Zargi: Wata sanarwar da ke daukar hankali wadda kuma ake ta yayatawa a dandalolin soshiyal mediya na zargin wai Lai Mohammed ministan yada labarai da al’adu ya ce gwamnati ta kara farashin man fetur ne domin ta rage yawan hatsari da cunkuson motoci a titunan Najeriya.
Binciken da DUBAWA ta yi na duk furucin da ministan ya taba yi kan man fetur ya tabbatar cewa bai taba fadar wani abu mai kama da haka ba. Mai magana da yawunsa kuma ya karyata zargin
Cikakken labari
Tun daga farkon wannan shekarar yankunan Najeriya da dama su ke fama da karancin man fetur da kma karin farashin man da aka yi a kasar baki daya.
Masu kawo labarai sun ce dillalan man sun kara kudin ne bayan da suka sami goyon bayan NNPC wajen kara kudin man daga Nera 165 kowace lita zuwa Nera 179.
Sakamakon karin farashin man fetur din da na diesel, masu amfani da soshiyal mediya suka fara yada wata sanarwa waddda ake dangantawa da ministan yada labarai inda ya ce an kara kudin man ne domin takaita zirga-zirgan motocin da ke cunkoso a tituna da ma rage yawan hatsarin mota.
Kalaman da ake ambato su ne “Mun kara farashin man fetur zuwa Nera 200 na diesel kuma zuwa Nera 800 domin rage hatsarin mota da takaita cunkoson motoci a kan titunan Najeriya,” a cewar Lai
DUBAWA ta lura da cewa yawancin wadanda suka mayar da martani sukar ministan kawai su ka yi kai tsaye ba tare da neman jin wani dalili ba.
Ganin irin cece-kucen da ya biyo bayan furucin ne ya sa DUBAWA ta ke so ta san ko lallai ministan ya furta wadannan kalamai.
Tantancewa
Da muka duba wannann sanarwar da ake zargin ministan ya fitar mun ga cewa babu rana ko kuma kwanan watan da ministan ya yi wannan furucin.
Mun cigaba da binciken duk jawaban da ministan yada labaran ya yi dangane da tashin farashin man fetur ba mu ba komai ba illa wani rahoton da jaridar Vanguard ta yi ranar 16 ga watan Mayun 2016. Shi ma rahoton da muka duba, ba mu ga wani furuci makamancin wanda ake zargin Lai Mohammed din da ya ba.
Bugu da kari mun yi bitar rahotannin duk jaridu masu nagartar da ke wallafa labarai a yanar gizo-gizo inda nan ma ba mu ga wani abu makamancin haka ba.
Da DUBAWA ta tuntubi Segun Adeyemi, mai magana da yawun ministan yada labaran shi ma ya ce mai gidan na sa bai yi wannan maganar da ake zargi ya yi ba.
Adeyemi ya ce: “Wannan karya ne kawai, ku yi watsi da batun.”
A Karshe
Furucin da ake dangantawa da Lai Mohammed Ministan yada labarai da al’adun Najeriya, wanda ke zargin ya ce gwamnati ta kara farashin man fetur ne don rage yawan ababen hawa a kan tituna da ma hatsarin mota ba gaskiya ba ne. Binciken da DUBAWA ta yi na duk furucin da ya yi dangane da karin da aka samu a farashin man fetur bai bayyana wani furuci makamancin wanda ake ce wa ya yi ba. Mai magana da yawun ministan ma ya karyata zargin inda ya ce sanarwar da ake yadawa ba daga ofishinsu ta fito ba.