African LanguagesHausa

Jam’yyar APC ta kwafsa, ta rubuta wa gwamnonin Kogi da Kwara da ma wadansu ministoci mukaman da ba na su ba

Shugabanin jam’iyyar APC mai mulki sun yi kuskure wajen rubuta mukaman wadansu gwamnoni da wani minista a wasu takardun da suka fitar kwanan nan wandada kuma su ka shiga hannun jaridar PREMIUM TIMES.

A takardar da ta kunshi jerin sunaye 86 na mambobin majalisar koli na yakin neman zaben gwamnan da za’a yi a jihar Osun ranar 15 ga watan Yuli, wanda aka fitar ranar talata, jam’iyyar ta kira Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq da na Kogi Yahaya Bello da Ministan Harkokin Matasa da Habaka Wasanni Sunday Dare a matsayin masu digirin digir-gir.

Takardar da aka yi wadannan kura-kuran na dauke da sa-hanun shugaban jam’iyyar Abdullahi Adami da Babban Sakatare Iyiola Omisore.

Majalisar wadda ke karkashin jagorancin shugabannin biyu wato gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu da na Kano Abdullahi Ganduje an kafa ta ne domin taimaka wajen zawarcin kuri’u a zaben jira Osun inda dan jam’iyyarta kuma gwamna mai ci Gboyega Oyetola ke neman yin tazarce.

Da PREMIUM TIMES ta gudanar da bincike ta gano cewa a cikin gwamnonin biyu da ministan babu wanda ke da digirin digir-gir kuma babu wanda ya kasance likita bare har a kira shi da sunan dokta, abin da takardar APCn ta kira su da shi.

Haka nan kuma a cikin ‘yan siyasan uku babu wanda ya taba samun digiri na girmamawa daga wata jami’ar da aka sani a duniya.

Ainihin takardun nuna sakamakon kammala karatu ko kuma cancantar da su ke da shi

Da ma can Mr. AbduRazaq ba shi da takardun makarantar da suka wuce sakandare, ita kanta makarantar sakandaren na sa an yi ta tababan sahihancin sakamakon gabanin zabukan 2019 a jiharsa.

Yayin da ya ke zargin wai ya kammala Kwalejin Gwamnati na Kaduna, inda ya yi jarabawar kammala makaranta a shekarar 1976, abokan hammayarsa sun ce bai kammala makarantar ba.

Ba ya ga rikicin sahihancin takardun makarantar  sakandaren ta sa, gwamnan Kwarar har yau ya gaza dakile mahawarar da ake yi bisa zargin da ya yi na cewa ya kammala digiri bare ma digirin digir-gir.

A daya hannun dai, jaridar ta iya tantance sahihancin takardun makarantar gwaman Kogi daga Firamare, sakandare har zuwa jami’a.

To sai dai babu hujjar cewa ya yi digirin digir-gir daga wata jami’a har ya sa APC ta yi amfani da shi a matsayin mukamin shi.

Mr Bello ya sami digirin shi na farko a fannin lissafin kudi daga jami’ar Ahmadu Bello da ke zaria, jihar Kaduna, kuma daga nan ne ma ya sami digiri na biyu a fannin gudanar da kasuwanci wato Business Administration.

Ko shakka babu, Mr Dare gogagge ne, wanda tsohon dan jarida ne wanda ya yi digirin farko a Alakar Diflomasiyya ta Kasa da Kasa a shekarar 1991, ya kuma sami digiri na biyu a fannin Shari’a da Diflomasiyya q 1996.

Baya ga wadannan, da kuma wadansu lambobin yabo da na karramawa da aka ba shi, babu wani abin da ke nuna cewa yana da digirin digir-gir.

Mun tuntubi masu magana da yawon gwamnonin Kwara da Kogi wato Rafiu Ajakaye da Muhammed Onogwu ta wayar tarho amma babu wanda ya amsa.

Haka nan kuma mun gaza samun Toyin Ibitoye mai magana da yawun Mr. Dare.

Wannan ya zubar da kimar jam’iyyar APC a idon jama’a – In ji kwararre kan tantance gaskiyar bayanai

Editan Dubawa wanda ke kula da sashen kula da binciken gaskiyar bayanai Kemi Busari ya ce abin takaici ne a ce shugabannin APC sun sanya hannu a kan irin wannan bayanin ba tare da sun tuba sun tabbatar wa kansu cewa babu kura-kurai ba.

Ya ce duk da cewa bazuwan bayanan da a gaskiya ba ko wadanda aka gyara dan su zama kamar gaskiya a Najeriya ba sabon abu ba ne a wurin shi, yadda APC ta aikata wannan  ba abu ne mafi takaicin da ya taba gani a shekaru biyar din da ya yi yana tantance irin zarge-zargen da ‘yan siyasa ke yi.

“A tunani na ba dai-dai ba ne a sanya musu mukamin da ba nasu ba. Idan ma har za su yi haka, kamata ya yi su sanya su cikin madogarai. Wannan ba dai-dai ba ne a ce ana ganin shi daga jam’iyya mai mulki, ya kuma kara jaddada irin rashin yardar da ke tsakanin masu mulki da al’umma.

“Muna tinkarar wata shekarar zabe inda mutane da yawa za su iya amfani da dalilai daban-daban wajen yanke shawarar wanda za su zaba, daya daga cikinsu shi ne yawan karatun da su ka yi. Don me zan yarda da ku idan har kuna cewa wanda ya yi digirin farko kawai yana da digirin digir-gir?

“Wannan koma baya ne ga jam’a wajen yanke shawara tunda bayanan da ke fitowa marasa gaskiya ne kuma wannan babbar matsala ce ga masu zabe,” a cewar Mr Busari.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »