African LanguagesHausa

Hoton bidiyon gawawwakin da aka kona ya fito daga Tanzaniya ne ba Najeriya ba kamar yadda ake Zargi

Zargi: Wani bidiyo ya bayyana wanda ke zargin walkiya ce ta kona ‘yan bindiga sadda suke kan hanyarsu ra zuwa jihar Zamfara don kai hari kan Kiristoci.

Hoton bidiyon gawawwakin da aka kona ya fito daga Tanzaniya ne ba Najeriya ba kamar yadda ake Zargi

Bincikenmu ya nuna mana cewa bidiyon ta fashewar wata tankar mai ne, wanda ya afku a wani gari mai suna Morogoro da ke Tanzaniya ba a Najeriya. Dan haka wannan zargin ba daidai ba ne

Cikakken labari

A ‘yan kwanakin, Najeriya ta fiskanci kashe-kashe da dama a hannun ‘yan ta’adda. Wadannan hare-hare sun hada da wanda ya faru a wani Coci a Owo da ke jihar Ondo da kuma wadanda su ka kai ga hallakar mutane uku a wadansu Coci-Coci a Kaduna, dan haka addu’o’i dangane da yawan hare-hare ba sabun abu ba ne a wuraren sujada.

Daya daga cikin abubuwan da ake amfani da shi a yi shaidar cewa Allah ya amsa ire-iren addu’o’in ne wani bidiyon da ake ta yada wa a WhatsApp da shafukan Facebook.  Wannan bidiyon na dauke da sakin da ke zargin wai ‘yan bindiga ne walkiya ta kona su yayin da su ke kan hanyar zuwa jihar Zamfara dan hallaka kirirstoci.

“Wannan ya faru ne jiya a Zamfara. An fada mun cewa wasu ‘yan bindiga ne ke kan hanyar zuwa Zamfara dan kai hari kan kiristoci dai dai ba su cimma burinsu ba domin tsawa da walkiya sun fadi a kansu ta yadda su ka kone kurmus har sun fita sigar jikin dan adam. Wa ya ce babu Allah?” in ji sakon.

Ana iya cewa kusan kowa mai waya ya sami wannan sakon saboda yadda aka yada shi a WhatsApp. A shafin Facebook ma an raba sau da yawa, kuma da dama sun dauka labarin gaskiya ne.

A baya DUBAWA ta tantance labarai irin wannan kuma sun kasasnce karya ko kuma yaudara. Shi ya sa ake sake tantance wannan zargin.

Tantancewa.

A lokacin da aka fara tantance wannan labarin babu wata kafar yada labarai da ta rawaito cewa walkiya ya kashe wasu ‘yan bindiga. Dama dai irin wannan labarin dole zai dauki hankali ya kuma kasance a babban shafin kowace jarida. Rashin ganin labarin a jaridu shi ne alamar farko da ke nuna rashin sahihancin labarin.

Haka nan kuma, DUBAWA ta gano cewa sakon bai fadi takamai-mai wajen da abin ya faru a jirar Zamfarar ba bai kuma fadi wajen da kiristocin za su yi taron da maharan ke shirin zuwa su kai harin ba.

Wasu karin bincikem sun nuna cewa an taba amfani da hoton bidiyon a sherkar 2021 domin a fadi irin wannan labarin. Sai dai ko a wancan labarin ba’a fayyace wajen da ake zargin abin ya faru ba a jihar Zamfara.

Da aka sake yin bitan bidiyon, DUBAWA ta gano wadansu abubuwa masu fashe a cikin hoton abin da ya karyata zargin cewa wutar da ta kai ga hallakar mutanen ta tashi a sanadiyyar “walkiya” ne ko “tsawa.” 

Bayan haka binciken mahimman kalmomin da aka yi a YouTube ya bayyana hotunan bidiyoyin fashewar wata tanka da gidan talbijin na Aljazeera da na NTV Kenya suka yi a shekarar 2020 wadan suka yi kama da wanda ake yadawar a yanzu haka.

Aljazeera ta rawaito cewa ana fargabara wasu mutane 60 sun hallaka bayan da wata tankar mai ta fashe a garin Morogoro a Tanzaniya. Dama dai tamkar man ta fadi ne sai jama’a suka taru su debi abin da za su iya sai wutar ta kama yayin da su ke ribibin dibar man,” labarin ya bayyana.

Al Jazeera ta kara da cewa duk da cewa masu agajin gaggawa sun yi iya kokarin su wajen taimakon wadanda wutar ta kama da yawa sun kone ta yadda ba ma za’a iya gane su ba. Baburan wadanda suka zo samun man su ma sun kone.

Da muka sanya bidiyoyin biyu gefe da gefe mun gano abubuwa da yawa iri daya. Na farko, a gaban tankar da ta kone akwai bishiyoyin da wutar ta kona. Na biyu tankar na kwance a waje guda a cikin bidiyoiyn biyu. Na uku kuma duka bidiyoyin biyu sun nuna baburan da suka kone.

Domin gano harshen da mutanen da ke cikin bidiyon ke amfanin da shi, DUBAWA ta tuntub Muhammad Auwal, wani dan Najeriyar da ya iya hausa dan ya fassara abin da su ke fada. Sai dai bai fahimci komai ba, inda ya ce ba ya ji harshen hausa ne su ke amfani da shi.

Mun sake bai wa wadansu wadanda suka iya hausa inda daya daga cikin su ya ce 

“Ba na fahimtar abin da su ke fada, kun tabbata daya daga cikn harsunan Najeriya ne? Shin wannan ma a Najeriya ne kuwa?

Haka nan shi me Abba Adamu ma’aikaci a jaridar Daily Trust shi ma ya ba mu tabbacin cewa harshen ba hausa ba ce.

“Wannan ba hausa ba ce,” ya fada bayan da ya kalli bidiyon.

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa bidiyon ta fashewar wata tankar mai ne, wanda ya afku a wani gari mai suna Morogoro da ke Tanzaniya ba a Najeriya. Dan haka wannan zargin ba daidai ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »