African LanguagesHausa

Eh! Gwamna Uba Sani ya taba yin ikirarin cewa a kama shi da laifi idan Nasiru Elrufa’i bai yi aikin ci gaba da bashin dala miliyan 350 na bankin duniya ba, amma bai ce a kama shi idan ya gaza biyan bashin ba

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa ta 1: Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi ikirari a baya cewa, idan Malam Nasiru Elrufa’i ya kasa aiwatar da ayyukan ci gaba da bashin da ya ciyo daga bankin duniya a kama shi.

Da’awa ta 2: Gwamna Uba Sani ya yi ikirarin cewa idan Malam Nasiru Elrufa’i ya gaza biyan bashin dala miliyan 350 a kama shi.

Eh! Gwamna Uba Sani ya taba yin ikirarin cewa a kama shi da laifi idan Nasiru Elrufa’i bai yi aikin ci gaba da bashin dala miliyan 350 na bankin duniya ba, amma bai ce a kama shi idan ya gaza biyan bashin ba

Hukunci na 1: Gaskiya ne! Bincike ya tabbatar da cewa Gwmnan Kaduna a yanzu Uba Sani, yayi wannan ikirarin lokacin da yake kan gaba wajen ganin an samu amincewar majalisar tarayyar Najeriya domin jihar Kaduna ta karbo rance daga Bankin Duniya.

Eh! Gwamna Uba Sani ya taba yin ikirarin cewa a kama shi da laifi idan Nasiru Elrufa’i bai yi aikin ci gaba da bashin dala miliyan 350 na bankin duniya ba, amma bai ce a kama shi idan ya gaza biyan bashin ba

Hukunci na 2: Karya ne! Uba Sani bai yi da’awar cewa a kama shi ba idan Nasiru El-rufa’i ya gaza biyan wannan bashin da ya ciyo.

Cikakken Bayani

Tun bayan da Gwamnan jihar Kaduna na yanzu Uba Sani ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kadunan Nasir El-rufa’i ya jefa jihar cikin tsaka mai wuya sakamakon tulin bashin da ya barwa jihar, alumma da dama ke ta cecekuce akan wanna batu.

Gwamnan Kaduna Uba Sani ya bayyana irin halin kuncin da jihar ke ciki sakamakon bashin da yace ya kai dala miliyan 587 da wasu naira biliyan 85 da kuma kudaden kwangila naira biliyan 115.

Uba Sani ya ce sakamakon dimbin bashin, hatta albashin ma’aikata ba zai iya biya ba.

Daga cikin wannan bashin akwai bashin da ake bin jihar na dala miliyan 350 da Gwamna Nasir Elrufai ya samu nasarar karbowa daga Bankin Duniya a shekara ta 2020, duk kuwa da tirjiya da kuma kin amincewa da ya samu daga wasu ‘yan jihar da al’ummar kasa.

Idan za’a iya tunawa a shekara ta 2017, lokacin da Gwamna Nasir El-rufa’i ya aikawa majalisar tarayya bukatar ta bashi damar karbo bashin daga bankin duniya sai dai Sanatoci dake wakiltar jihar wato Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi na jam’iyyar APC da Danjuma Laah na jami’iyyar PDP sun nuna rashin amincewa da wannan yunkurin cin bashin lamarin da yasa majalisar dattawa ta ki amincewa da bukatar a shekara ta 2018.

Tun a wancan lokacin, Sanata Shehu Sani yayi ta gargadin cewa wannan bashin zai jefa al’umma cikin matsala ba

Wasu na ganin hakan ne ya sa Sanatocin suka kasa komawa majalisar a lokacin zaben 2019, inda Sanata Uba Sani da Sanata Suleiman Kwari suka sami shiga majalisar saboda goyon bayan da suke yi na ganin an ciyo wannan bashin.

Bayan zaben su ne kuma shi Uba Sani ya sha alwashin sake neman bukatar amincewa da majalisar don ta bada dama jihar Kaduna ta karbo bashin.

To sai dai wani labari da wata jaridar da ake wallafawa a shafukan sada zumunta mai suna ATP Hausa tace ta bankaɗo wata tsohuwar magana da Gwamna Uba sani yayi a lokacin mulkin Malam Nasiru El-Rufa’i.

Eh! Gwamna Uba Sani ya taba yin ikirarin cewa a kama shi da laifi idan Nasiru Elrufa’i bai yi aikin ci gaba da bashin dala miliyan 350 na bankin duniya ba, amma bai ce a kama shi idan ya gaza biyan bashin ba
  • Hoton da aka zakulo a shafin Facebook

Wannan labarin ya dauki hankalin jama’a inda aka yi sharhi (Comment) har sau 49, sannan aka yada labarin (Share) sau 36, kamar yadda muka zakulo a ranar 6 ga watan Afrilun 2024.

Dubawa ta yi bincike domin gano gaskiyar wannan labarin, ganin yadda wannan lamarin ya nuna cewa Gwamna Uba Sani yana cikin wadanda suka goyi bayan cin bashin amma kuma yanzu yake korafin cewa bashi ya yiwa jiharsa katutu. 

Tantancewa: (Da’awa ta 1)

A kokarin gano gaskiyar labarin mun dauki wasu muhimman bayanai a cikin labarin da ATP Hausa ta wallafa kamar su kwanan wata, da adadin kudaden da ake magana akan su, sa’annan muka yi amfani da manhajar bincike ta Google inda muka gano labarin da ke tabbatar da hakan a jaridun da ake wallafawa a harshen turanci a Najeriya, wadanda suka hada da jaridar Vanguard, da The Nation, da kuma This Day.

Dukkanin jaridun sun wallafa labarin ne wanda a ciki Uba Sani ke cewa “Ku kama ni da laifi idan El-Rufa’i ya gaza”

Tantancewa: (Da’awa ta 2)

Binciken da muka yi da kuma labarun da muka gani da suka shafi wannan labarin na bashi da bankin duniya ya baiwa jihar Kaduna, babu wurin wurin da Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani yayi ikirarin cewa a kama shi idan Elrufa’i ya gaza biyan bashin a kama shi.

A cewar Kwamishinan kudi na wancan lokacin Suleiman Abdul-Kwari, ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa “rancen yana da ƙarancin kudin ruwa na kashi 0.5 cikin ɗari, tare da lamunin shekaru 10, da kuma wa’adin biyan na shekaru 50.

Wannan ya nuna cewa, a wancan lokacin Uba Sani yana da masaniyar cewa ba za’a fara biyan bashin ba sai bayan shekaru 10, saboda haka kenan bai yi wannan ikirarin ba.

A Karshe

Da’awar dake cewa, Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya taba yin ikirarin cewa a kama shi da laifi idan Tsohon Gwamnan Jihar Malam Nasiru Elrufa’i bai yi aikin ci gaba da bashin dala miliyan 350 da ya karbo daga bankin duniya ba, Gaskiya ne! Kafofin yada labarai da dama sun wallafa labarin
Sai dai Da’awar cewa Uba Sani yace a kama shi idan Elrufa’i ya gaza biyan bashin, Karya ce! Bincike ya nuna cewa sai bayan shekara 10 za’a fara biyan wannan bashi.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button