Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Ana iya amfani da albasa a sa gashi tsurowa a inda aka riga aka fara samun sanko.
Hukunci:Yaudara ce! Bincike ya nuna cewa lallai albasa na da sinadaran da ke iya sa gashi tsurowa sai dai dole sai an yi wani karin binciken kafin a tabbatar ana iya amfani da shi wa masu sanko.
Cikakken bayani
Albasa, abinci ne wanda ake yawan omawa. Yana da dangi da tabarnuwa da albasa mai lawashi da wasu sauran ganyayyakin da ke da kanshin albasar. Hakazalika, albasa shuka ce wadda aka san cewa tana da sinadarai da dama da ke da alfanu ga jikin dan adam. Ban da dafa abinci, ana kuma iya amfani da shi wajen samun mai, ana amfani da shi wajen ilimi da kuma samun launonin da ake amfani da su wajen rini.
@desola__xn ya wallafa a kan shafin X cewa albasar na iya taimakawa masu sanki. A cikin bayanin da ya yi, marubucin ya ce duk mai sha’awa na iya yanka albasa, ya matse ruwan ya shafa a kan inda ya ke da sankon.
Nan da nan wurin da ake tsokaci ya cika da tambayoyi daga mutanen da ke so su san sahihancin bayanin da ma tabbacin ko ruwan albasar na aiki kamar yadda ake da’awa, yayin da wasu da dama kuma su kuma suka bayyana shakkunsu.
Fobs (@diction234), wanda ke shakkar sahihancin da’awar cewa ya yi, “Ba ya aiki. Za ku yi ta wari kawai ba gaira ba dalili’” wani shi ma mai amfani da shafin na X Olamilekan (@Olamispread12), cewa ya yi, “Wow, nagode kwarai da wannan bayanin, da ma sanko na ya dade ya na bani damuwa.”
Baya ga X an sake wallafa wannan da’awar a wasu shafukan a shafin Facebook kamar nan, nan, da nan. Tun bayan da aka wallafa wannan labarin ranar 30 ga watan Maris 2024, an yi tsokaci 286 a kai, an sake yadawa sau 840 an sa alamar like 2,000 sa’annan wadansu sun adana shafin dan komawa kai sau 2,700.
Ganin yadda batun ya dauki hankali sosai da ma dai irin tsokacin da aka rika yi ya sa muka ga ya dace a tantance gaskiya.
Tantancewa
Bisa bayanan shafin kiwon lafiya na Healthline, wata sa’a ana iya amfani da ruwan albasa inda gashin mutun na cinyewa. Zai iya maido da kaurin gashin ya ma sa shi ya yi kyalkyali. Haka nan kuma ana iya amfani da shi wajen hana gashi yin furfura da wuri da ma warkar da amosanin kai.
Albasa na inganta abinci sosai, domin ya na da sinadarin sulfur wanda jikin dan adam ke bukata sosai.
A duk sadda aka sa shi cikin gashi ko fatan kai, ruwan albasa na iya taimakawa wajen sa gashi ya tsuro da kyau a cika ya kuma yana shi zubewa.
Wani binciken da Khalifa Sharquie aa Hala Al-Obaidi suka gudanar, sun duba kimiyar amfani da ruwan albasa dan tsurowar gashi. Rukunin wadanda suka wanke gashinsu da ruwan albasa sun fi ganin karuwa a tsawon gashin yayin da wadanda suka wanke na su da ruwa zalla kuma ba su ga wani banbanci ba. Maza kuma sun fi samun alfanu daga wannan gwajin fiye da mata.
Bacin haka, wasu karin bincike da bitar da aka yi kan irin magungunan da ake amfani da su wajen rage zubewar gashi, sun yi amfani da wannan binciken wajen shaida cewa lallai albasar na taimakawa wajen ganin gashi ya tsuro.
To sai dai, bai kamata a yi amfani da shi a matsayin magani na sanko da ma dai sauran cututtukan da ka janyo zubewar gashi ba. Duk da cewa an sahida ya kan kara tsawon gashi, babu binciken da ya nuna cewa ana iya amfani da shi a cututtukan da ke sanadin zubewar gashi.
Ra’ayin kwararru
Adenike Iwuchukwu, wata kwararriya a kan gashi, ta yi bayani kan yadda ake amfani da ruwan albasa dan gashi ya yi tsawo. Ta kuma ce ana iya amfani da ruwan albasar ma a irin cututtukan da ake iya warkarwa a gida ba sai an je asibiti ba.
Ms Iwuchukwu ta rubuta cewa, yayin da za’a iya amfani da shi wajen tsuro da gashi, ba abun da jikin kowa ke karba ba ne, saboda ba za’a iya auna yawan shi ba, yawan da aka diba, mai yiwuwa zai iya yi wa wasu yawa. Ta kuma ce wadanda ba su iya jurewa albasa ma bai kamata su yi amfani da shi ba dan zai iya mu su lahani sosai.
Mun kuma tattauna da Daisy Obiano, wta masaniyar cututtukan da suka shafi gashi da kai wato trichologist a turance, wadda ta ce sa albasa a gashi na da wari sosai. Kuma idan har ma ana so a yi amfani da shi a kan masu sanko ne dole sai an yi nazarin irin tasirin da ya ke da shi a kan ramukan da kan tsuro da gashin ba, kuma amfani da ruwan albasa kadai ba zai iya yin hakan ba.
“Ruwan albasa abu ne da ake amfani da shi a gida dan gashi ya tsuro, amma ba’a riga an tabbatar da hakan a kimiyance ba. Dole sai an gwada sinadaran albasar masu kaifi. Dole kuma a yi la’akari da abubuwan da ake amfani da su wajen inganta gashi domin abu daya kawai ba zai tsuro da gashin ba,” ta bayyana.
Ms Obiano ta bayyana cewa sabbin kwayoyin da ke tsuro da gashi kan dauki makwanni shida kafin su tofo, amma albasa ba zai iya sa gashi ya tsuro a cututtukan da ke da nasaba da zubar da gashi. Ta ce ba’a riga an sami hujjoji na kimiya ba.
Ta kammala da cewa ba ta ga wani bincike na kimiya da ya tabbatar da cewa ana iya warkar da sanko ba. Dan haka shawararta ga wadanda ke neman karin bayani shi ne su tuntubi kwararru dan samun cikakken bayani.
A karshe
Duk da cewa an ce ruwan albasa abu ne da ake iya amfani da shi wajen kara tsawon gashi da ma warkar da wasu cututtuka a gida, babu tabbacin cewa ruwan albasar na iya warker da cututtukan da ke zuwa da zubewar gashi ba.