Getting your Trinity Audio player ready...
|
TSAKURE
Ci gaban kowace al’umma yana tafiya ne tare da ire-iren tsare-tsare da shirye-shiryen wannan al’umma dangane da yadda take tafiyar da harkokinta waxanda suka shafi al’adunta da aƙidunta musamman waɗanda suke da alaƙa da tarbiyya. Dukkan al’ummar da ‘ya’yanta ba su da kyakkyawar tarbiyya yana da matuƙar wuya ta zauna lafiya. Idan kuwa babu zama lafiya babu yadda za a yi wannan al’umma ta sami bunƙasar da za ta taimaka mata ta sami dauwamammen zaman lafiya da qaruwar arziki yadda kowa zai yalwata ya sami ci gaba. Domin ba da tawa gudummuwa wajen samar da mafita ga halin da al’ummar Hausawa suke ciki a wannan zamani, ya sa a wannan takarda za a yi bayani a kan irin kyakkyawar tarbiyyar Hausawa ta gargajiya kafin su sami cuxanya da wasu baƙin al’umma, waɗanda koyi da al’adunsu ne ya kai al’ummar Hausawa shiga cikin wannan mummunan hali da muke ciki a yau. Domin kuwa, matuƙar aka waiwayi kyawawan al’adun Hausawa musamman waɗanda suka shafi tarbiyya aka yi masu ‘yan gyare-gyare, za su taimaka a sami ingantaccen shugabanci ba a ƙasar Hausa ba kawai, a’a, har ma da Tarayyar Nijeriya baki ɗaya. Wannan ne zai sa Tarayyar Nijeriya da dukkan al’ummomin da suke cikinta su sami dauwamammen zaman lafiya, a kuma sami bunƙasa, matasa su sami abubuwan yi yadda arzikin ƙasa zai ƙara yalwata.
Gabatarwa
Hausawa na cewa, “zama lafiya ya fi zama ɗan sarki”, har abada ba za a sami zama lafiya da kwanciyar hankali ba idan babu tarbiyya mai kyau. Kyakkyawar tarbiyya take sa a sami ingantaccen shugabanci da zaman lafiya da ƙaruwar arziki ga kowace al’umma. Hakika, idan muka dubi wannan bayani da ya gabata muka kuma waiwayi irin zaman da Hausawa suka yi kafin shigowar wannan zamani, watau lokacin da suke yin cikakken riƙo da kyakkyawar tarbiyyarsu ta gargajiya, wadda ta yi koyi da yin biyayya ga dokokin addini, da bin gaskiya da riƙon amana, da sadar da zumunci da taimakon juna, da yin biyayya ga tsarin shugabanci irin na Hausawa, da riƙe sana’o’in gargajiya, da nuna juriya da gwada jarunta, da nuna kunya da kara, da kuma kyakkyawar mu’amala a tsakaninsu, sannan kuma idan muka kwatanta su da halin da al’ummar Hausawa suke a yau, lokacin da waɗannan kyawawa al’adu suka ɓace, ma iya yanke hukunci da cewa, watsi da kyakkyawar tarbiyyar Hausawa ne, ya kai mu shiga cikin wannan hali na rashin tabbas. Watau halin da ƙarami ba ya yi wa na gaba da shi biyayya, don idan wata rashin jituwa ta shiga tsakaninsu, ƙarami ba ya jin kunyar cin mutunci wanda ya girme shi ko da kuwa ya kai tsarar mahaifinsa. Iyaye sun koma su ne ‘ya’ya, don kuwa ‘ya’yan suna juya su yadda suke so. Zaman banza da yaudara da cuta da yin banga ga ‘yan siyasa marasa kishin ƙasa sun zama abubuwan yi a wannan zamani. Haka kuma, rashin gaskiya da cin amana sun zama ruwan dare, kuma ba a ɗauke su wani abin kunya ba. Shiga cikin irin wannan hali ga dukkan al’ummar da ta san ciwon kanta, al’amura ne waɗanda suke bukatar dubawa da idon basira don samun mafita. Matuƙar ana son a sami mafita dole ne a koma wa tarbiyyar Hausawa ta gargajiya. Dangane da haka, wannan takarda za ta yi bayani ne kan wasu daga cikin hanyoyin tarbiyyar Hausawa na gargajiya don kawo shawarwarin da za su taimaka a sami mafita cikin wannan hali da ƙasar Hausa da Tarayyar Nijeriya suke ciki na rashin ingantaccen shugabanci a wannan zamani.
2.0 Waiwaye a kan Tsarin Tarbiyyar Hausawa a Jiya
Tun lokaci mai tsawo da ya gabata kafin shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa al’ummar Hausawa suke gudanar rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya. Wannan kuwa ya faru ne saboda suna da kyakkyawan tsarin tarbiyya wanda ya ba kowa damarsa yadda wani ba ya shiga cikin harkar da ba ta shi ba. Wannan dalili ne ya sa ko da addinin Musulunci ya shigo ba a fuskanci wasu manyan matsaloli ba dangane da halin zamantakewar wannan al’umma. Matuƙar ana son kwalliya ta biya kuɗin sabulu, yadda za a sami ingantaccen shugabanci a wannan zamani, na ga ya dace a waiwayi tsarin tarbiyyar Hausawa ta gargajiya.
2.1 Biyayya ga Dokokin Addini
Hanyar bauta wa wani abu wanda mutum yake tsammanin zai biya masa buƙatun rayuwa na yau da kullum shi ne addini. Addinin farko na mutanen ƙasar Hausa shi ne addinin gargajiya watau bautar iskoki. Addinin gargajiya ya faru ne ta bin wasu hanyoyi da mutane suka ƙirƙiro wa kansu ta bautar waɗansu abubuwa don cimma biyan buƙatunsu. Irin wannan hanyar bauta ta daɗe ƙwarai a dukkan sassan duniya ba ƙasar Hausa kaɗai ba. Mutanen da suka fara zama a duniya ne suka ƙirƙiro ta, daga nan abin ya zama al’ada ga sauran ƙabilun da suke biye da su har ya zo ga Hausawa. Irin wannan addini ya sami rauni sakamakon zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa da kuma karɓar shi ga al’ummar Hausawa. Amma duk da haka ba a bar yin wasu abubuwan da suka danganci addinin gargajiya ba, don kuwa za a ga yakan yi naso a wasu al’amuran rayuwar Hausawa na yau da kullum.
Ta wannan fuska idan muka yi waiwaye muka duba yadda al’ummar Hausawa suka gudanar da addininsu na gargajiya, za a ga ba suna sassaƙa wani gunki ne su riqa bauta masa ba, a’a, mafi yawancin bautar su ta hanyar tsafi ce. Bauta ta hanyar tsafi tana nufin bauta wa wani aljani da aka ɗauka yana zaune a wani wuri na daban. Ire-iren waɗannan aljannu an ɗauka suna zaune ne a wata kwankwamar dutse, ko wata sarƙaƙƙiya, ko wurin wata tsohuwar itaciya, misali kuka ko tsamiya ko marke da sauransu. Ire-iren waxannan wuraren tsafi a ƙasar Hausa sun haɗa da wurin bautar aljani Tsumburbura wanda aka ɗauka ya zauna a Dutsin Dala ta Kano da Kaina-Fara-Arnan-Birchi masu bautar aljani Ɗantalle da suka ce yana zaune a cikin Dutsin Birchi ta Ƙaramar Hukumar Kurfi a Jihar Katsina. Arnan Kwatarkwashi kuma suna bauta wa Maiki wanda suka ɗauka yana zaune a cikin Dutsin Kwatarkwashi ta Jihar Zamfara. Haka kuma, a duwatsun Kufena ta Zariya cikin Jihar Kaduna, mazaunan farko na wannan wuri sun ɗauka a cikin waɗannan duwatsu, akwai wasu aljannu da suke zaune a wurin waɗanda suke biya masu buƙatunsu. Akwai kuma arnan Suna ta ƙasar Kwatarkwashi da kuma wasu arnan a wasu sassa na ƙasar Katsina da suke bautar aljani Magiro wanda suka ɗauka yana zaune a wurin tsamiya mai sarƙaƙƙiya da duhuwa wadda ba mai iya zuwa wurin da take sai masu yin bautar wannan tsafi.
Bayan tsafi wani nau’i na addinin gargajiya na Hausawa shi ne bori, watau bautar iskoki ko mutanen ɓoye. A wurin Hausawa bori tsohuwar al’ada ce, domin kuwa an daɗe ana yin ta a matsayin addini, kuma har yanzu da addinin Musulunci ya zama jiki ga Hausawa ba a bar yin ta ba. Hausawa sun ɗauka ban da ma mutane, wannan duniya da muke ciki tana ɗauke da wasu ɓoyayyun halittu masu ɗabi’u irin na mutane. Wannan dalili ne ya sa suke kiran su mutanen ɓoye. A saboda wasu dalilai ‘yan bori sun rarraba iskoki zuwa kashi biyu; baƙaƙen iskoki da fararen iskoki.
Baƙaƙen iskoki su maƙetata ne masu neman mutum da sharri. Idan ana son a yi wa mutum maganin da zai mutu, ko ya haukace, ko ya lalace, ko wani bala’i ya faɗa masa ana neman taimakon yin haka daga baƙaƙen iskoki. Ire-iren su sun haɗa da Uwar-gona da Baƙo da Kure da Gajimare da Danko da Duna da Kakare. Su baƙaƙen iskoki ba a neman su sai ta ɓaci don su ƙara ɓata al’amari.
Fararen iskoki kuwa na kirki ne kuma suna taimakon mutane ta hanyar bayar da dukiya da kuma sarauta. Bugu da ƙari kuma, suna ba mutane maganin cuce-cuce ciki har da na maganin baƙaƙen iskoki. Daga cikin fararen iskoki akwai Sarkin Makaɗa Dafau da Sarkin Aljan da Sarkin Rafi da Uban Dawaki da Inna (Bafulatana) da Ɗangaladima da Malam Alhaji.
Waɗannan iskoki baƙaƙe da farare,’yan bori sun bayyana, wasunsu na zama tare da mutane, su kuma yi abota da su. Mutanen na hawa borinsu sai su riƙa gaya masu magungunan wasu cuce-cuce. Haka kuma, suna gaya masu labarin gaibi, watau abubuwan da za su faru gobe ko baƙi da sauransu. Ire iren waɗannan mutane da suke yin hulɗa da aljannu ne Hausawa suke kira ‘yan bori. Dukkan wanda yake son zama ɗan bori dole sai an yi masa girka. Ana yin girka don a shirya dukkan iskokin da suke kan mutum don ya zauna lafiya da su. Ana kuma yin girka don yin magani ga marar lafiya wanda iskoki suke kansa kuma suka hana shi zama lafiya.
