Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa:Wani ma amfani da shafin instagram ya ce akwai sabon binciken da ke nuna cewa rashin wanke hankora da daddare kafina a kwanta na iya kara hadarin kamuwa da cututtukan da ke da nasaba da zuciya.

Hukunci: Da gaske ne. Sakamakon bincike daban-daban na nuna cewa cututtukan hakora, wadanda ke da alaka da dabi’ar rashin goge hakora yadda ya kamata na iya janyo cututtukan zuciya.
Cikakken bayani
Cututtutakan zuciya wadanda aka fi sani da Cardiovascular diseases (CVDs) a turance cututtuka ne da sukan shafi zuciya da kuma hanyoyin hini. Bisa bayanan hukumar lafiya ta duniya World Health Organisation (WHO), ta ce cututtukan da ke da nasaba da zuciya ne suka fi kissa a duniya baki daya.
Abun mamaki kuma, wani mai amfani da shafin Instagram @thefarmacyreal sai ya danganta dabi’ar google hakora da wadannan cututtukan masu tsanani. A cewar mai amfani da shafin, akwai biniciken da ya tabbatar cewa rashin goge hakora da daddare na iya karawa mutun hadarin kamuwa da cututtukan zuciya.
@thefarmacyreal ya bayyana cewa da daddare, bakin mutun ba ya iysa fitar da yanwu sosai, dan haka ba a cika samun yawan da ya dace a samu dan dauraye bakin yadda ya kamata ba, domin idan ya dauraye bakin zai awar da yawancin kwayoyin cutar da kan makale a kan hakora . Wannan ne ya kan sa hakora da dasashi duk su rube kuma ta haka ba wuya kwayoyin cutar da suka rubar da hakoran sun shiga cikin jinin mutun.
“Abin da watakila ba za ku sani ba shi ne, kwayoyin cutar da ke sa hakora su rube na iya bi ta hanyar jini su sa kumburi. Wannan kuma zai iya sa kwayoyin cutar toshe wadannan hanyoyin jinin. Ana kiran wannan cutar atherosclerosis da turanci kuma ana danganta shi da bugun zuciya, hawan jini, da kumburi a hanyoyin jini, da ma cutar da kan shafi hanyoyin da jini ke bi,” wani bangaren sakon ya bayyana.
Wani mai amfani da shafin @mlbcad ya tambaya ya yi dangane da binciken da ake magana a kai. “Wani bincike ke nan?” ya tambaya.
Wani kuma, @sh33na, cewa ya yi, “To amma wasu kuma kan ce abun goge bakin kan janyo cutar daji, dan haka da wuya mutun ya gane abin da ke zahiri.”
@Joker_srr, kuwa ko daya ma bai yadda da batun ba, inda ya ce “fake.”wato “bogi”
DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar batun tunda abu ne da ya sgafi lafiyar al’umma.
Tantancewa
Abin da muka fara yi shi ne duba makalun da mawallafin ya sa. makalar farko ta kai mu ga wani labari ne daga shafin labaran kiwon lafiya wato Medical News dangane da yadda rashin goge hakpra a kai-a kai ka iya janyo hadari.
Wannan labarin ne ma aka yi amfani da shi a matsayin hujja cikin wani binciken da aka yi a shekarar 2023 cikin mujallar rahotannin kimiya mai taken “rashin goge hakora da daddare na iya janyo cututtukan zuciya.” Wannan binciken ya yi kokarin gano ko rashin goge hakora na da alaka da cutututtukan da ke da nasaba da zuciya kuma sakamakon ya nuna cewa yayin da goge hakora ke da mahimmanci da safe kafin karin kumallo, goge hakoran kafin a kwanta ne ma ya fi mahimmanci.
Labarin da ke cikin makala ta biyu kuma daga Kungiyar Masanan ZUciya na Amurka ne mai taken “Rashin wanke hakora yadda ya kamata na da alaka da cututtukan zuciya.”
Rahoton ya nuna cewa goge hakora sau biyu a rana cikin minti biyu kowane lokaci zai rage hadarin kamuwa da cututtukan zuciya. Wannan labarin ya danganta hujjojin shi da rahoton wani binciken da aka wallafa a shekarar 2018 cikin mujallar AHA, tare da taken “Rasgub kula da hakora da shawo kan hawan jin tsakanin magidantan Amurka: Sakamakon bincike daga Hukumar kyla da Lafiya da sanya ido kan abinci daga 2009 zuwa 2014.”
Wannan binciken ya gano cewa cutar dasashi kan kara ta’azzara hawan jini kuma ma ya na tasiri a kan magungunan da ake amfani da su dan hawan jini.
Binciken da muka yi na mahimman kalmomin a shafin google na kwararrun masu bincike wanda aka fi sani da Google Scholar dan gane dangantakar goge hakora da cututtukan zuciya, kamar yadda mawallafin ya rubuta, ya kai mu ga wani binciken da aka yi a shekarar 2024 mai taken “Alakar da ke tsakanin goge hakora a kai-a kai da hadarin cutar zuciya: Bita da Nazari.”
Sakamakon binciken na 2024 ya goyi bayan da’awar cewa goge hakora a kai-a kai na iya rage hadarin kamuwa da cututtukar da ke da nasaba da zuciya.
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa wannan da’awar gaskiya ce. Bincike da dama masu nagarta sun danganta goge hakora da cututtukan da ke da nasaba da zuciya. Akwai bayani ma wanda musamman ya danganta cututtukan zuciya da na hakora wanda aka fi sani da periodontal disease (wanda ya kunshi rubewar dasahi da kumburi da rubewar hakori.