|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya yada wasu hotuna yana da’awa cewa Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci Anthony Joshua a asibiti.

Hukunci: Karya ce. Babu wata hujja mai karfi da ta tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya ziyarci Anthony Joshua a asibiti, hoton da aka yada tare da da’awar an yi amfani da fasahar AI ne wajen kirkirarsa, wasu kafofi sahihai sun bayyana cewa shugaban kasar ya tattauna da Joshua da iyalansa ta hanyar amfani da wayar tarho.
Cikakken Bayani
Anthony Joshua kwararren dan wasan dambe ne mai takardar zama dan kasar Birtaniya wanda ya zama zakaran dambe na duniya har sau biyu ya kasance fitacce a fagen wannan wasan dambe da yayi shuhura a duniya.
Ya taba ci wa Birtaniya lambar zinariya a wasan tsalle-tsalle da motsa jiki na Olympic da aka yi a birnin London a 2012 ya kuma samu lambobin yabo da dama a mataki na duniya
A ranar 29 ga Disamba,2025 Joshua ya samu kai a yanayi na hadarin mota a babbar hanyar zuwa Ibadan daga Legas a Kudu Maso Yammacin Najeriya.
Rahotanni sun nunar da cewa motar da yake ciki Lexus SUV ta kwacewa direba inda ta fadawa babbar mota.
Yayin da Joshua ya sami kananan raunika, wannan hadari yayi sanadin rayukan wasu abokansa makusanta biyu wadanda kuma abokan wasansa ne.
Danwasan damben ba da bata lokaci ba aka garzaya da shi asibiti a Legas inda mahukunta suka tabbatar da cewa ya samu sauki.
Biyo bayan afkuwar lamarin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tuntubi Joshua tare da mahaifiyarsa inda yayi masu gaisuwar ta’aziya tare da yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa.
Ya kuma yi magana da Gwamnan Ogun Dapo Abiodun kan abin da ya shafi lafiyar ta Joshua. A Jawabi da ya fita daga fadar shugaban kasa an tabbatar da cewa shugaban ya tuntubi iyalan don gaisuwa tare da fatan samun sauki cikin gaggawa.
Jim kadan bayan da a shafin Facebook Zamani’s Blog, ya fitar da da’awa cewa shugaban kasa Tinubu da kansa ya kai ziyara asibiti don duba lafiyar Anthony Joshua’ Ga abin da wani bangare ma na taken labari ke cewa “Shin da gaske haka ne? Kasa da sa’oi 24 Tinubu ya fitar da wallafa har guda biyu kan hadarin Joshua. Yayi duk abin da ya wajaba don tabbatar da ganin cewa ya tuntubi iyalansa don jin halin da yake ciki, amma idan mutane 20 suka rasa rayukansu a hadarin mota ba za ka ji duriyarsa ba…Abin lura shine idan dan talaka ne kai ka tashi haikan da nema, babu wanda ya damu da kai, kalli yadda Tinubu ya damu kan fitaccen danwasa Anthonu Joshua. ”
Ya zuwa ranar 31 ga Disamba,2025 wallafar ta samu masu nuna sha’awa 8,300 (likes) da masu nuna tsokaci 634 (comments) da masu sake yadawa 157 (shares).
Wannan da’awa ta samu martani mabanbanta daga masu amfani da shafin Facebook yayin da wasu irin su Ned K Nice, ke kare shugaban kasa inda yake cewa “A magana ta gaskiya babu abin da za a ce shugaban kasa yayi na laifi jinjina ma za a yi masa,” wasu kuma na nuna tantama a nasu bangare.
Wata mai amfani da shafin Aisha Scott ta nuna alamar tambaya a dangane da yadda asibiti yake a Najeriya “wato haka asibiti yake a Najeriya?” a cewarta.
Wasu kamar Blessed Bliss ta yi fatali da da’awar inda tace ban yadda da wannan ba an hada ne da fasahar AI.”
Duba da mabanbantan ra’ayoyi da yiwuwar yada labarai wadanda ba na gaskiya ba shirin DUBAWA yaga dacewar gudanar da bincike don tantance da’awar.
Tantancewa
DUBAWA ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ya gudanar da bincike ko zai ga wasu kafofin yada labarai sahihai da suka buga labarin cewa Shugaba Tinubu ya ziyarci Anthony Joshua amma babu wata kafa ko daya da ta buga labarin.
Kafafan yada labarai irinsu The Punch da BusinessDay, da Premium Times, sun buga labarin amma sun bayyana cewa Shugaba Tinubu yayi magana da Joshua da iyalansa ta hanyar wayar tarho.
Da aka duba shafin X na Shugaba Tinubu ya nuna cewa tabbas shugaban ya tuntubi Joshua da mahaifiyarsa amma bai ziyarce shi a asibiti ba.
Sai kuma a ka sanya hoton a manhajar da ke tantance hoto ko an hada shi ta hanyar amfani da fasahar AI. Sakamako da aka samu daga manhajar Hive Moderation ya nunar da cewa hoton an hada shi ta hanyar amfani da Kirkirarriyar Fasaha ta AI.

Hoton sakamako daga Hive Moderation
Haka kuma an yi amfani da SiteEngine wata manhajar tantance hoton na AI inda ta nuna cewa akwai alamu da kaso 67% da ke nuna cewa wannan hoto an hada shi ne daga manhajar ta AI.

Hoto daga SiteEngine
Karin bincike ya nuna cewa Shugaba Tinubu ma a wannan lokaci ba ya Najeriya an samu rahoto cewa yana Nahiyar Turai don hutu na karshen shekara inda yake shirin tafiya taron kasa da kasa a Abu Dhabi.
A karshe Dada Olusegun, mai taimaka wa shugaban yayi fatali da wannan hoto wanda ya bayyana da cewa na karya ne kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
A Karshe
Da’awar cewa Shugaba Tinubu ya ziyarci Anthony Joshua a asibiti karya ce.



