Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin instagram, unfilteredr3ailty, ya wallafa bidiyon da ke da’awar cewa sabulun goge hakora ko kuma toothpaste kamar yadda aka san shi da turanci “na zaman abu mafi gubar da ake sanyawa a baki” haka nan kuma sinadarin fluoride din da ke ciki, wanda sinadari ne ke inganta karfin kasusuwan jiki da na hakori “na da dafi ga kwakwalwa.”

Hukunci: Yaudara ce. Bayanan kimiya masu nagarta da hujjojin da muka samu wajen bincike ba su goyi bayan cewa sinadarin fluoride din da ke cikin man goge baki na da hadari ko lahani ga kwakwalwa ba. Likitocin da ke kula da hakora sun tabbatar cewa sinadarin fluoride na da mahimmanci ga ingancin hakora da ma lafiyar baki gaba daya sa’annan ba ya janyo wani lahani ga kwakwalwa kamar yadda ake da’awa.
Cikakken bayani
Bidiyon da wani mai amfani da shafin instagram da suna unfilteredr3ailty na da’awar cewa sabulun goge hakora na da hadari sosai. Mai amfani da shafin ya kwatanta sabulun a matsayin “abu mafi gubar da ake sanyawa a baki” ya kuma yi gargadin cewa sinadarin fluoride din da ke kunshe a cikin sabulun na da lahani ga kwakwalwa.
Daga ranar 17 ga watan Satumban 2025, dubban mutane sun yi ma’amala da labarin inda wasu 5,900 suka raba labarin, tokacin kwament sektion kuma ya kai 179 sa’annan da alamar like 4,700.
Daga cikin tsokacin da aka yi dai an bayyana ra’ayoyi mabanbanta. Lesley.harris ta runuta cewa “abun kuma ya fara zama hauka, yanzu ba za mu ma iya goge hakoranmu kuma ba ke nan. Duk wani abun da muka ci ya na da hadari. Abun da a baya ya ke inganta lafiya yanzu ya zama guba. Da haka ai sai mu kwanta kawai mu mutu.”
Wani mai amfani da shafin shi ma, Teen_minute2020, ya bayyana cewa akwai wadansu abubuwan da za su iya maye gurbin sabulun goge hakoran wadanda ba sai an saya ba sa’annan su na da rangwame sosai.
A waje guda kuma, Mackayderksenunderhill ya karyata zargin ne da bayyana abin da ya faru da shi a zahiri: “Ya ce da nake yaro an rika ba ni maganin da ke kunshe da sinadarin Fluoride kuma ina amfani da sabulun goge hakorin da ke kunshe da fluoride, yanzu shekaru na na haihuwa 76, kuma lafiya na lau! Ko sadda na ke yaro ma na rika ci kuma ba abin da ya same ni.”
DUBAWA ta yanke shawarar tantance wannan batun na abin goge baki domin abu ne da ake amfani da shi kullun.
Abin da kimiyya ke cewa
Fluoride sinari ne da ake amfani da shi cikin abin goge baki dan kare hakora daga rubewa. Kusan kowanne na dauke da sinadarin sai dai yawan ya banbanta amma dukansu ba su wuce mizanin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kayyade.
Bisa bayanan shafin labaran kiwon lafiya na Medical News Today, fluoride ba shi da wani lahani ga kwakwalwa. Illolin da kan biyo bayan amfani da shi kamar matsalar sauyi a launin hakori wanda ake kira dental fluorosis a turance, kan bayyana ne idan har aka yi amfani da shi fiye da kima. Ganin yadda sabulun goge bakin ko kuma toothpaste a saman hakorin ake amfani da shi ba wai hadiyewa ake yi ba, amfani da shi ba ya tattare da hadari musamman idan dan kalilan ne ake amfani da shi.
Cibiyar shawo kan cututtuka da tabbatar da kariya na bayar da shawarar sanya ido kan yara a duk sadda suke goge hakori dan kada su hadiye shi domin zai iya sauya launin hakorinsu idan har suka yi amfani da shi fiye da kima. To sai dai sabukun goge bakin ba shi da lahani idan har aka yi amfani da shi yadda ya kamata.
Ra’ayoyin kwararru
Wani likitan hakori, Timileyin Daniel, ya ce sinadarin fluoride abu ne da aka yi ammana da shi a matsayin sinadari mai amfanin gaske a duk fadin duniya.
“Hukumar Tarayya ta tabbatar da ingancin abinci da magunguna a Amurka ta sanya sinadarin cikin jerin abubuwa na musamman. Wannan kuma ya sami goyon bayan kwani na musamman na Hukumar Lafiya ta Duniya kan sinadarai wanda ya lisafta fluoride din a cikin sinadarai 14 na musamman da dan adam ke bukata,” ya ce.
Timileyin ya jaddada cewa idan da fluoride na da hadari, cibiyoyin lafiya masu nagarta za su bayyana hakan ba tare da bata lokaci ba.
Ya ce kamar kowani magani ko sinadari, amfani da shi fiye da kima na iya janyo hadari musamman a kananan yara saboda hadiya. Ko da shi ke duk da haka ba’a taba bayyana lahani ga kwakwalwa a matsayin daya daga cikin hadarurrukan da akan fuskanta ba.
“Da’awowi irin wadannan yawanci wadanda ke neman tallata nasu kayayyakin wadanda za su iya maye gurbin sabulun goge bakin ne suke yada su. Ban da haka ma yawan sinadarin da ake sanyawa cikin abin goge bakin ba shi da yawa kuma ba zai taba wuce kima ba, kuma ma idan har hakan ya faru akwai yadda ake kula da yaran da suka hadiye shi,” ya kara da cewa.
Deborah Babatope, wadda ke aikin kula da hakoran ita ma ta karyata wannan da’awar na cewa flouride na da lahani ga kwakwalwa, ta na cewa abin da hakora ke bukata ke nan dan su kasance cikin lafiya.
“Fluoride ba shi da hadari: hasali ma ya na da kyau wa hakora. Lokacin da ya kan kasance da hadari shi ne idan an yi amfani da shi fiye da kima, musamman a mata amasu juna biyu, saboda lahanin da zai iya yi a kan kwakwalwar jinjiri. Amma dai idan har ba’a wuce mizanin da ya kamata ba, ba zai iya la’anta kwakwalwa ba. Floride ne ke kare karfin hakora, kuma ma yawancin abincin da muke ci da ruwan da mu ke sha duk suna dauke da wannan sinadarin,” ta bayyana.
Deborah ta kara da cewa yawancin sabulan goge hakora a Najeriya na dauke da iya yawan fluoride din da aka tantance a matsayin yawan da ya kamata, ba kamar wasu kasashen ba wadanda ruwansu ma na kunshe da fluoride dan haka ba wuyan samun tooth paste din da ba shi da flouride.
“A Najeriya, babu sinadarin Fluoride cikin ruwan sha sosai dan haka ne ma ya sa samun sabulun goge baki mai flouride ke da mahimmancin gaske ga lafiyar baki dan kare hakora daga rubewa,” ta ce.
A Karshe
Da’awar cewa sabulun goge hakora mai fluoride na ha lahani ga kwakwalwa yaudara ce. Hujjojin kimiyya sun nuna cewa idan har aka yi amfani da shi yadda ya kamata ya na da amfani sosai wajen kare hakora daga rubewa.