|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wata mai amfani da shafin Instagram, @Drbelswelness, claimed tayi da’awar cewa sabon bincike da aka gudanar ya nuna cewa ingancin kwan haihuwa na mata baya raguwa saboda shekaru, amma maniyin maza na rage inganci saboda shekaru.

Hukunci: Yaudara ce. Shedu na kimiya da aka tattara sun nunar da cewa duka maza da mata damar su haihu na raguwa idan suna kara tsufa ko da yake sun banbanta yadda suke yi, mata kan rasa yawa da ingancin kwan haihuwarsu yayim da maza kyau na maniyinsu ke raguwa da yadda kwayoyi halittarsa ke rarrabuwa a tsawon lokaci.
Cikakken Sako
Aikin likitancin zamani na kara zakulo hanyoyi na kara fahimtar yadda jikin dan Adam yake. A shekaru na baya-bayan nan an samu ci gaba advancements a ilimin kyawowin halitta da yadda kimiyar kananan halittu take da yadda ake iya daukar hoto na halitta a fitar da tarin bayanai daga ciki, wannan ya sanya aka kara fahimta na abin da ya shafi lafiya da cutittika. Wannan ci gaba da aka samu ya sanya ake gano tarin hanyoyin magani da gano abubuwan da a baya ake ganin ba za su taba yiwuwa ba. Abin da ke kara nuna cewa akwai abubuwa da dama a jikin dan Adam da ba a ma gano su ba.
A baya-bayan nan wata mai amfani da shafin Instagram @Drbelswelness tayi da’awa cewa sabon ilimin kimiya yayi babbar fallasa bombshell inda ya tabbatar da cewa kwan haihuwa na ‘ya mace baya raguwa saboda shekarunta, amma maniyi na da namiji shine bayan lokaci ke raguwa.
Mai amfani da shafin ta kara bayani da cewa, “Sau tari kuna ji ana cewa mata na da dama ta lokaci na dena haihuwa. Yanzu kimiya ta sauya wannan tunani. Masu aikin bincike sun zurfafawa wajem fahimtar kwan halittar ‘ya mace da maniyin da namiji a lokacin da suke kara shekaru sai suka gano wani abu da zai baku mamaki. Kwan halitta na ‘ya mace kwayoyin halittarsa na DNA basa sauyawa sai dai kwayoyin halittar da ke cikin maniyin da namiji, a takaice dai shi da namiji shine bayan tsawon lokaci da shekaru maniyinsa ke fuskantar barazana a kwayar halitar da ake samun damar haihuwa.”
@Drbelswelness ta kara da cewa saboda akwai sauye-sauye a cikin maniyi da ake samu dalilin yawaitar shekaru, yaran da iyayensu tsofaffi ne sun fi fuskantar barazana a haife su da matsaloli kamar galahanga da masu zuwa da karamin kai da sauransu.
Mai amfani da shafin ta ce ta yarda da da cewa yawan kwai na matan na raguwa da yawan shekaru, sai dai kwayar halittar ta DNA na nan na ingancinta idan aka kwatanta da maniyin maza.
Ya zuwa ranar 24 ga watan Oktoba,2025 wannan wallafa ta samu nuna sha’awa likes 100,000 da tsokaci ko comments 4843 . Bayan duba a sashin tsokaci a akwai mabanbantan tsokaci.
Da take murna da wannan batu @Nanaya102 ta rubuta cewa, “Ina tunin mata na bukatar neman afuwa babba daga kimiya, saboda tsawon lokaci da ake zargin mata kan batun kwayoyin haihuwarsu, godiya ga Allah kwayoyin halittarmu sun ‘yantu!! Bara na kwanta cikin kwanciyar hankali,” ita kuwa @Deborah ta rubuta cewa “Ina manyan mata ku auri matasan mazaje” ya ku mazaje tsofaffi idan kun so kada ku je kuyi aure akan lokaci, lokaci dai tafiya yake.
@Official Dralex ta kalubalanci abun ne inda ta rubuta cewa “A ina ne aka wallafa wannan bincike, a kuma wace kasa a ka yi? Ina shedun da aka yi amfani da shi a ina aka samu samfurin kayan gwajin da kabila da yankin da kuma al’umma.?”
@Dr Amandajordan, Wacce bata aminta da da’awar ba ta bayyana cewa “wannan ba gaskiya ba ne kamar yadda kowane kwayar halitta take a jikin dan Adam, yawan maniyi na raguwa haka nan kwayaye na mata ma na tafiya da shekaru, kin dakusar da bayananki da kika hada su da karya.”
@Davev ta kara da cewa “ wannan karya ce kasancewar ilimin kimiya bai ambata haka ba..”
Tsokacin da mutanen ke yi dai ya zama daban-daban yayin da wasu ke murna da samun wannan ci gaba wasu na karyatawa wasu na cewa an dauki bangare. Duba da haka DUBAWA ya ga dacewar gudanar da bincike kan wannan batu saboda irin muhimmanci da yake da shi a zamantakewa.
Tantancewa
DUBAWA da fari ta bukaci wacce ta yi da’awar ta bayyana asalin inda ta samo bayananta ko inda aka yi binciken da ta bayyana a wallafarta sai dai babu wata amsa daga bangarenta.
Sai muka fara gudanar da bincikenmu ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ga misali ingancin kwan haihuwar mata a shekaru “ingancin kwan haihuwar mace (women egg quality age,)” da lokacin da kwayoyin halittar maniyin namiji ke sassauyawa “ shekarun da namiji maniyinsa ke sassauyawa/(paternal age sperm mutations,”) da wane lokaci ne kwayoyin halittar maniyi na namiji ke ci gaba da rayuwa da tayaya shekaru ke shefar haihuwa a wajen maza da mata da sauransu. Burin wannan bincike shine a gano ko a kwai wasu sahihan bincike da suka mara baya ga wannan da’awa ko kuma wadanda suka yi mata raddi, bayan da take cewa kwan haihuwa na mata baya rasa inganci yayin da a bangaren maza maniyinsu ke rasa nasa ingancin bayan wasu shekaru.
Binciken dai ya gano cewa dukkanin bangarorin biyu, bangaren mace kwan haihuwa da namiji maniyi, dukkaninsu shekaru na tasiri a kansu idan ana magana ta haihuwa. A 2025 wata mujalla da aka wallafa Journal of Ovarian Research ta yi nuni da cewa yayin da mace shekaru suke cimmata kwan haihuwarta ma shekarun na shafarsu ta fuskar ingancinsu da ma yawansu.Wannan ya nunar da cewa ana iya samu bayan shekaru sun yi nisa macen idan ta zo haihuwa ‘yan halitar su samu tasgaro sai ka ga ana haifar yara da ake kira masu galahanga ko wasu su kira su da ‘yanruwa ko masu karamin kai.
Wani nazarin na PubMed noted ya lura cewa a kwai fargabar samun kwayoyin halitta (chromosomes) wadanda ba daidai suke ba inda ake samun kwan halittar na mata yana dauke da kwayoyin halittar chromosomes wanda ba haka suke ba, wannan na karuwa idan aka haure shekaru 35. Wannan nazari ya tabbatar da cewa shekaru na shafar kwan halittar , abin da ke nuna fadin cewa shekaru basa shafar ingancin kwan halittar wannan ba haka yake ba.
A lokaci guda kuma DUBAWA ta lura cewa da’awar kan maza su iya haihuwa a kwai alamun gaskiya a ciki duk da cewa an gabatar da bayanin ba tare da cikakken bayani ba.
Sabaninn mata maza suna ci gaba da fitar da maniyi a duk rayuwarsu sai dai nazari ya tabbatar da cewa bayan shelkaru sun tura ingancin maniyin na raguwa.
A shekarar 2022 akwai makala da ta fita a mujallar Nature Reviews Genetics inda ta ba da rahoto reported da ya nunar da cewa tsofaffin iyaye na iya tura wasu kwayoyin halitta da aka sassauya zuwa ga ‘ya’yansu wamda kuma hakan ka iya jawo a haifi yara da galahanga ko wadanda ake kira da ‘yanruwa . A wani nazarin kuma da aka wallafa a Nature a 2019 ya samu tallafi supported na wannan bincike wanda ya nuna cewa yawaitar shekarun iyayen na shafar irin yaran da suke haifa. A wani nazari kuma a mujallar Oxford Academic’s Human Reproduction journal ya nunar da cewa rarrabuwar kwayoyin halittar na DNA da matsi da rashin isasshen maniyin abubuwa ne aka fi samu a wajen mutane da suke da yawan shekaru
Daga wannan sharhi ya nunar cewa yiwuwar samun haihuwa tsakanin maza da mata na raguwa idan shekarunsu suka yi nisa amma saboda tsari na halitta, mata na fuskantar raguwar kwayoyin haihuwarsu da rashin daidaitton kwayoyin halittarsu a bayan tsawon lokaci, yayin da maza ke fuskantar barazana da lalacewar kwayoyin halittar na DNA wasu ma su mace.
Babu wani nazari da ya goyi bayan da’awar cewa kwan haihuwar mata baya raguwa yayun da a bangaren maza maniyin maza na raguwa.
.Bincike dai ya nunar da cewa dukkanionsu maza da matan batu na haihuwarsu na samun tasgaro ta dalilin shekaru amma kowanne akwai hanya ta daban da yake bi.
Tsokaci na kwararrun masana a fannin lafiya
Bila Esther, kwarriya kan sha’aniun da ya shafi haihuwa a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe, ta bayyana cewa fadin cewa kwan haihuwar mace baya tsufa duk da shekarunta, wannan abu ne da ba za a dogara da shi ba, ya kuma kamata ayi taka tsantsan. Shedu na kimiya sun nunar da cewa yawan kwai na haihuwa a wajen mace na raguwa, ingancinsa ma na raguwa a lokacin da mace ke tsufa.
Ta kara da cewa duk da kasancewar nazarce-nazarce sun nunar da cewa akwai abin da ake kira halittar Mitochondria a cikin kwayayen wacce ke samar da kuzari ga kwayayen tana iya zama daram a yanayin da take tsawon lokaci amma halittar da ake kira nucleus wacce ke rike da kwayoyin halittar wannan ba makawa shekaru na shafarta.
“Shi kwai kwayar halitta ne kamar kowane kwayar halitta (cell) a jikin jiki. Kamar yadda kwayar halittar ke tsufa ta samu rauni haka suma kwayayen. Wannan na nufin nagartar kwayayen na raguwa yayin da mace ke tsufa.”A cewarta.
Esther ta nunar da cewa batu na haihuwa a dukkanin bangarori na mata da maza duk suna raguwa idan shekaru na karuwa. Maniyi karkonsa na raguwa da daidaitonsa bayan lokaci, yayin da a bangaren mace yanayin cimaka da gajiya da wasu yanayi na muhalli duk suna shafar kwanta. Wannan abu ne da haka yake faruwa a rayuwa, a cewarta.
Shehu Ibrahim likitan mata a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano yayi bayani yana cewa matsalar ta shekaru ke sanyawa wasu matan ke alkinta kwan haihuwarsu, ya kara da cewa matan da suke so su dakatar da haihuwarsu dalilin karatu ko aiki irinsu su kan kai ajiyar kwan haihuwarsu a sa shi na’urar sanyi, har sai lokacin da suka shirya haihuwar.
“Idan mace ta ajiye kwan haihuwarta a tun da fari akwai yiwuwar ta samu damar haihuwa cikin sauki, amma idan shekarun suka yi nisa aka fara tsufa damar haihuwar na raguwa wannan abu ne na zahiri da ake gani ba kawai a bangaren matan ba har ma da maza.”
Har ila yau ya kuma bayyana wasu dabi’u kamar shan taba sigari da shan barasa da shan miyagun kwayoyi na iya kawo tasgaro ga samun damar haihuwar. A cewarsa akwai kuma tsari na rayuwa da wasu ke dauka wanda hakan ma na iya shafar yadda za su haihu, wannan kuma ya shafi maza da matan.
“Idan ana magana ta kalubalen haihuwa, ba kawai magana ce ta kasancewa mace ko namiji ba. Shekaru da batu na lafiya da tsarin rayuwa duk bangarori ne da ke iya shafar duka bangaren na mata da maza.” a cewar Ibrahim.
A Karshe
Yayin da bincike ke kara zurfi kan batu na lafiya babu wani nazari da ya nuna cewa kwai na haihuwar mace shekaru basa shafarsa, dukkaninsu maza da mata shekaru na shafarsu ta fuskar samun damar haihuwa duk da cewa kowane da yadda abin ke shafarsa a tsari na halitta, don haka wannan da’awa yaudara ce.




