarin.