|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wasu masu amfani da shafin sada zumunta sun yi da’awa cewa allurar rigakafin hana kamuwa da kwayar cutar da ke haddasa kansa ta mata da ake kira (human papillomavirus vaccine (HPV) wacce sau tari ake cewa a yi wa mata daga shekaru 9 zuwa 14 tana kawo rashin haihuwa ko ma ta yi sanadi na rayuwar wanda aka yi wa allurar. duk da cewa wannan da’awar ta bulla a 2023, har yanzu ana yada bayanan a shafuka irin su Whatsapp

Hukunci: Karya ce!Bincike da dama da aka yi da bayanan masana sun tabbatar da cewa babu wata sheda ta kimiya da aka samu wacce ta tabbatar da wannan da’awa, sai dai ma suna bayyana cewa yin allurarr na kashe kwayoyin cutar ta HPV wacce ke zama sanadi na samun cutar kansar mahaifa.
Cikakken Sako
A watan Oktoba, 2023 gwamnatin Najeriya ta bijiro (introduced) da allurar rigakafi ta human papillomavirus (HPV) vaccine wacce aka kudiri aniyar a yi wa yara mata miliyan bakwai, wadanda ake son ayi wa wannan allura yara ne daga shekara 9 zuwa 14.
A Najeriya wannan kwayar cuta ta human papillomavirus, a cewar Majalisar Dinkin Duniya ita ke kawo cutar kansar mahaifa da kaso 70 cikin dari, kansar kuma ita ce cutar kansa ta uku da aka fi sani wacce kuma ke zama ta biyu da aka fi samu tana jawo cutar kansa mai halaka mata tsakanin shekaru 15 zuwa 44.
Muhammad Ali Pate ministan lafiya da zamanatakewa da walwala ya ankarar (noted) cewa “HPV ita ke jawo cutar kansar mahaifa, kuma iyaye za su iya kaucewa ganin tashin hankali da asarar kudade ta hanyar yi wa yaransu allurar rigakafi.”
Ya bayyana cewa yayi wa ‘ya’yansa mata hudu wannan allura kuma yana kira ga iyaye su yi wa yaransu irin wannan allura.
Gwamnatin ta bayyana cewa gangamin allurar na yi da yawa a makarantu da yankunan al’umma an tsara shi lokacin kaddamar da shirin a jihohi 16 da Babban Birnin Najeriya Abuja.
Ya kara da cewa za a shigar da aikin allurar cikin tsarin alluran rigakafi da ake yi a cibiyoyin kula da lafiya. Zagaye na biyu na allurar an tsara shi a watan Mayu 2024 a jihohi 21 (states).
Me ake nufi da Human papillomavirus?
Hukumar Lafiya ta Duniya World Health Organization ta bayyana kwayar cutar ta
human papillomavirus (HPV) a matsayin cutar da ake yawan samunta ta dalilin saduwa tana kuma shafar fata da yankin al’aura da makogwaro.
Hukumar tace kusan duk mutanen da ke mu’amala da ta shafi jima’i a wani lokaci na raywarsu suna kamuwa da kwayoyin cutar ko da yake wasu basa ganin wata alama , wasu kuma garkuwar jiki ke kawar da HPV daga jikin na dan Adam.
Sai dai kuma idan ana harbuwa da kwayoyin cutar akai-akai hakan na jawo fitar wasu kwayoyin halitta wadanda ke zama baki wanda kuma suke bunkasa su zama cutar kansa.
A cewar hukumar lafiyar ta duniya “Idan wannnan kwayoyin HPV aka ci gaba da samunsu akai-akai (a kasan mahaifa wanda ke zuwa har farjin mace ko hanyar da ake haihuwa), kaso 95% shi ke zama dalilin kamuwa da cutar kansar mahaifa.”
A nasa bangare, asbitin Cleveland Clinic ya bayyana cewa akwai nau’ikan HPV sama da 100, yace daga cikin wannan adadi akwai nau’ika 30 na HPV da ke shafar al’aura, wanda ya hadar da farji da kasan mahaifa da azzakari da dubura da babban hanji.
Ya kara da cewa a kwai nau’in HPV da ke shafar al’aura basu da illa, wasu kalolin kuma sau da yawa nau’i na 16 da 18 suna sauya kwayoyin halittar kasan mahaifa (cervical dysplasia) wanda kan haifar da kansar kasan mahaifa.
“…HPV na zama babbar barazana ga mata da mata a lokacin haihuwa (AFAB) saboda babbar barazanar HPV na iya girmama ta jawo cutar daji ko kansa ta kasan mahaifa idan ba a kula ba a lokacin da ya dace.
Yin gwajin da wuri na taimakawa wajen kare kamuwa da cutar kansar ta kasan mahaifa, Akwai nau’in HPV wanda bashi da illa da ke haifar da kurarraji ga mata’’ kamar yadda asibitin ya bayyana.
Yayin da kansar kasan mahaifa ke zama sananniya akwai kuma sauran wasu nau’ikan HPV da ake samu su haifar da cutar dajin ko kansar dubura da ta azzakari da ta farji da ta saman farji.
Da take bayani kan yadda ake yada cutar Medical News Today tayi bayani cewa HPV na yaduwa ta hanyar saduwa, abin fargabar shine wannan na iya faruwa ko da kuwa babu wata alama da aka gani.
Duk da cewa ba duka harbuwa da kwayoyin cutar ta HPV ke sanadi na samun cutar kansa ba, akwai karin barazana idan mutum ya harbu da wasu kwayoyin cutar da ake samu ta sanadiyar saduwa kamar chlamydia da ake samu ga wadanda suka haihu da wuri da masu tarin ‘ya’ya da masu shan taba sigari da masu raunin garkuwar jiki.
Cibiyar kula da bazuwar cutika ta Centers for Disease Control ta ba da shawarar cewa yara da maza da mata da ke tsakanin shekaru 11 da 12 koma in suna shekaru 9 akwai bukatar ayi masu allurar rigakafi don rage barazanar ta HPV.
Duk da kokarin gwamnati da fadakar da al’umma kan wannan allurar rigakafi shirin DUBAWA ya lura da yadda ake yada bayanai da ba na gaskiya ba kan wannan shiri tare da sage gwiwar iyaye da masu daukar nauyi na matasan su amince ayi masu allurar.
A wani shafin Facebook mai zaman kansa, Once A Mum Always A Mum Initiative (OMAM), wata da ke amfani da shafin ta bukaci jin ra’ayin jama’a kan tasirin rigakafin allurar ta HPV.

Hoto da aka dauka daga shafin na Facebook
Cikin sa’oi kadan wasu daga cikin mambobin shafin suka ba ta amsa, inda suke cewa ta manta da wannan batu tana haifar da cutar rashin haihuwa ga yarinya anan gaba ko ma ta yi sanadi na rai kamar yadda za a gani a wani hoto da aka dauka a kasa. Wani hoton amsa da aka bata a shafin Facebook
Wata mai amfani da shafin na Facebook ta yi da’awar cewa wannan allurar ana yinta ne don rage yawan al’umma a Najeriya ta hanyar mayar da yarinyar mara haihuwa. DUBAWA ya lura cewa wannan martani yayi kama da rashin fahimtar da dama ake yadawa ba ma a shafukan sada zumunta kadai ba.
Hoton wata amsar da aka bayar a shafin na Facebook
Shugaba a makaranta ya fada wa DUBAWA tasa fahimta
DUBAWA ya lura cewa sakamakon abin da ake fadi da dama sun gaza tattara bayanan yara mata wadanda za a sanya su cikin wadanda za a yi wa allurar.
A daya daga cikin gungun makarantun da mai binciken yaje shugaban makarantar ya fitar da sanarwa da aka lika a bango daga hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Legas da taken: Sanarwar gabatar da allurar rigakafi ta HPV a Najeriya.’
Sakon ya fadakar da iyaye da masu lura da yara mata masu shekaru 9 zuwa 14 su kai yaransu a yi masu allurar rigakafi.
Hoton sakon da aka lika a makarantar
Amma shugabar makarantar da ba ta so a bayyana sunanta saboda dalilai na tsaro ta bayyana wa DUBAWA cewa amsoshi da suke karba daga iyayen yara abun babu dadi.
“Mun samu labarin cewa gwamnati za ta fara allurar rigakafi, wanda tuni iyayern yaran sun same mu suna fada mana cewa “allurar kisa ce” don haka kada mu bari ayi wa yaransu.Nayi kokarin wayarwa da wata kai amma taki tace allurar mutuwa ce, inda take ba da misali da allurar rigakafin COVID-19. Na fada mata cewa allura ce ta kaucewa kamuwa da cutar kansa, ni kaina na so na yi allurar, idan kuma da a ce yarana sun kai shekarun da na sa a yi masu.’’ kamar yadda ta bayyana.
A kokari na jan hankalin wasu iyayen ta bayyana cewa:
“Abun da muka yi shine mun tura wasika wadanda suka amince kamar uku ne (biyu daga cikinsu daga iyali guda sai kuma guda daya) sai da muka kira iyayen don su tabbatar mana, sauran yaran sun fada mana basu nuna amincewarsu ba saboda iyayensu na jin tsoro. “Na samu wasu iyayen kai tsaye don tattaunawa da su suka ce ba zan gane ba, don haka dole na tafi. ”
Shugabar makarantar ta bayyana cewa duk yaran da suke da shekaru sama da 20 a makarantarta hudu ne kawai a cikinsu suka amince a yi masu allurar, tace uku a makarantar aka yi masu allurar yayin da daya daga cikinsu mahaifiyarta ce ta kaita cibiyar lafiya aka yi mata allurar.
Saboda damuwa kan batun sai ta yi kira ga gwamnati ta ci gaba da ilimantar da iyaye cikin yaruka ko harsuna da suke ji a kafafan yada labarai don sanin muhimmancin allurar rigakafin.
Me bincike ke cewa game da allurar HPV
Bincike (article) da aka wallafa a watan Oktoba,2022 kan samar da kariya daga allurar HPV ya bayyanar da cewa allurar ba a maganin cutar da aka samu da ita, tana hana kamuwa da kwayoyin cutar ne kan daidaikun mutane. Binciken kuma ya tabbatar da cewa ana samun tatsuniyoyi kala-kala da rashin fahimta a kan allurar a wajen mutane, inda ya bukaci ganin an fadakar da al’umma kan tasirin allurar da kariya daga cutar kansa. A cewar binciken wannan zai sanya iyaye su rika yin allurar rigakafin ga yaransu.
Sakamakon binciken da aka samu yayi daidai da rahoton wani bincike research irin wannan da aka yi a garin Gambella a Kudu maso Yammacin kasar Habasha, wanda ke nuni da bukatar ganin an kara ilimantar da al’umma kan allurar ta HPV da yadda ake samun cutar da bukatar ganin al’umma sun sauya halayyarsu da samun iliimi game da cutar.
Wata makalar article da aka wallafa a PubMed ta nuna irin illar allurar ta HPV bayan tsawon lokaci kamar yadda aka gani a gwaje-gwajen jami’an lafiya da bayanan da aka tattara a duniya. Abubuwan da aka gano a nazarin ya nunar cewa an samu ci gaba a dangane da daukar matakan kariya a game da allurar rigakafin HPV da kan haifar da cutar kansa me kama bangaren al’aura da kuma baki kamar yadda aka tabbatar a gwaje-gwajen kimiya da ma abin da ke zama na zahiri a duniya. Har ila yau binciken ya nunar da cewa ko da a ce an yi wa yaran maza da mata allurar rigakafin ta HPV a lokacin da suka fara balaga, wani abu kuma muhimmi shine a sanya idanu wajen ganin tasirin allurar har zuwa lokacin da za su zama suna aiwatar da jima’i a lokacin da suke shekaru daga 20 zuwa 30.
Ra’ayin Kwararru
A kokari na kawar da shakku da labaran da ba haka suke ba a dangane da allurar rigakafin ta HPV, DUBAWA ya ga dacewar tattaunawa da kwararrun likitocin mata ganin yadda iyaye ke nuna shakkunsu kan allurar rigakafin wannan cuta.
Dr Nathaniel Adewole, farfesa kan abin da ya shafi daukar ciki da haihuwa kuma likitan mata a asibitin koyarwa na Abuja ya fadawa DUBAWA cewa babu wata alaka tsakanin wannan allurar rigakfi da mutuwa ko rashin haihuwa kamar yadda wasu ke da’awa.
Adewale yace ana yin allurar rigakafin ne don rage fargaba ta yiwuwar kamuwa da cutar ta kansa kamar yadda ake rigakafi ne don rage fargabar kamuwa da cutar polio, yace cutar kansar mahaifa ita ce cuta ta biyu ta kansa da ta fi kashe mata a Najeriya.
“Allurar HPV ba ta da wata nasaba da rashin haihuwa haka, kuma bata da wata nasaba da mutuwa, inda ace ana mutuwa da kaji yadda al’umma za su fito suna kokawa. Idan suka dauki matakin sanya yaransu aka yi masu allurar da wuri hakan shine mafi kyau, cutar sankarar mahaifa na iya mayar da mashahurin mai kudi ya zama talaka, bai kamata ayi wasa da ita ba, duk wanda ya samu wannan dama kada yayi wasa da ita, tsawon lokaci muna ganin yadda gwamnatin Najeriya ke hada kai da wasu hukumomi na kasashen waje don tabbatar da ingancin lafiyar al’umma da yara,” a cewar likitan.
Kwararren likitan matan ya bayyana cewa mata da suke tsakanin shekaru 9 zuwa 14 dole ayi masu allurar don kare su daga cutar sankarar mahaifar da sauran cutaka masu alaka kafin lokacin da za su shiga harkoki da suka shafi jima’i. Sai yayi kira ga iyayen yaran da su rungumi shirin allurar rigakafin.
“Wannan babban zuba jari ne daga bangaren gwamnati, tsari ne mai kyau, allura ce mai tsada da gwamnati tace kyauta ce, mutane na fadin wani abu daban, kada a manta wadannan mutane ne dai suka yi allurai aka rage masu cutar Polio , da tarinfika da kyanda da sauran cutuka,” a cewarsa.
Shima a nasa bangaren, Dr Qudus Lawal, kwararren likita kan sha’anin abin da ya shafi haihuwa da likitan mata a asibitin kwararru na Irrua Specialist Teaching Hospital a jihar Edo yace “allura ce mai kyau kuma a kwai nazari da dama da ya goyi bayan wannan” Babu wani abun tashin hankali game da wannan kasancewar akwai wannan tsari a kasashe da suka ci gaba tun a shekarar 2006 inda aka yi wannan allura sama da miliyan 270 ga matan wanda kuma ba a taba samun rahoto na ta zama dalilin rashin haihuwa ba ko ma a ce wai an mutu ta dalilinta ba.
Dr Lawal yace wannan bai rasa nasaba da yadda ake yada labarai wadanda ba haka suke ba, dangane da allurai a Najeriya, kuma gashi yara mata ake son yiwa wadanda sun haure shekaru da ake ganin na yin allura ne ga yara, ga kuma sanin cewa abun na da alaka da batun jima’i wanda ake ganin abin kunya ne tattaunawa ma a kansa.”
Ya kara da cewa a Najeriya wannan gangami ya kuma takaita ne ga yara mata saboda takaitattun kudade”A wasu kasashe irin Ostareliya da Burtaniya da wasu sassa na duniya wannan allura ana yinta ne ga maza da mata , amma inda ke da kudaden aikin kadan kawo yanzu ana yi wa yara mata ne kawai.’” a cewarsa.
Dr. Lawal ya kara da cewa batun cewa ana mutuwa dalilim allurar rigakafin ta HPV babu wata “hujja akai” ya kara da cewa “a kimiya muna da hanyoyi na gano yadda abubuwa ke da alaka da juna ko ya wani abu ke jawo wani abun.”
“
“Ga misali idan mutum yanzu ya sha lemon Coke bayan minti biyu sai ya hau mota ya fita ba za ka ce ya mutu dalilin shan Coke ba, irin wadannan mutane na alakanta abubuwa guda biyu ne marasa alaka da juna su ce allura ce ke zama dalili na faruwar wani abu, a kimiyance babu wata hujja da ta nuna cewa allurar rigakafin HPV tana da alaka da duk wadannan abubuwa da ake fadi, a cewarsa.
A Karshe
Da’awar cewa allurar rigakafi na zama dalili na jawo rashin haihuwa da mutuwa karya ne, babu wata hujja a kimiyance da ta nuna hakan.




