Getting your Trinity Audio player ready...
|
Kwararru daga kafafen yada labarai sun bukaci al’ummar masu tantance bayanan da ba daidai ba da su nemi sabbin hanyoyin samun tallafi bayan da wasu kafofin samun tallafin janye dan tabbatar da amincin labarai.
Wannan kirar ta zo ne yayyin wani taron X space da Dubawa ta shirya ranar 3 ga watan Afrilun 2025, wanda aka yi wa taken “Yunkurin lakantar muhallin tantance bayanan da ba daidai ba wanda ke cigaba da sauyawa: Kalubale, damammaki da makomar amincin bayanai.”
Dandalin ya mayar da hankali ne kan sauye-sauyen da aka samu kwanan nan a fannin tantance bayanan da ba daidai ba tare da jaddada matsaloli da kuma damammakin da wadannan sauye-sauyen suka samar.
A watanni hudun da suka gabata ne hadakar kungiyoyin da ke binciken tantance bayanan da ba daidai ba wato IFCN suka sami wata sanarwa daga babban kamfanin shafukan sada zumunta na Meta inda ya ke cewa ya yanke shawarar dakatar da kawancen da ya ke yi da duk kafafe/shafukan da ke tantance bayanan da ba daidai ba a Amurka. Sa’annan haka nan zai kasance ga sauran dandalolin binciken da ke wajen Amurka shekara daya bayan wannan sanarwar.
Wannan sanarwar mai tayar da hankali na nufin cewa Meta zai dakatar da tallafin da ya ke bai wa kungiyar hadakar masu binciken, wanda ke zaman babban kaso na kimanin kashi T 45.5 cikin 100 na jimilar kudaden da ta ke samu. Dan haka kungiyar ba ta san inda za ta dosa dan samun kudi nan gaba ba. Wannan na kuma sanya alamar tambaya kan irin yardar da sauran duniya ke da shi a kan kwarewar kungiyoyin da ke gudanar da binciken wajen tabbatar da dorewar ayyukan tantance bayanan dan tabbatar da cigaban al’adar gaskiya.
An kaddamar da tattaunawar ne da mai gabatarwa, Nanji Nandang, babban mai dauko rahotanni a Cibiyar Bincike Mai Zurfi a labarai ko kuma ICIR, wanda ya gabatar da wadanda za su yi mahawara. Ya fara ne daga babban editan DUBAWA, Kemi Busari, inda Nanji ya tambaye shi irin tasirin da katse tallafin zai yi a dandalolin tantance bayanan da ba daidai ba.
Dan jaridan wanda ya lashe lambobin yabo da dama ya fadawa mahalarta cewa janyewar da Meta ya yi zai kori mutane da dama daga ayyukansu kuma kungiyoyin binciken za su yi fama saboda rashin wannan tallafin.
Ya kuma kara da cewa ingancin aikin zai ragu domin shi “communiyt notes” din salon da Meta ya ce zai maye gurbin tantance bayanan kamar yadda aka san shi yanzu ba lallai ne ya gudanar da aikin yadda ya kamata ba, musamman a batutuwan da aka kirkiro da manhajar da ke kwaikwayon dabi’un ‘yan adam ko kuma wadanda aka rubuta cikin harsunan gargajiya, domin tantance su zai dauki lokaci sosai.
“Dan haka idan har kungiyoyin da ke tantance bayanan da ba daidai ba suka gaza biyan ma’aikata sakamakon rashin tallafi daga kafofin da suka saba samu, lallai zai shafi akin mutane,” a cewar Kemi, inda ya kara da cewa, Wata sa’a bazanan karya kan fito ne daga harsunan gargajiya. Community notes ba za su iya shawo kan su ba. Bugu da kari ana iya shafe watanni kafin a iya tantance hotuna da makalun shafuka.”
Editan ya kuma jaddada cewa yawancin kungiyoyin tantance bayanan ba na kudi ba ne, kuma idan har ba su da kudi suna iya shiga siyasa da bangaranci inda tilas su rike yin abin da wanda ke ba su kudi ya umurce su su yi.
Domin sake fadada tattaunawar, Nanji ya tambayi Rejoice Taddy kwararriya wajen binciken bayanan da ba daidai ba ko ana iya amfani da hukumar da ke kula da bayannan sirri na OSINT wahen yaki da da wannan lamarin. Rejoice ta ce ‘yan jarida da masu binciken gaskiya wadanda ke iya gane bayanan da ba daidai ba kai tsaye, musamman yanzu da ake da manhajojin da ke kwaikwayon dabi’un dan adam, na bukatar amfani da kayayyakin aikin OSINT wajen tantance labaran karya yadda ya kamata.
