HausaAfrican Languages

Da gaske ne yana da amfani a jinkirta yanke cibiya

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Jinin da ke shiga jikin jariri daga uwa na da amfani ga lafiyar jariri sannan kada a yi hanzari wajen yanke cibiya da ke hade jariri da mahaifar uwarsa.

Da gaske ne yana da amfani a jinkirta yanke cibiya

Hukunci: Gaskiya ne! Shedu daga jami’an kimiya da wasu hukumomi na lafiya da kwararru a fannin na lafiya sun goyi bayan jinkirta yanke cibiya kasancewar a kwai wasu sinadarai muhimmai da ake bukatar ganin sun shiga jikin jaririn.

Cikakken Sako

A ranar 18 ga watan Yuli,2025 wani sako a shafin Facebook da aka wallafa (post) a shafin Zainab Suleiman ya ja hankali inda a sakon da ta wallafa take cewa bai kamata a ce ana gaggauta yanke cibiyar jarirai ba da zarar an haife su . A hoton da ta wallafa a kwai wani jariri Bature inda ake ganin cibiyar na sadar da wasu sinadarai daga uwar zuwa abin da ta haifa. “Duk wani jini ya tafi zuwa jaririn kamar yadda tsarin yake.” A wannan gaba ce yayi daidai a yanke cibiyar a datse ta.

 A wallafar ta yi zargin cewa wasu asibitocin na gaggawar yanke cibiyar cikin dakikoki na haifar jaririn, “dazarar an haifi jaririn , jami’an za su gaggawa ana fadawa iyaye cewa haka ake yi.”Babu wanda zai tsaya ya tambaya …. Shin menene a cikin cibiyar?” a cewar wallafar.

Tace a jinin da ake gani cikin cibiya ba “kari” bane ko abin da ya lalace, amma abu ne mai muhimmanci “ajiya ce muhimmiya a fannin halitta,” akwai iska isasshiya ta oxygen ga kwayoyin halitta masu ba da kariya ga sinadarin Iron da wasu kwayoyin halitta masu amfani ga girman jariri da bashi kariya.Tace saurin datse cibiyar na hana jaririn samun wannan moriya m nan ta sake nuna muhimmancin wannan jini na jikin cibiya da mahaifa abubuwan da ake iya siyarwa don amfani a dakin bincike da wajen hada magunguna da abubuwan da suka shafi kayan shafe-shafe.

Duk da cewa a sakon da ta wallafa bai bayyana tsawon wane lokaci ne ya kamata a datse cibiyar ba, ta bukaci iyaye su tabbatar da ganin jinin ya kammala tafiya kafin yankewa. Ganin yadda Zainab ke da yawan mabiya (page) a shafinta da suka kai 74,000 da yadda wannan wallafa ta samu martani har 547 , wannan ya ja hankali tare da kawo rudani da taka tsantsan. 

Daya daga cikin masu amfani da shafin Facebook, Kotto Myahwegi, ya rubuta cewa: “ A  al’adar mutanen Afurka cibiya ana binne ta a wani boyayyen waje cikin gida, ban san wannan bayani ba.”  

Wani mai amfani da shafin Abdulrahman Muhammad, ya mayar da martani kan wannan wallafa inda yake cewa “Wannan abu ne na yaudara “Ya kamata ne a datse cikin mintuna daga daya zuwa uku bayan yaro yayi kuka an ga yana da alamun koshin lafiya. (APGAR).”

Shi kuwa King Noble bayyana taka tsantsan yayi inda yake cewa “Idan unguwar zoma ko malamar asibiti ce ta fadamin haka, zance to ta bani a rubuce duk abin da ya samu jaririna alhaki a kanta, ba mai sani a cikin matsala.”

Batun jinkirta yanke cibiyar jariri abune muhimmi kasancewar ya shafi lafiyar sabbin jarirai da aka haifa, gudanar da bincike kan lamarin babban abu ne kasancewar ya shafi iyaye da masu lura da marasa lafiya kwararru abin da zai sa su dauki mataki na kimiya ba kawai abin da wani ya wallafa ba da ka iya sanya tsoro a zukatan al’umma.

Tantancewa

 A bincikenmu mun gano cewa ba Zainab Suleiman ta fara wannan labari ba ya samo asali ne daga Jodi Shabazz, da aka bincika cikin hanzari a shafin intanet ya kaimu ga shafin Jodi, wacce ke zama likitar gargajiya da zamani (Naturopathic Doctor), da ta fara wallafa wannan fadakarwa (original post)  ga wadanda take isarwa sako a ranar 16 ga watan Yuli,2025.

Wannan ya jawo zurfafa bincike na kimiya da matsayar likitoci kan batun na jinkirta yanke cibiyar jarirai.

Domin tantancewa mun duba tsari da shawarwari daga jagorori a fannin kula da lafiya da kungiyoyi na jami’an lafiya da suka hadar da Hukumar Lafiya ta Duniya World Health Organisation (WHO) da American College of Obstetricians and Gynaecologists (ACOG) da American Academy of Paediatrics (AAP da ma jin ta bakin kwararru a fannin na lafiya.

Matakan da Hukumar Lafiya ta Duniya ta shimfida (WHO guidelines) kan batun jinkirta yanke cibiyar wanda aka fitar a 2014 da sake sabuntawa a 2020 ya nuni da cewa an ba da shawarar cewa jarirai sabbin haihuwa (term ko preterm) wadanda basu fuskanci matsi ba wajen ganin sun yi numfashi, bai kamata a yanke masu cibiya ba kafin cikar minti guda da haihuwarsu.

Sai dai kuma ta ba da shawarar cewa sabbin haihuwar wadanda basu yi numfashin ba sai a shafa bayansu ninki biyu zuwa uku kafin daure cibiyar, sannan a yi kokarin ganin sun yi numfashi ta hanyar dabarun na jami’an lafiya.

Wannan shawara ta zama sheda da ke nuna bukatar ganin a jinkirta yanke cibiyar jariran, don samun isasshiyar lafiya da samun sinadarai da ake bukata. Hukumar ta WHO ta ce “Jinkirta yanke cibiyar (DCC) da akalla dakika 60 abu ne mai kyau don ingantar lafiyar jaririn da uwarsa da sinadaran da zai samu.”

Haka nan kuma kwalejin jami’an kula da goyon ciki da likitocin mata ta Amurka ( American College of Obstetricians and Gynaecologists (ACOG) ta ba da shawarar a jinkirta yanke cibiyar jariri da misalin dakika 30 zuwa dakika 60 bayan haihuwar jariri a jariran da suka cika lokacin haihuwa da wadanda basu karasa ba.

Shima dai kwamitin jami’an lafiyar ACOG Committee Opinion No. 814 (2017, reaffirmed 2023), ya nunar da cewa “Jinkirta yanke cibiya da dakika 30 zuwa dakika 60 na da muhimmanci ga jariran da ake haihuwa wadanda lokacin haihuwarsu ya cika da wadanda bai karasa ba.”

Suka kara da cewa yin hakan na kara sawa yaro ya samu wadatar jini a jikinsa lokacin da aka haife shi ya samu sinadaran Iron, abin da zai taimaki yaro a watanninsa na farkon rayuwa haka kuma wajen bunkasar kwakwalwarsa.

Makarantar koyon aikin kula da jarrai a Amurka (AAP) ta goyi baya (supports) da a rika jinkirta yanke cibiyar da dakika 30 zuwa dakika 60 don samun jariri lafiyayye. Wannan makaranta ta AAP ta kara jaddada bukatar hakan kasancewar za a samu isasshen sinadarin iron a jikin jariri haka nan zai taimaka wajen kare jariri daga cutar karancin jini.

Abin lura shine yawancin bincike ya nuna amfanin jinkirta yanke cibiya. An yi sharhi da aka wallafa a cikin bayanan da ake tattarawa na (The Cochrane Database of Systematic Reviews) a shekarar 2014, aka kuma sabunta a 2018. Bayanan sun nunar da cewa jinkirtawar sama da minti daya yafi alfanu da a yanke kasa da minti guda abin da ke sawa jariri ya samu isassen jini, haka nan sinadarin iron da zai dauki lokaci mai tsawo na watannin haihuwarsa.

Masana a fannin lafiya da dama a duniya sun goyi bayan wannan tsari.  Alan Greene, farfesa a fanin likitancin kula da yara a jami’ar (Stanford University School of Medicine), tsawon lokaci yana fafutuka (advocated) na a rika jinkirta yanke cibiya, saboda muhimmanci da ke akwai wajen isar da isasshen jini daga uwa zuwa jaririnta. Yace “Kimanin kaso uku na jinin jariri yana cikin mahaifa a lokacin da aka haifi jariri, idan an yanke cibiyar wannan na nufin an yanke wannan jini da zai tafi zuwa jaririn.”  

Judith Mercer, jagorar bincike kuma farfesa a fannin ilimin jinya a Jami’ar Rhode Island wacce aikinta ya taka muhimmiyar rawa wajen dora al’umma kan hanya (significantly influenced) ta nunar da muhimmacin hakan ga lafiyar jariri.  

Ta kara bayani da cewa, “ Tsagaita yanke cibiya na ba da damar fitar da sinadaran daga mahaifa zuwa ga jaririn, inda yaron zai samu isasshen jini da garkuwa wadanda muhimmai ne ga ci gaba da girman yaro da lafiyarsa.”

Wadannan bayanai da ra’ayoyin kwararru sun nunar da muhimmancin tsagaitawar da dakikoki 30 zuwa dakika 60 ga yaran da aka haifa lafiyayyu , Wannan lokaci zai ba da dama ta tafiyar wasu muhimman sinadarai daga mahaifar zuwa jaririn ta yadda zai amfana da tarin abubuwa kamar yadda mai wallafar ta nunar, musamman samun sinadaran na iron da karin jini, abin da ke taimakawa wajen ci gaban kwakwalwa.

A Najeriya, bayanan shawarwarin na kasa da kasa da aka fitar da kuma wasu ‘yan bayanai na shedu da aka samu a kasar sun nunar da muhimmancin jinkirta yanke cibiyar da tsawon kimanin dakika 60 kamar yadda jami’an lafiyar suka nunar a kasar abin da zai taimaka wajen bunkasar lafiyar jaririn, wannan tsari na samun karbuwa musamman a wajen unguwar zoma da suka samu horo a fadin kasar.

A wani nazari na taron kawarawa juna sani da aka yi a shekarar 2021 survey a cibiyar da ke kula da yara jarirai da ake haifa a Lagos (LASUTH). Taron da ya tattaro masu karbar haihuwa 55 ( likitoci da unguwar zoma) ya nunar da cewa kaso 76.4 cikin 100 suna da masaniyar amfanin jinkirta yanke cibiyar jarirai. Kaso 49.1 cikin 100 na yin hakan, kuma a cikin masu aiwatarwar suna daukar lokaci daga dakika 30 zuwa mintuna uku, wasu kadan daga cikinsu kuma suna tsayawa ne har sai sun ga babu abin da ke fita daga mahaifar zuwa jariri.

Ibrahim Shuaib, wani lokita ne a Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya (FMC), Katsina, ya tabbatar da cewa jinkirta yanke cibiyar jarirai abu ne muhimmi ga sabbin haihuwa “musamman wadanda aka haifa ba da cikakkiyar koshin lafiya ba.”

Sai dai ya kara da cewa idan aka haifi yaro cikin koshin lafiya kuma ya fara kuka, tsawaita lokaci kafin yanke masa cibiya fiye da yadda yake a ka’ida ba  dole ba ne. 

Karshe

Da’awar cewa jinkirta yanke cibiyar jarirai na da amfani ga lafiyar jariran gaskiya ne.Manya-manyan cibiyoyin kula da lafiya kamar su Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Kungiyar jami’an lafiya masu kula da goyon ciki da likitocin mata a Amurka  (ACOG) da Kwalejin karatun kula da lafiyar jarirai ta Amurka (AAP) sun ba da shawarar cewa ana iya tsagaitawa tsakanin dakika 30 zuwa dakika 60 kafin yanke cibiyar jariran da zarar an haife su.

Nazari da aka yi cikin al’umma da ra’ayoyin kwararru sun tabbatar da cewa a Najeriya cibiyoyin kula da lafiya sun goyi bayan jinkirta yanke cibiya musamman idan jaririn ba a cikin wani hali yake ba na bukatar wata kulawar gaggawa. Ya kamata iyaye su tattauna da jami’an lafiya kan batun na jinkirta yanke cibiya a bi ka’idoji da jami’an lafiya suka shimfida.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »