|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wasu daga cikin masu amfani da shafin Facebook kamar a wadannan wurare here da here da here sun yi da’awar cewa majalisar dattawa a Najeriya karkashin jagorancin Godswill Akpabio ta amince da sabuwar dokar yaki da masu aikata zamba ta intanet ta shekarar 2025.

Hukunci: Yaudara ce, DUBAWA a binciken da ta yi ta gano cewa majalisar ta tafi hutu bata amince da wata doka ba irin wannan.
Cikakken Sako
Dokar yaki da aikata laifuka a shafin intanet da aka yi wa kwaskwarima a 2024 an gabatar da ita ne don karfafa yaki cikin gaggawa kan ayyukan laifuka da ake yi kamar zamba cikin aminci da satar bayanai da muzanta mutane ta hanyar intanet.
Sai dai kuma wannan doka ta jawo cece-kuce kungiyoyin al’umma da masu fafutukar kare hakkin bil Adama sun bayyana cewa wasu daga cikin abubuwan da dokar ta tanada basu da tushe, za a iya amfani da su wajen yin barazana da dakile ‘yanci na fadin albarkacin baki da dakushe ko dakile ‘yanfafutuka da aikin jarida.
Kungiyoyin fafutuka irinsu Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta kalubalanci wannan doka a kotun ECOWAS, yayin da hukumar karen hakkin bil Adama ta kasa National Human Rights Commission da masu sanya idanu na kasa da kasa international observers suka bukaci a sake nazari kan dokar. A martanin gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa za ta sake zama da masu ruwa da tsaki don sake tattaunawa kan dokar.
Ana tsaka da wannan ne sai kawai aka rika ganin wallafa na yawo a shafukan intanet na Facebook kamar a wadannan wurare here da here da here, a watan Agusta,2025, wadanda ke cewa sabuwar dokar yaki da masu aikata laifuka a shafin intanet ta 2025 an amince da ita ta zama doka.
Daya daga cikin irin wannan wallafa da ta fi bazuwa na cewa “LABARI DA DUMI-DUMI: Sabuwar dokar yaki da laifukan a intanet ta 2025, an amince ta zama doka karkashin shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio.”
Wannan na nufin duk wani nau’i na laifi a shafin na intanet karkashin dokar (abin da ya hadar da haramci da hanawa da sauransu) a yanzu dokar za ta yi aiki, za a aiwatar da ita a duk fadin Najeriya. Idan kai mai amfani da shafin intanet ne, ko mai samar da wani bidiyo ko shugaba a wani guruf a wasu shafuka (WhatsApp da Facebook da Telegram da sauransu, ), dole sai ka san doka saboda rashin sanin doka ba zai zama abin dogaro ba.”
Wasu da suka yi tsokaci a shafin sun nuna tantamarsu kan wannan doka, James Smith yace “Wannan doka ba za ta yi tasiri ba. ‘Yansiyasa suke kan gaba wajen taka doka, idan har ba za a mutunta doka ba , Adalci ba zai samu ba.” Godiya ga Allah a cewar Chima, “Wannan wata hanya ce ta dakile ayyukan ‘yanjarida masu bin diddigin labari, a dakatar da su a kokari na bankado wasu ayyuka da aka yi bisa kuskure.”
A nasa tsokaci kuwa Tony Grey, cewa yayi “Wannan abu ne me kyau.” Shi kuma Jeremiah Odimayo Gbenga yayi ajiyar zuciya yana mai cewa “Hmm! A halin da ake ciki, gidajen ajiya da gyaran hali za su cika makil.”
Ganin cewa an yi suka kan wannan doka bisa cewa tana barazana ga ‘yancin fadin albarkacin baki da ‘yancin walwala, Labaran karya kan wannan sabuwar doka na iya jawo fargaba mara dalili cikin al’umma da ‘yanjarida da masu fafutuka. DUBAWA da ta dubi lamarin ta ga dacewar gudanar da bincike kan wannan da’awa.
Tantancewa
Bincike da DUBAWA ta yi ta gano cewa majalisar dattawan Najeriya tana hutu na shekara ne (annual recess) tun daga karshen watan Yuli,2025 za kuma ta koma bakin aiki a ranar 23 ga watan Satumba,2025. Wannan ya sanya cewa batun cewa an amince da dokar ta (Cybercrimes Act 2025) bata ma taso ba.
Har ila yau, kudirin doka a Najeriya don majalisa ta amince da shi baya nufin za a yi amfani da shi a matsayin doka har sai shugaban Najeriya ya rattaba hannu a kanta (Presidential assent).
Wane lokaci ne kudiri ke zama doka a Najeriya?
Kafin kudiri ya zama doka a majalisa, dole zai bi matakai daban-daban:
1. Matakin gabatarwa – A ba da dalilai na bukatar gabatar da kudirin.
2. Karatu na farko– A gabatar da kudirin a farko ba tare da yin muhawara ba.
3. Karatu na biyu – Babbar muhawara kan makasudin kudirin.
4. Matakin Kwamiti – Filla-filla da kudirin, sautari ya hadar da sauraren jin ra’ayin jama’a.
5. Karatu na uku– Duba na karshe da kada kuri’a.
6. Amincewar majalisa –Dukkanin majalisun biyu sai sun amince (Majalisar dattawa da majalisar wakilai).
7. Sanya hannun shugaban kasa—Shugaban kasa dole ya sanya hannu kan kudirin doka cikin kwanaki 30 da mika masa kamar yadda yake kunshe a sashi na 58(4) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kamar yadda muka ga wadannan matakai da ke a sama, babu wata dokar yaki da aikata laifuka ta hanyar shafukan intanet (Wacce ta haramta ko ta hana aikatawa da sauransu) da aka yi kwaskwarima kan dokar ta 2024 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattabawa hannu a ranar 28 ga watan Fabrairu,2024, kasancewar shi kansa tattaunawa kan batun ya fara ne a May 2025, babu wata sabuwar doka da ta fita.
A Karshe
Da’awar cewa an amince da sabuwar dokar yaki da aikata laifuka ta hanyar intanet (Cybercrimes Act 2025) wannan yaudara ce, majalisar dokokin Najeriya a yanzu tana hutu ne, kuma babu wata doka mai kama da haka da aka amince da ita, dokar ma da ake magana a kanta kawo yanzu ita ce ta kwaskwarima kan dokar laifukan ta intanet (Cybercrime (Amendment) Act 2024) wacce ake sake duba a kanta bayan karuwar laifukan.




