African LanguagesHausa

Da gaske ne za a tiso keyar Simon Ekpa don ya fuskanci tuhumar ta’addanci a Najeriya?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafinFacebook yayi zargi (alleged) cewa Simon Ekpa, dan asalin Najeriya mai takardar zama a Finland da ke fafutukar neman awaren Biafra za a tiso keyarsa daga Finland zuwa Najeriya a watan Yuli 2025 don ya fuskunci tuhumar aikata ta’addanci.

Da gaske ne za a tiso keyar Simon Ekpa don ya fuskanci tuhumar ta’addanci a Najeriya?

Hukunci: Karya ce! Sabanin labaran da suka yadu a shafukan sada zumunta na Facebook da X, babu wata kafar yada labarai mai inganci da ta wallafa wannan labari cewa za a kawo Simon Ekpa Najeriya a watan Yuli na 2025.

Cikakken Sakon

Bisa ga dukkanin alamu Simon Ekpa tsawon lokaci ya kasance shiru ba a jin duriyarsa daga bangaren magoya bayansa da masu bibiyarsa. Wannan batu kuma ya kasance abin lura a bangaren masu bincike da bibiyar tarin bayanai marasa inganci (sheer volume) da ake yi a kansa da ma irin wahala da ake sha idan za a gudanar da binciken gano gaskiya a game da shi..

Bayan da mahukunta a kasar Finland suka kama (arrest) shi  a watan Nuwamba, 2024 saboda wasu dalilai da ke da alaka da ta’addanci an ga tsayawar ayyukansa na ajandar kungiyar IPOB ko tsayar da bazuwar wasu bayanai da ke iya harzuka zukatan al’umma a shafukan intanet ko dakatar da baza labaran karya wadanda ke zuwa kai tsaye daga wajensa.

A watan Maris 2025, wani kwamiti na Najeriya Nigeria Sanctions Committee ya sanya takunkumi ga Simon Ekpa da wasu mutane 16 bisa zargin lafin daukar nauyin ayyukan ta’addanci.Wannan wani yunkuri ne mai karfi wajen ganin an dakile ayyukan ta’addanci kamar yadda yake a kokari na kasa da kasa, don haka ne aka shigar da batun na fafutukar Ekpa wanda shima ake ganin wata alakar da wadancan masu laifukan ta’addancin. Idan ma an dawao da shi kasarsa ba makawa zai fuskanci wasu tarin tuhume-tuhume.

Ana tsaka da wannan ne sai wani mai amfani da shafin Facebook, @Nigerianews, ya wallafa wani hoto na Simon Ekpa a ranar 23 ga watan Afrilu, 2025 tare da taken “Simon Ekpa za a tisa keyarsa zuwa Najeriya a ranar 15 ga watan Yuli don ya fuskanci tarin tuhuma, da ta hadar da zargin ta’addanci da cin amanar kasa da wasu laifuka masu alaka da wannan.”

Lokacin da  DUBAWA ta nazarci wannan wallafa a ranar 6 ga watan Mayu, 2025 ta lura cewa ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu Likes guda 7 da wadada suka kalla 35 kuma wannan wallafa ta bayyana a shafukan Facebook da dama kamar a wadannan wurare here, here, here, here, here, here, da here.

Bayan tsawon watanni da aka dauka ana tattaunawar diflomasiya tsakanin Najeriya da Finland an samu irin wadannan tarin wallafa wadanda ke nuni da cewa kasar ta Finland ta tabbatar da cewa za ta mika shi.

A sashen yin tsokaci wani mai suna @Adajo yayi martani da cewa “Yanzu ne zai san muhimmanci na “yanci.”

Wani ma mai amfani da shafin@JoeIbe, yayi martani ne da cewa “ku kwantar da hankalunku, abu ne da ba zai taba yiwuwa ba.”

Irin wannan da’awa ta sake bayyana a shafin X inda a ranar 22 ga watan Afrilu,2025  aka ganta a shafin  @Aje, wanda ya bayyana stated cewa za a dauko Ekpa daga Finland zuwa Najeriya a ranar 15 ga watan Yuli, 2025 bayan hukunci da kotun Päijät-Häme District Court da ke Lahti ta fitar a ranar 18 ga watan Afrilu,2025. A wannan wallafa har da hoton Ekpa a dakin kurkuku.

Duba da yadda wannan da’awa ta bazu da yadda mutane ke saurin amincewa da labari da suka gani a intanet ba tare da bincike ba, hakan ya sanya DUABAWA ganin wajibcin gudanar da bincike.

Tantancewa

DUBAWA ta gudanar da bincike a shafin intanet na kotun Päijät-Häme District Court da ke a Finland sannan ta duba rahotanni  reports daga kafafan yada labarai na Finland da Najeriya, babu wata sheda da ta nunar da cewa kotun ta Finland ta fitar da wata rana ta tiso keyar Simon Ekpa zuwa Najeriya.

Duk da cewa akwai wasu tsofaffin rahotanni da jawabai na al’umma kamar bayanin da shugaban rundunar sojan Najeriya Janar  Christopher Musa, ya nunar da alamu da ke nuna cewa akwai yiwuwar tiso keyar tasa (possibility of extradition) sai dai babu wani bayani a dangane da ranar komawar kamar yadda da’awar ta nunar.

DUBAWA ta kuma tabbatar confirming da wani rahoto na kafar yada labaran BBC inda lauyan Simon Ekpa wato Kaarle Gummerus, yayi watsi da da’awar cewa zaa tiso keyar Ekpa. A tattaunawar da aka yi da shi ya bayyana cewa jagoran ‘yan awaren ana sa rai zai bayyana a kotu a watan Yuni,2025 don fara sauraren tuhumar da ake masa ba wai za a tiso keyarsa zuwa Najeriya ba.

Kari kan wannan wani rahoto na jaridar Punch reported ya nunar da cewa babban mai gabatar da kara na Gwamnatin Tarayyar Najeriya kuma Atoni Janar (AGF), Lateef Fagbemi (SAN), ya tabbatar da cewa akwai wasu abubuwa da ke bukatar warwara a dangane da shari’ar ta neman a tiso keyar Ekpa, yayin da Najeriya ke tattaunawa da mahukunta na kasar Finland akwai wasu tarin kalubale na shari’a da ke kawo tsaiko a dangane da batun.

Fagbemi yayi bayani da cewa za a tiso Ekpa ne kawai idan har mahukunta na Finland sun kammala tasu shari’a, matsayar da ta yi kama da ta lauyan da ke ba da kariya ga Ekpa.

Ana dai ci gaba da tsare Ekpa wanda ke da takardar zama dan kasa ta Finland da ta Najeriya. Batu na shari’ar da ke nuna cewa za a tiso keyarsa har kawo yanzu akwai sarkakiya.

Hoto da aka sanya a manhajar google don gano asalin hoto ta nunar da cewa hoton da aka wallafa a shafin na X an dauko hoton fuskar EKPA ne aka makala ba asalin fuskarsa ba ce, daga asalin hoton ne  Alamy da aka dauka ranar 13 ga watan Fabrairu,2018Is Simon Ekpa set to be extradited to Nigeria for terrorism?

A Karshe

Da’awar cewa Simon Ekpa za a tiso keyarsa daga Finland zuwa Najeriya karya ce, babu wata kafa sahihiya da ta tabbatar da haka. Kuma lauyansa ya tabbatar da cewa za a fara saurarar tuhumar da ake masa a kotu.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »