|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya fitar da wata wallafa (posted) dauke da jerin sunaye na “kasashe da ya bayyana da cewa su suka fi yawan masu ilimi a Afurka” inda ya bayyana sunan Najeriya a matsayin ta daya.

Hukunci: Karya ce! Kungiyoyi fitattu na kasa da kasa sun sha bayyana Seychelles a matsayin wacce ke kan gaba a tsakanin kasashen Afurka, duba da yadda ake auna matsayin kasashen ta fuskar ilimi inda ake sanya su a mizani na duba yawaitar masu ilimi da jadawalin na ci gaban al’umma Human Development Index (HDI).
Cikakken Sako
A ranar 24 ga watan Agusta,2025 wani shafin Facebook mai suna Comedic Memes (shared) ya wallafa labari inda ya jero wani jerin sunaye na kasashe da suka fi yawan masu ilimi a Afurka. A jerin sunayen ya bayyana Najeriya da zama kasa ta farko sannan wasu kasashe na Afurka suka biyo bayanta.
A wallafa ya ce “KASASHE DA SUKA FI ILIMI A TSAKANIN KASASHE AFURKA”1. Nigeria 2. Morocco 3. Egypt 4. Algeria 5. Seychelles 6. Mauritius 7. Tunisia 8. Kenya 9. Botswana 10. Ghana.”
Ya zuwa ranar 26 ga watan Agusta,2025 wannan wallafa ta ja hankali inda aka samu masu nuna sha’awa likes 19 da masu sharhi comments 25. Wannan wallafa ta samu masu tsokaci kala-kala, wasu na suka wasu kuma na mayar da martani me kama da zolaya daga wasu masu suna irin na ‘yan Afurka ta Kudu.
Daya daga cikin masu amfani da shafin, Muziwokuthula Mashazi, yayi tsokaci da cewa, “Amma duka mun sani cewa wannan jerin sunayen na karya ne, mu mun sha gabanku a fagen ilimi, kun san haka.”
Chris ya rubuta cewa, “Bro SA wato Afurka ta Kudu ita ce ta 1. naga irin wannan jerin sunaye sau shida a wasu guruf din.”
An sake yada wannan wallafa a shafin na Facebook kamar a nan here.
DUBAWA ta shirya gudanar da bincike kan wannan da’awa don tantance matsayin ilimi a nahiyar da kaucewa yada labaran karya.
Tantancewa
Ganin cewa akwai sarkakiya a fitar da wata hanya daya tilo ko wasu hanyoyi da za a ce da sune ake tantance wata kasa da za ta zama ta wadanda suka fi ilimi, wasu kungiyoyi kamar Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya na amfani da wani jadawali ne ciki kuwa har da yawaitar masu ilimi da jadawalin abubuwan da suke haduwa don samar da ci gaban al’umma (Human Development Index (HDI)), don duba wane mataki kasa ta cimma a fagen na samar da ilimi.
Saboda haka mun nazarci bayanan nazari kan al’ummar duniya Literacy Rate by Country 2025 kuma bayanan da muka samu sun nunar da cewa Seychelles ita ke kan gaba a fagen ilimi inda take da maki 95.9% a tsakanin kasashen Afurka sai kuma kasar Afurka ta Kudu da ke da maki (95%) da São Tomé and Principe (94.8%) da Namibia (92.3%) da Mauritius (92.2%. Zaa iya samun wadannan bayanai kuma a Data Pandas da The African Exponent.
Shirin raya kasa na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) da jadawalin ci gaban al’umma Human Development Index (HDI) na auna ci gaban ilimin kasashe ne ta hanyar duba kiyasin yaran da suke makaranta har zuwa shekaru 25 da sama da haka, da duba shekarun da yaran ke shiga makarantar.
A jawaban shirin na MDD UNDP 2023 da jadawalin HDI da ya duba yankin na Afrika Sub-Saharan Africa Region, Seychelles ita ke kan gaba da maki 0.848, sai kasar Mauritius (0.806) sai kuma Afurka ta Kudu (South Africa (0.741) kana Gabon ke biye mata baya da maki (0.733) da Najeriya mai maki (0.560).
Rahotanni na labarai da aka nuna kasashe 10 da ke kan gaba a fannin na ilimi a Afurka kamar yadda aka nunar a Matsh da AfricaFactsZone, sun nunar da cewa Seychelles ita ke kan gaba kana Tunisiya da Mauritius da Afurka ta Kudu suke biye mata baya.
Bayanan da aka samu daga DataPandas Education Rankings, wadanda aka sake sabuntawa a ranar 19 ga watan Mayu,2025 sun nunar da cewa Afrika ta Kudu ita ce ta 61 a jadawalin inda ta sha gaban sauran takwarorinta na Afurka, an yi duba ne kan yadda suka banbanta wajen samar da abubuwan da ake bukata a fannin na ilimi da kiyasin yaran da suke zuwa makaranta, Seychelles ita ke biye mata baya inda ta zama ta 68 Gabon (112) da Botswana (114) da Equatorial Guinea (126) da Najeriya (150).
Mun lura cewa sanya Najeriya a matsayin ta farko a jerin wadancan sunaye a Facebook bata cikin jadawali na kasa da kasa, kuma ita kasar Seychelles wacce ke zama gaba-gaba a bayanan manyan cibiyoyi, a shafin na Facebook an nuna ta a matsayi na biyar.
Haka kuma ita ma Afurka ta Kudu wacce ke a gaba-gaba idan ana maganar ilimi babu ita a jerin sunayen na Facebook, wannan ya kara sanya shakku kan da’awar.
A Karshe
Wallafar da aka yi a shafin Facebook da ake cewa Najeriya ita ce ta farko “kasar da ta fi kowace a fannin ilimi a nahiyar Afurka” karya ce, kungiyoyi na kasa da kasa sun rika nuna Seychelles a matsayin kasar da ke a gaba-gaba idan ana maganar ilimi a tsakanin takwarorinta na Afurka