Duk da kasancewar a al’adar Hausawa ba a yi wa budurwa aure sai ta kai shekara goma sha takwas ko fiye da haka, watau an tabbatar da ta balaga, an yarda idan saurayi yana neman aure budurwa ya je tsarince wurinta, watau ya kwana gidansu a ɗaki ɗaya da ita bisa shimfiɗa ɗaya, ko ita ta je gidan saurayin nata su kwana tare, amma duk da haka al’ada ba ta yarda ya ko taɓa jikinta ba, balle ma har ya aikata wani abu da ita ba, watau ya yi lalata (zina) da ita ba. Idan ya kuskura ya tava ta ko ya yi ƙoƙarin yin lalata da ita, to ya shiga uku ya lalace, don kuwa duk wannan yanki nasu ba zai ƙara samun budurwar da za ta yarda da shi ba. Wannan dalili ne zai kai shi ga rasa matar da zai aura, daga ƙarshe dole ya gudu ya bar ƙasar baki ɗayanta yadda ba a za a sake jin labarinsa ba. Ire-iren waɗannan mutane ne za a tarar sun je wasu garuruwa inda ba wanda ya san su a garin. A wasu lokuta har su mutu ba a sanin daga inda suka zo wannan ƙasa. Wannan hukunci ga namiji ke nan.
Ita budurwa kuwa idan ta kuskura ta yi lalata (zina) tana fuskantar hukunci mai tsananin wanda a wani lokaci yana iya zama dalilin mutuwar ta. Wannan hukunci ya danganta da abin bautar gidansu. Da farko abin da ake fara yi shi ne, za a kira ta a tambaye ta, ko ta san xa namiji? Idan ta amsa da cewa ta san ɗa namiji, shi ke nan ta jawo wa kanta da dukkan zuri’arta abin kunya, sai kuma a rage yawan dukiyar aurenta. Idan kuwa ta amsa da cewa ba ta san ɗa namiji ba, sai aka iyayenta su bi hanyar da suka gada ta tsafi don gane gaskiyar abin da ta faɗa. Ga misalin ire-iren yadda ake gane budurwa ta san ɗa namiji ko ba ta san shi ba kafin a yi mata aure a al’adar Maguzawa da kuma irin hukunci da suke yanke wa ‘ya’yansu mata waɗanda ba su kai budurcinsu ba dangane da abubuwan da suke bauta wa na gargajiya.
2.1.1 Masu Bautar Aljanin Magiro
Maguzawan da suke bautar wannan tsafi sun ɗauka aljanin yana zaune a dutsin Kwatarkwashi. A Kwatarkwashi arnan Suna ne suke bautar wannan gunki, haka kuma akwai wasu arnan a wasu sassan ƙasar Katsina da suke bautar wannan tsafi. A ƙasar Katsina a ƙauyukan Kunkunna da Makanwaci da Tamna da Maikada da Daulai cikin ƙaramar Hukumar Safana. Haka kuma, a ƙauyukan Barza da Gerecen-Arna da Aidun Gadaje cikin ƙaramar Hukumar Ɗanmusa akwai arnan da suke yin irin wannan bauta ta tsafin Magiro. Domin yin wannan bauta, suna samun bishiyar tsamiya ko marken da yake da duhuwa da sarƙaƙƙiya. Waɗannan arna na samun yashi mai laushi da kyawo su zuba a gindin wannan tsamiya ko marke, sai kuma su kawo baƙin zane da baƙin rawani da baƙar hula da baƙar riga da baƙin wando dukkansu na saƙi sai a ɗaɗɗaura su wurin wannan tsamiya. Daga nan, sai a sami tulunan giya biyu a ajiye gindin wannan tsamiya ko marke, sai kuma a yanka baƙin bunsuru a gindin tsamiyar. Dukkan wanda ya ga waɗannan alamomi zai fahimci akwai wani abu da yake faruwa a wurin, kuma ana gargaɗin mutane da su yi nesa da wurin, don ba mai zuwa wurin sai wanda yake kula da tsafin ko wani daga cikin zuri’arsa. Ana tsorata mutane da cewar, dukkan wanda ya je wurin, idan ba waɗannan mutane ba, dukkan abin da ya same shi ya kuka da kansa.
Mabiya tsafin Magiro sun ɗauka wannan aljani na kare su daga dukkan bala’o’i, kuma yana biya masu dukkan buƙatun da suka nema daga gare shi. Haka kuma, suna ikirarin cewa, dukkan wanda yake da shakka kan gaskiyar tsafinsu suna iya nuna masa ta hanyar kiran aljanin. Akwai dalilan da kan sa a kira aljanin Magiro waɗanda suka haɗa da idan ana biki gidan mabiyansa, yana zuwa don ya bayyana wa jama’a da mahaifan wannan yarinya da za a yi wa aure ba ta yi lalata (zina) ba a lokacin da take budurwa. Hanyar da ake gane haka shi ne, a ranar da za a ɗaura wa yarinyar aure, tun da asuba sai mahaifanta su kira ta, sai a ajiye turmin daka a tsakiyar gidansu ta hau kansa ta zauna. A wannan lokaci ne za a kira wannan aljani na Magiro. Da ya iso gidan, sai ya yi ta zagaya gidan kamar iskar guguwa, ya kuma yi ta yin ruri kamar bajimin sa. Idan wannan yarinya ta taɓa yin lalata, sai ya kashe ta. Idan kuwa ba ta taɓa yi ba, sai ya yi ta zagaye-zagayensa har ya gama ba abin da zai sami wannan yarinya.
Wata hanya da mabiya wannan tsafi suke gane budurwa ba ta yi lalata ba ita ce, idan ya rage saura kwana ɗaya a yi bikin, sai a sami baƙin ɗan’akuya da jan zakara da goran giya a kai su wurin da ake yin tsafin Magiro. Idan gari ya waye, sai a je wurin a duba. Idan aka tarar ɗan akuyan da zakaran sun mutu, kuma goran giya babu kome cikinsa, alama ce wadda take bayyana cewa wannan yarinya ba ta yi lalata ba, Magiro ya yi maraba da ita ke nan, sai iyayenta su yi ta murna saboda ɗiyarsu ta kai budurcinta. Daga nan, sai a ɗauki wannan yarinya a kai ta ɗakin mahaifiyarta inda za a yi sauran al’adun da suka dace a yi mata don kai ta gidan miji. Idan kuwa aka tarar ɗan akuyan da zakaran suna raye, kuma ba a taɓa goran giya ba, alama ce wadda take bayyana wannan yarinya ba ta kai budurcinta ba, Magiro bai yi maraba da ita ba ke nan, sai ya kashe ta. (Ibrahim, 1982: 172).
2.1.2 Maguzawa Masu Bautar Tsafin Uwar-Gona
Su kuma Maguzuwa masu bautar tsafin Uwar-Gona a lokacin da ‘yarsu budurwa za ta yi aure, hanyar da suke bi don su gane cewa wannan yarinya wadda za a yi wa aure ta yi lalata ko ba ta yi lalata ba ita ce, sai a sa waɗanda za su auri wannan yarinya su kawo ɗan akuya. Daga nan sai a samo turamen daka uku, a kuma samo mutane uku, sai a jera turame biyu kusa da kusa, sai a sanya turmi na cikon ukun a gefen waɗannan turame biyu. Daga nan, sai mutane biyu daga cikin mutanen nan uku su hau kan turmi ɗaya – ɗaya, shi kuma na cikon uku sai ya hau kan ɗaya turmin. Sai a kawo wannan ɗan akuya a ba waɗannan mutane biyu waɗanda suke kan turame biyu da suke kusa – kusa. Ɗaya ya riƙe ƙafafun gaba, shi kuma ɗayan ya riƙe ƙafafun gaba. Shi kuma wanda yake kan ɗayan turmi na cikon uku, sai a kawo masa wani takobi na tsafi wanda aka ajiye ba a amfani da shi sai irin wannan rana. Lokaci da ya amshi wannan takobi, sai ya sari wannan ɗan akuya da shi. Idan wannan yarinya ba ta san ɗa namiji ba, sara ɗaya zai yi wa wannan ɗan akuya ya raba shu biyu. Shi ke nan sai iyaye da abokan arziki su yi ta murna, ‘yarsu ta kai budurcinta. Idan kuwa wannan yarinya ta san ɗa namiji ko sara nawa ya yi wa wannan ɗan akuya ba zai yi masa ko ƙwarzane ba balle ya raba shi biyu. Daga nan, nan take wannan yarinya za ta faɗi ta mutu.
2.1.3 Maguzawa Masu Bautar Tsafin Kurmawa
Maguzawan da suke bautar tsafin Kurmawa waɗanda ake samu a ƙasar Katsina da Kano da Zamfara, a lokacin da za su yi wa ɗiyarsu budurwa aure, idan an tambaye ta ko ta san namiji? Idan ta amsa ba ta san ɗa namiji ba, sai a samo ɗan kwikwiyo da rago a yanka su, a feɗe su, a kuma yayyanka namansu a haɗe su wuri ɗaya a soya. Bayan ya naman ya soya, sai a kira wannan yarinya a ba ta naman ta ci. Idan ba ta san ɗa namiji ba, duk lokacin da za ta ɗauko tsokar naman, sai ta ɗauko ta ragon, za ta ci har ta ƙoshi ba abin da zai same ta. Idan kuwa ta san ɗa namiji ba za ta bambance naman kare da na ragon ba, sai ta haɗa su ta yi ta ci har sai ta qoshi. Daga nan sai ta faɗi ta mutu nan take. Idan kuwa a lokacin da aka tambaye ta, ko ta san ɗa namiji? Ta amsa da cewa ta sani, sai a ba ta wannan kwikwiyo ta riƙa yawo da shi, don bayyana wa jama’a ba ta kai buturcinta ba, sannan kuma a rage yawan dukiyar aurenta. Wannan dalili ne, ya sa Hausawa yin maganar hikima da suke cewa, ‘laifi kwikwiyo ne mai shi yake bi’.
2.1.4 Maguzawa Masu Bautar Tsafin Maƙera
Su kuwa Maguzawan da suke bautar tsafin Maƙera waɗanda su ma ana samun a ƙasar Katsina da Kano da Zamfara, a lokacin da za su yi wa ‘yarsu budurwa aure, idan ya rage saura kwana ɗaya a ɗaura mata aure, sai a kira ta a tambaye ta ko ta san ɗa namiji? Idan ta amsa da cewa ba ta san ɗa namiji ba, sai a samo jan zakara. Daga nan, sai a ɗebo jar dawa a sami mata uku ko huɗu majiya ƙarfi, sai a kamo wannan zakara a sanya shi ƙarqashin turmin da ake daka, a zuba wannan jar dawa cikin wannan turmi, sai waɗannan mata su yi ta dakan wannan dawa har sai sun mayar da ita gari. Lokacin da suke dakan wannan dawa wannan zakara na ƙarƙashin turmin da suke dakan. Idan wannan yarinya ba ta san ɗa namiji ba, duk tsawon lokacin da aka ɗauka ana dakan wannan dawa ba abin da zai sami zakaran. Hasali ma, washegari ranar da za a ɗaura auren wannan yarinya, zakaran ne zai fara cara da asuba don tayar da mutanen wannan gida daga barci. Idan kuwa wannan yarinya ta san ɗa namiji, da safe idan aka ɗaga turmin da aka sanya zakaran za a tarar ya rududduge ya saje da ƙasa. Ana ganin haka, ita kuma wannan yarinya tana faɗuwa nan take ta mutu (Ibrahim, 1982: 173 – 175) .

2.2 Biyayya ga Tsarin Shugabancin Gargajiya na Hausawa
Shugabanci yana nufin yi wa al’umma jagora a halin zamantakewarsu na yau da kullum. A nan duk wanda aka ba ragamar tafiyar da mulkin al’umma, nauyi ya hau kansa na tsare lafiyarsu da dukiyarsu da mutuncinsu. Su kuma waɗanda ake shugabanta haƙƙinsu ne su ba wanda yake shugabancinsu haɗin kai, da bin ummurnin sa ta hanyar bin doka da oda, da yi masa biyayya don ya sami sauƙin tafiyar da mulkinsu cikin kwanciyar hankali.
A ƙasar Hausa shugabanci yana farawa daga gida, a kowane gida wanda yake ƙunshe da mutanen da suka kai biyu ko waɗanda suka wuce haka, akwai maigida wanda nauyin dukkan mutanen wannan gida yana kansa. Shi ne yake shugabancin harkokin rayuwar yau da kullum na mutanen da suke wannan gida. A saboda haka dukkan mutanen wannan gida waɗanda suka haɗa da matansa da ‘ya’yansa da ƙannensa da jikokinsa da barorinsa duk da matansu da ‘yan cin arziki suna bin ummurninsa. Haka kuma, shi ne yake ɗaukar nauyin yi masu dukkan abubuwan da suka shafi sutura da abinci da tsaro da kare mutuncinsu. Idan ire-iren waɗannan gidaje suka yi yawa, sai su kafa unguwa. Daga cikin masu waɗannan gidaje, sai a sami wani mai kwarjini da iya tafiyar da harkokin al’ummarsa a ba shi muƙamin mai’unguwa. Mutanen wannan unguwa ne suke zaɓar sa su kai shi ga dagacinsu wanda shi ne zai amince da shi. Daga nan nauyin tafiyar da harkokin mulkin al’ummar wannan unguwa ya hau kansa. Shi ne kuma zai riƙa wakiltarsu a duk wasu harkoki da kuma yin sasanci a tsakanin talakawan wannan unguwa. Haka kuma, shi zai riƙa tattara kuɗin harajin mutanen wannan unguwa don kai wa dagacinsu (Usman, 1972:176).
Samuwar unguwanni da yawa ke sa a sami dagaci wanda shi yake shugabantar masu unguwanni. Dukkan abubuwan da ke faruwa a waɗannan unguwanni sai an sanar da shi. Haka kuma, duk wani sasanci da ya gagari mai’unguwa, sai ya kai wa dagaci don ya sasanta. Dagaci ne yake wakiltar al’ummominsa waɗanda suke zaune a unguwanni a wasu al’amuran da suka shafi waɗannan unguwanni, kuma shi masu unguwanni suke kai wa kuɗin harajin unguwanninsu don ya kai wa hakimi.
Garuruwan dagatai da yawa suke samar da ƙasar hakimi ko uban ƙasa, wanda shi yake shugabancin dukkan garuruwan dagatai da suke ƙarƙashinsa. Dukkan abubuwan da suke faruwa a garuruwan dagatai sai an sanar da hakimi, kuma shi yake wakiltarsu a wasu ma’amalolin da suka shafi wannan ƙasa tasu. Idan dagatai sun gaza wajen yin sasanci a tsakanin talakawansu, sai su miƙa maganar ga hakimi wanda zai yi iyakar ƙoƙarinsa ya yi sasanci. Bayan dagatai sun kammala tattara kuɗin harajin ƙasashensu, sai su kawo wa hakimi daga nan sai ya kai wa sarki.Waɗannan ƙasashe na hakimai su ne suke taruwa su kafa ƙasar sarki wanda shi ne wuƙa da nama a duk harkokin da ke faruwa a wannan masarauta. Dukkan mutanen da suke zaune a wannan ƙasa na ƙarqashin ikonsa, kuma hakimai na sanar da shi dukkan abubuwan da suke faruwa a ƙasashensu. Idan hakimai sun gaza wajen yin sasanci tsakanin talakawansu, sai su kai maganar ga sarki, wanda ta hanyar shawartar ‘yan majalisarsa zai yanke hukunci na ƙarshe ko da daɗi ko ba daɗi.Wanda hukuncin bai yi wa daɗi ba, dole ya yi haƙuri (wannan dalilin ne ya sa ake yi wa sarakunan gargajiya na ƙasar Hausa laƙabi da sunan wuƙar-yanka). Idan hakimai suka kammala tattara kuɗin haraji na ƙasashensu, sai su kai wa sarki, wanda zai sa a saka su cikin Baitulmali don gudanar da harkokin mulki na wannan masarauta (Usman, 1972:176).
A kowace masarauta akwai ‘yan majalisar wannan sarki, su ne suke taimaka wa wannan sarki da shawarwarin aiwatar da mulkin wannan ƙasa cikin nasara da adalci. Waɗannan ‘yan majalisa sun haɗa da waziri wanda shi ne babban mai taimaka wa sarki, kuma a mafi yawancin lokaci shi yake wakiltarsa a lokacin da ya yi wata tafiya wajen masarautarsa. Bayansa, akwai alƙali da magatakarda da ma’aji ko ajiya da sarkin fada da shamaki da shantali da galadima da sarkin gida da sauransu da dama.
Bayan waɗannan sarautu, akwai waɗanda ake ba masu yin sana’o’in gargajiya. Kowace sana’a tana da wanda ake ba jagorancin masu yin wannan don ya yi jagoranci da sasanci a tsakanin masu yin wannan sana’a da kuma tafiyar da sana’ar bisa ingantaccen tsari. Ire-iren waɗannan sarautu sun haɗa da sarkin noma ga manoma da sarkin maƙera ga masu sana’ar ƙira da sarkin aska ga wanzamai da sarkin makaɗa ga makaɗa da sanƙira ko sarkin roƙo ga maroƙa da sarkin fawa ga mafauta da sauransu da dama (Adamu,1978:5).
Dukkan waɗannan sarautu da aka yi bayani a kansu tun daga mai unguwa zuwa ga sarki da ‘yan majalisarsa da masu riƙe da sarautun sana’o’in gargajiya, an tsara su ne bisa tafarkin gado.Watau idan wanda yake riƙe da sarauta ya rasu ko aka tuɓe shi, a mafi yawancin lokaci ana zaɓar wani daga cikin ‘ya’yansa ko ɗan’uwansa don ya gaje shi.
Babban ginshiƙin tafiyar da kowane irin mulki shi ne adalci, watau shugaba ya zama adali wajen tafiyar da mulkinsa ba tare da nuna bambanci ba, ya kuma ba kowa haƙƙinsa ba tare da la’akari da nasabarsa, ko muƙaminsa ba. Dukkan ƙasar da take da shugabanni masu yin adalci ga talakawansu, wannan ƙasa za ta zauna lafiya ta kuma sami cigaba da ƙaruwar arziki. Idan muka waiwayi yadda aka riƙa gudanar da mulki a ƙasar Hausa kafin zuwan wannan zamani za a ga cewa, ana gudanar da shi ne bisa adalci, don kuwa akwai zaman lafiya tsakanin al’ummomin wannan ƙasa. Misali, a cikin gida ko unguwa ko cikin gari, manya suna iya yin hukunci idan suka ga na ƙasa na yin rashin daidai ko da kuwa ba su da wata dangantaka ko nasaba ta jini. A tunaninsu yaro duka na kowa ne, matuƙar ka ga yana yin wani abu na rashin daidai, idan ba ka tsawata masa ba, to, a al’adar zamantakewa ta Hausawa ba a yi daidai ba, kuma ba za a ɗauki wannan mutum wanda ya san daidai ba. A wancan zamani takan kai matakin idan babban mutum ya tarar ana yin rashin daidai yana iya yin hukunci mai tsanani (ko da kuwa zai kai matsayin duka) ga waɗanda ya tarar suna yin rashin daidai ɗin, ko ya san su, ko bai san su, ko da dangantaka ko babu wata dangantaka tsakaninsu.
2.3 Bin Gaskiya da Riƙon Amana a Al’adar Hausawa
Gaskiya na nufin yin dukkan wani abu wanda zai bayyana zahirin yadda wannan abu yake, watau ba ragi ba ƙari. Riƙon amana kuma na nufin adana wani abu na dukiya ko sirri wanda a lokacin da bukatar shi ta taso a bayar da shi kamar yadda aka bayar. Idan kuma wani sirri ne ba za a sanar da kowa ba, daga kai sai wanda ya sanar da kai. Kafin zuwan wannan zamani an san al’ummar Hausawa da bin gaskiya da riƙon amana ga dukkan al’amuransu na rayuwa. Wannan dalili ne ya sa a wancan zamani kafin shigowar addinin Musulunci al’ummar Maguzawa ba sa faɗin ƙarya komin tsanani ko daɗi. Haka kuma, al’ummar Hausawa mutane ne masu riƙon amana. Abin nufi a nan shi ne, a wancan zamani duk irin halin matsi da tsananin da aka shiga idan ka kawo wani abu wanda ya shafi dukiya ko kuɗi ka ba Bahaushe ajiya ko ka ba shi saƙo ya kai wa wani, duk irin halin da yake ciki ba za ya yi amfani da wannan dukiya ba har sai lokacin da ka bukata ya ɗauko maka. Haka kuma, idan saƙo ne ka ba shi ya kai wa wani, zai kai masa kamar yadda ka ba shi ba tare da ya rage wani abu ba. Idan kuma ka sanar da shi wani sirri, ba za ya gaya wa kowa ba daga kai sai shi. Wannan al’amari ya taimaka matuƙa gaya wajen zaman Hausawa lafiya a wancan zamani. Saboda irin yadda Hausawa suka yarda da bin gaskiya har maganganun hikima suke da su masu yawa waɗanda suke nuna muhimmanci gaskiya kamar haka:
- Komi za ka faɗi, faɗi gaskiya kome taka ja maka ta biya.
- Marar gaskiya ko cikin ruwa yake ya yi jiɓi.
- Gaskiya dokin ƙarfe.
- Ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi.
- Gaskiya nagartar namiji.
- A daɗe ana yi sai gaskiya.
- Gaskiya akurkin ɗunɗu mai wuyar saka hannu.
2.4 Sadar da Zumunci da Taimakon Juna a Al’adar Hausawa
Sadar da zumunci al’amari ne wanda al’ummar Hausawa suke ba matuƙar muhimmanci, don kuwa lokaci bayan lokaci ‘yan’uwa da abokan arziki kan riqa ziyartar juna don gaisawa da ganin halin da suke ciki. Kafin su tafi ziyartar ‘yan’uwa da abokan arziki sukan riƙa wani abu su kai masu, ana yin haka gwargwadon ƙarfin arzikin mutum. Wasu kuma, saboda rashin abin da za su kai ba za ya hana su yin zumuncin ba, suna zuwa wurin ‘yan’uwansu domin su ga halin da suke ciki ba dole sai sun kai masu wani abu ba.
Domin tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum cikin sauƙi, al’ummar Hausawa suna bin tafarkin rayuwa ta cuɗan-in-cuɗe-ka, watau taimakon-kai-da-kai. Ta wannan fuska, idan abin arziki ya sami ɗan’uwa, ko abokin arziki, ko wanda ake zaune tare da shi a wannan ƙauye ko unguwa ko gari, misali aure ko haihuwa, sai duk a taru don taya shi murna. A lokacin bikin, za a yi ta kawo masa gudummuwa wadda wasu kan kawo hatsi ko abinci ko kuɗi ko sutura da sauransu don dai a taimaka wa wannan ɗan’uwa, ko abokin arziki gudanar da wannan hidima ba tare da ya wahala ba. Irin wannan halayya ce a wannan zamani ta haifar da ƙungiyoyin taimaron-kai-da-kai da kuma ƙungiyoyin ajo domin taimaka wa juna.
Haka kuma idan abin baƙin-ciki ya sami wani mutum, misali rashin lafiya, ko mutuwa, ko wata masifa, ‘yan’uwa da abokan arziki da waɗanda ake zaune tare da su, na kusa da na nesa suna ziyartar sa domin yi masa jaje da taya shi jimamin wannan hali da ya shiga na rashin lafiya ko masifa ko rashin ɗan’uwa.
Bayan wannan al’ummar Hausawa na tafiyar da ayyukan gayya don taimakon-kai-da-ka. Ana yin ayyukan gayya wajen yin sababbin ɗakuna da gyara tsofaffi da yin darnin gida da na garka a gonaki da ɗorin ɗan bisan ɗaki da na rumbu. Haka kuma ana yin ayyukan gayya a gonaki don yin sassabe da huɗa da shuka da noma da girbi da ɗaurin amfanin gona da kuma kawo shi gida. A cikin ƙauyuka da garuruwa ana yin ayyukan gayya don gyaran magudanun ruwa da mashayar ruwa ta mutane da ta dabbobi da kuma gyaran hanyoyin da ake bi don kai amfanin gona gida da kasuwanni (Sallau, 2010: 5-6).
2.5 Riƙo da Sana’o’in Gargajiya na Hausawa
Kafin zuwan wannan zamani al’ummar Hausawa mutane ne waɗanda suka riƙe sana’o’insu na gargajiya da suka haɗa da noma da kiwo da fatauci da dukanci da ƙira da jima da saƙa da sassaƙa da wanzanci da sauransu. Mata ma ba a bar su baya ba, don kuwa sun riqe sana’o’insu da matuƙar daraja irin su kaɗi da dakau da kitso da sauransu. Riƙo da waɗannan sana’o’i ya taimaka al’ummar Hausawa a wancan zamani sun zauna lafiya ba tare da fuskantar matsalolin da a yau shugabannin wannan zamani suka gaza wajen warware su, musamman rashin ayyukan yi ga matasa. A ra’ayina akwai ayyukan yi ga dukkan mazauna ƙasar Hausa ‘yan gida da baƙi. Matsalar ita ce, kowa ya mayar da hankalinsa wajen aikin gwamnati ko na kamfanoni don a waɗannan wurare ne za a sami kuɗi ba tare da an yi wata wahala ba. Matuƙar an koma ma tarbiyyar riƙe sana’o’in gargajiya na Hausawa za a warware wannan matsala.
2.6 Kara da Alkunya a Al’adar Hausawa
A al’adar Hausawa ta gargajiya ana ba kara da alkunya matuƙar muhimmanci saboda kasancewarsu wasu al’amura da ake bambanta mutumen kirki da mutumen banza. Ta wannan fuska, don nuna kara, al’ummar Hausawa suna girmama dukkan wanda ya fi su shekaru ko da kuwa ba su da wata dangantaka ta jini. Misali, dukkan wanda ya kai tsarar mahaifi ba a kiran sunansa, sai da a ce masa “baba”. Haka kuma, dukkan wanda ya fi ka shekaru, ba a faɗin sunansa sai dai a ce masa “yaya”. Su ma mata, suna da irin wannan al’ada, don kuwa a lokacin da ya gabata, mace ba ta faɗin sunan mijinta na fari, ko ɗanta na fari. Duk ana yin waɗannan abubuwa don nuna kara.
Ta fuskar alkunya kuma, akwai abubuwa masu yawa waɗanda al’ummar Hausawa da suka gabata suka ƙyamata don kar a danganta su da marasa kunya. Misali, manyan mutane ba sa yin maganganun banza da na batsa wurin da yara suke. Haka su ma mata, akwai abubuwa masu tarin yawa waɗanda ba sa aikatawa don gudun jin kunya, kamar ci abinci rariya da sauransu.
3.1 Matsayin Tarbiyyar Hausawa a yau
Idan muka dubi tarbiyyar Hausawa a yau kuma muka kwatanta ta da tarbiyyar Hausa ta gargajiya, watau kafin shigowar wannan zamani, za a ga akwai babban sauyi, wanda wannan sauyi ne ya kai mu shiga cikin halin da muke ciki a yanzu. Idan za mu ɗauki waɗannan hanyoyin tarbiyya na gargajiya da kuma irin yadda zuwan addinin Musulunci ya ƙara masu ƙarfin gwiwa, za a ga cewa, a yau watsi da su ne ya kai ƙasar Hausa da Tarayyar Nijeriya shiga halin da muke ciki na rashin kyakkyawan shugabanci da ingantacciyyar al’umma. Misali, idan muka ɗauki biyayya ga dokokin addini, wanda a wannan zamani mafi rinjaye na al’ummar Hausawa sun karɓi addinin Musulunci, za a ga cewa, a yau biyayya ga dokokin addinin Musulunci a baka suke kawai. A aikace biyayya ga dokokin addinin Musulunci ta yi rauni saboda ba a bin dokokinsa wajen yanke hukunci kamar yadda suke cikin Alqur’ani da Hadisan Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi. Haka kuma, tsarin shugabanci a wannan zamani ya sha bamban da yadda Hausawa suka gudanar da shi kafin zuwan wannan zamani.
Zuwan Turawa ƙasar Hausa ya sa sun kawo sabuwar rayuwa wadda ta shafi yadda ake gudanar da mulki, sun ce mulkin Dimokraɗiyya ne, watau jama’a su zaɓi shugabannin da za su yi masu jagoranci, amma saboda yadda ake son mulkin ya sa ba a barin jama’a su zaɓi waɗanda za su yi masu mulkin adalci. Maimakon haka ana tilasta shugabanni a kan mutane waɗanda suke sace dukiyar al’umma, suka cusa wa al’umma matsanancin talauci wanda ya yi sanadiyyar mayar da wasu mutane bayi, ana juya su yadda aka so, ana sanya matasa suna cin mutunci dukkan wanda ba ya goyon bayansu ko wanda ya ce ba su yi daidai ba. Wannan ne ya sa a yanzu gaskiya da riƙon amana suka yi rauni a cikin zukatan wasu mutane. Abin da ake so kawai shi ne, ta wace hanya za a sami kuɗi a azurta a dare ɗaya ba tare da an yi wata wahala ba. Sannan kuma, zumunci ya yi wuya, don a wannan zamani ana bin aƙidar kowa tashi-ta-fisshe shi. Ɗan’uwa mai arziki ba ya taimaka wa danginsa mabuƙata, maƙwabci ba ya kyautata wa waɗanda yake maƙwabtaka da su. Yara ba su kunyar manya, manya ba su tausaya wa ƙanana. Ayyukan ɓarna (zinace-zinace da ta’addanci da sace-sace da fashi da makami) sun yi yawa cikin ƙasa har ta kai matsayin ba a jin kunyar aikata su a gaban jama’a.

4.1 Shawarwarin da za su Taimaka a sami Ingantaccen Shugabanci a Wannan Zamani
Matuƙar ana son samun gyara yadda wannan ƙasa tamu za ta sami ingantaccen shuganacin da zai sa a sami zama lafiya, arzikin ƙasa ya dawo yadda kowa zai sami wadata da ƙaruwar arziki ya zama dole a koma wa tsarin tarbiyyar Hausawa ta gargajiya wadda za a yi mata wasu ‘yan gyare-gyare yadda za ta tafi daidai da zamani:
- Shugabanni su riƙa gudanar da mulkinsu cikin adalci, kuma da yake a wannan zamani ana mulki irin na siyasa, ya zama dole a bar jama’a su zaɓi waɗanda za su shugabance su, don kuwa tilasta shugaba a kan al’umma zai ƙara ɓata al’amari.
- Ya zama dole a riƙa tsare gaskiya da riƙe amana wajen gudanar da mulki da sauran ma’amalolin rayuwa a kowane hali mutum ya sami kansa.
- Ƙara sada zumunci da taimakon juna zai taimaka a ƙara samun fahimtar juna, yadda za a gudu tare a tsira tare.
- Koma wa sana’o’in gargajiya na Hausawa don samun abubuwan yi maganin zaman banza da yin bangar siyasa da maula.
Jawabin Kammalawa
Bisa la’akari da abubuwan da aka tattauna a wannan takarda waɗanda suka danganci tarbiyyar Hausawa ta gargajiya don samo hanyar da za ta taimaka a sami ingantaccen shugabanci a wannan zamani, a iya cewa ya zama dole a fahimci cewa, kyakkyawar tarbiyya ita ce ginshiƙin da zai tarbe dukkan wata fitina da za ta fuskanci kowace ƙasa. Kyakkyawar tarbiyya ce za ta taimaka wa ɗan’adam ya san abin da yake bauta wa, ita ce za ta horar da mutum ya san abubuwan da abin da yake bauta wa yake so da waɗanda ba ya so. Haka kuma, ya zama dole a riƙa gudanar da shugabanci bisa adalci da tsoron Allah, a kyautata wa waɗanda ake shugabanta ta hanyar sauraren koke-kokensu da biya masu bukatunsu. Sannan kuma, ya zama dole a bar al’umma ta riƙa zaɓar shugabannin da za su jagoranci mulkinta. Riƙo da gaskiya da tsare amana na daga cikin abubuwan da matuƙar aka rie su za a sami ingantaccen shugabancin da zai taimaka wa al’umma ta sami dauwammen cigaba da zama lafiya. Dukkan al’ummar da take sadar da zumunci, kuma ‘ya’yanta suna taimakon junansu za ta ƙara samun cigaban da zai taimaka mata ta zauna lafiya. Idan har muna son samun ingantaccen shugabanci a wannan ƙasa tamu, ya zama dole mu rungumi waɗannan hanyoyi na tarbiyya kamar yadda Hausawa suka gudanar da su musamman bayan sun karɓi addinin Musulunci.
Manazarta
Adamu, M. (1978) The Hausa Factor in West African History, Zaria/Ibadan: Ahmadu Bello University Press/Oxford University Press of Nigeria.
Alhassan, H. da Wasu, (1982) Zaman Hausawa.Zariya: Institute of Education Press, ABU.
Ibrahim, M.S.(1982) ”Dangantakar Al’ada da Addini:Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Isah, Z. (2006) “Gaskiya a Tunanin Hausawa”, Kundin Digiri na Farko. Zariya: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Afirka, Tsangaya Fasaha, Jami’ar Ahmadu Bello.
Sallau, B.A.S. (2009) “Sana’ar Wanzanci da Sauye – Sauyen Zamani Jiya da Yau”, Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Sallau, B.A.S (2010) Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna:M.A.Najiu Professional Printers, No. 3 Kenya Road.
Smith, M.G. (1957) “The Hausa System of Social Status”, in Africa Vol. XXVII. No.1.
Shu’aibu, M. (2003) “Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Usman, Y.B. (1972) ”Some Aspects of the External Relations of Katsina Before 1804”, Savanna Vol.I.No.2.
Bashir Aliyu Sallau. Ph.D. (Sarkin Askar Yariman Katsina) Farfesan Nazarin Al’adun Hausawa Sashen Koyar da Hausa Tsangayar Fasaha Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dutsin-ma Jihar Katsina – Katsina ne ya yi mana wannan nazarin.