“Ya na da mahimmanci cewa, ‘yan jarida da masu aiki a kafafen yada labarai wadanda, da duk wadanda ke ganin bayanai irin wadannan su iya amfani da OSINT su karyata wadannan zarge-zargen,” ta kwatanta.
Samad Uthman, wanda ke aiki da kamfanin dillancin labaran AFP, ko kuma Agence France-Presse, ya tofa albarkacin bakinsa dangane da irin matakan da ya kamata a dauka yayin da ake fama da matsalar rashin tallafi a al’ummar masu binciken gaskiya.
Ya ce ya kamata kungiyoyi su fara neman wuraren da ua su sami tallafi. Ya kuma bayyana cewa labaran karyar da ake da su sun fi karfin wadanda ke aikin tantance gaskiya dan haka ya kamata a sami daidato.
Daga nan Nanji ya yi wa Kemi tambaya dangane da irin kalubalen da za’a iya samu idan har aka kulla kawance tsakanin dakunan labarai da masu binciken gaskiyar da ke yaman kansu da kamfanonin fasaha wajen tabbatar da ingantattun labarai musamman a yanayin da ake ciki yanzu inda bangarorin ba su cika jituwa ba.
A martaninsa, editan ya ce tilas ne a samar da irin wannan dangantakar tsakanin duka bangarorin domin al’ummar yanzu na cike da labaran karya kuma yawancin wadannan labaran na kan kafofin sadarwar da manyan kamfanonin fasaha ke da shi. Ya ce ana iya samar da dangantaka mai aminci idan har duka bangarorin suka amince su samar da amtakan da za su tilastawa kamfanonin bayar da hadin kai tare da jaddada musu da mahimmancin da suke da shi wajen tabbatar da sahihancin labarai.
Daga baya Kemi ya ce tilas kungiyoyi su fara duba wasu sabbin hanyoyin cimma burrukansu na kudi. A cewars binciken gaskiyar ba shi da banbanci da aikin jarida, dan haka wannan ke kara sa shi kasancewa tilas “ a rika gudanar da tattaunawa dangane da tsarin kasuwanci ta yadda idan har daya ya durkushe ana iya komawa ga dayan.”
Daga nan mai gabatarwar ya tambayi masu mahawarar ko suna da shawara dangane da irin matakin da ya kamata kafofin yada labarai na gargajiya su dauka a yakin da suke yi da yaduwar bayanan karya.
A martaninsa, Samad ya ce bacin yadda ake rubuce-rubucen fadakarwa da ma amfani da harsunan gargajiya, masu amfani da shafuka sun fi mayar da hankali kan abubuwan da infuluernsas ke yi: “Abubuwan da suka fi dauakr hankalin jama’a ke nan.” dan haka ne ma ya ce ganin yadda matasa ke ma’ala da shafukan sadarwar sosai, ya kamata ‘yan jarida su mayar da hankali su kuma rike hulda da mahawara matasan musamman ta yin amfani da salon maganar da suke amfani da shi.
Rejoice ta yi bayani kan karuwar infuluwensas a soshiyal mediya wadanda ake amfani da su wata sa’a a yada bayanan karya. To sai dai ta kara da cewa ta na fata masu binciken za su rika amfani da bazanan sz wajen fadakar da jama’a da wayr da kansu musamman a yankunan karkara dan kada abun ya lalace.
Editan sashen Faransanci na Africa Check, Valdez Onanina ya nuna cewa dole kafafe su yi amfani da salon zaben labaran da masu sauraronsu ko karanta su ke so. Ya yi misali da yin amfani da bidiyoyi, shirin rediyo na podcast da kuma sauran shafukan sada zumunta inda za ce yawancin masu binciken sun iya yada bayanai da kyau ta yadda jama’a za su fahimta.
Da ya ke na sa tsokacin, Kemi ya ce zawancin lokuta masu binciken kan dauki irin labaran da suka san mztane za su so ji ne kawai. Ya bayyana cewa yawancin mutanen na son shiga shafukan da suke da sha’awa ne ba shakka. Amma duk da haka bai kamata su mance da aikinsu na kasancewa kan gaba wajen wanzar da shika-shikan dimokiradiyya.
Yayin da ake cigaba da fargabar inda za’a sami kudi, tilas ne a sa himma wajen samun sabbin hanyoyi da ma yanayin gabatar da bayanai dan tabbatar da inganci da nagartar labarai ta yadda zai taimakawa dimokiradiyya – domin shi ne ginshikin wannan aikin!