African LanguagesHausa

Karya ne! Ruwan AC ba shi da amfani; zai iya wa batura lahani sabanin yadda ake da’awa

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Shafin labarai na tsegumi Gistlover cikin wani labarin da ya shuhura a shafinsu na Facebook na da’awar cewa ruwan AC daidai ya ke da ruwan da aka tsabtace dan haka ana iya amfani da shi a batura da ma wasu daga cikin ayyukan da ake yi a dakunan bincike.

Karya ne! Ruwan AC ba shi da amfani; zai iya wa batura lahani sabanin yadda ake da'awa

Hukunci: Karya. DUBAWA ta gano cewa ruwan AC ba daidai ya ke da tsabtataccen ruwan sha ba dan haka ba za’a iya amfani da shi a batura ko ma bincike na kimiya ba.

Cikakken bayani

Kwannan nan wata da’awa ta fito ta na cewa ruwan da ke fitowa daga AC na da amfani, kuma labarin na ta yawo kusan ko’ina Najeriya musamman a shafukan sada zumunta. A cewar da’awar, ruwan da ke fitowa daga AC tsabtatacce ne kuma ana iya amfani da shi  wajen gudanar da wasu ayyuka ko kuma a saida shi dan samun ruba. Wannan da’awar ta bulla a shafun TikTok, Facebook, da Nigeriannewsdirect.com.

Sanannen shafin tsegumi na Najeriya  Gistlover ya yi bayani makamancin wannan a shafin shi na Facebiik ranar 23 ga watan Yunin 2025  inda ya ce  ruwan da ke fitowa daga AC na da amfani sosai ya kuma yi kira ga jama’a cewa a maimakon zubar da shi su rika saidawa.

A cewar bayanin, “Idan har kuna zubar da ruwan AC, lallai asara ku ke yi na miliyoyin nera. Ruwa daga AC wanda ma akan kira tsabtataccen ruwa, ana amfani da shi cikin batura da ma bincike irin na kimiya. A yanzu haka ana iyza samun lita biyar kan nera duba biyar, gara ku fara sayar da ruwan yau.”

Daga wannan lokacin zuwa 17 ga watan Yuni, mutane sama da 2,000 sun yi ma’amala da bayanin wasu 846 sun yi tsokaci, yayin 92 suka sake yada labarin. Masu amfani da shafin da dama sun ja hankalin abokansu, sun bayyana sha’awarsu kan batun sun kuma tattauna yiwuwar karbar ruwan dan su saida.

Agorsor Godwin Kojo Dzadzagonor ya yi tsokaci kamar haka, “Jude Boison, yi riba a kai maimakon amfani da shi a bayi.” 

Godfrey Daniel shi kuma da’awa ya yi yana cewa, “Abun mamaki ne wai ‘yan Najeriya ba su san cewa ruwan AC na dauke da sinadarin nitrogen mai yawan gaske ba. Lita 50 na ruwan AC na iya kai wa ₦ 540,000. IAna neman shi sosai.”

Preccy Precious Page ta kara da cewa, “wancan lokacin da mu ke darasin chemistry a dakin gwaji, ruwan AC muka rika amfani da shi kuma daga karshe sakamakon ya kan fito daidai yadda ua kamata.”

Sai dai akwai wadanda suka bayyana shakkunsu. Akeem Babatunde Daramola cewa ya yi, “ba daidai ya ke da irin ruwan da ake sanyawa a batura ba. NI da nake aiki a ofishin da ke da AC 27 wadanda ke aiki kullun ba kakkautawa ne ku ke so ku yi wa karya.”

Wannan da’awar wadda ta yi ta yawo sosai a shafin Facebook, Whatsapp da sauran dandalolin da ke kan yanar gizo-gizo, ta janyo damuwa, domin za ta iya yaudarar jama’a su yi amfani da shi a hanyoyin da bai kamata ba.

Abin da ya sa DUBAWA tantance labarin ke nan.

Tantancewa

DUBAWA ta gano cewa duk da shi ke ruwan AC din kan samu ne bayan kankara ya narke, tsarin da ya ke kama da salon da ake bi wajen tacewa ko tsabtace ruwa, ba za’a iya cewa ya bi tsari ko kuma ma ya yi amfani da irin sinadaran da ake bukata wajen samun ruwan da ake bukata ba. 

Tsabtataccen ruwa kan samu ne bayan an tafasa ruwa an cire tururin da ya ke yi, wanda ke tabbatar da cewa an narkar da duk sunadaran da ba’a bukata an kuma kashe kwayoyin cuta da sauran abubuwa masu lahani. Yayin da  shi kuma ruwan AC ya kan samu ne a lokacin da iska ya zama ruwa ya like kan wayoyin da ke cikin AC. Yayin da iskan ke shiga cikin AC din  ya na iya gurbacewa daga kura, tsatsa, da roba, da sauran kananan kwayoyi ko halittu wadanda za su hana iya amfani da shi wajen gudanar da bincike irin na kimiyya.

Karin bincike ya nuna cewa yawancin lokuta ruwan AC na dauke da kwayoyin cuta a cike har da masu lahani wadanda ake kira  Legionella da Mycobacterium a turance, wadanda kuma suka fi rayuwa a wuraren da ke AC ko kuma cikin shi saboda danshi. Wadannan abubuwan yawanci su ne ke sanyawa ba za’a iya amfani da ruwan a cikin batura ko ma bincike ba, musamman ma a abubuwan da ke bukatar mayar da hankali kan tsabta.

Kwararru sun sa baki

Adegoke Borisade, wani mai bincike a Cibiyar Bincike da Cigaban Makamashi da ke jami’ar Obafemi Awolowo, can a Ile-Ife ya yi bayanin cewa ana samun tsabtataccen ruwan sha ne ta dafa shi sosai da tacewa ta yadda za’a tabbatar cewa babu kwayoyin cuta dan tabbatar da kariya. Ya kuma yi gargadi kan amfani da ruwan AC inda ya ce ba’a tace ba kuma ma ba shi da irin sinadaran da ake bukata.

“Ruwan AC na iya bayyana kamar yana da tsabta, sai dai yawancin lokuta a cike ya ke da kura, da kwayoyin karafa da kwayoyin cutar da ya kwaso daga cikin AC din. Amfani da shi na iya kasancewa da lahani wajen gudanar da bincike sa’annan ya na iya lalata abubuwan da ake amfani da su ya kuma ma kasance hatsari ga lafiyar jama’a,” ya yi gargadi.

Adegoke ya kara da cewa tsabtataccen ruwan da ake amfani da shi wajen bincike ya kan cimma tanadin kasa da kasa abun da ruwan AC ba ya yi “

Adebayo Abolore, Injiniya tare da Florex Apex Nigeria Limited-  wani kamfanin Solar da ke Ibadan ya yi gargadin amfani da ruwan cikin batura. Shi ma ya ce tsabtataccen ruwan kadai ya kamata a yi amfani da shi domin shi ne ke da irin sinadaran da ake bukata ya kuma fi dacewa da baturan yadda ba zai yi sanadin wani lahani ba.

A karshe

Da’awar cewa ana iya amfani da ruwan AC a kan batura ko ma bincike irin na kimiyya ba daidai ba ne. Kwararru da binciken DUBAWA duk sun tabbatar mana cewa ruwan AC na dauke da dauda da kwayoyin cuta wadanda suka keta dokokin kasa da kasa. Dan haka suna da lahanin gaske kuma yada irin wannan labarin yaudara ne domin ya na da lahanin gaske.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »